Skip to content

Hausa Bible

Ibraniyawa 4

1 Da yake alkawarin shiga hutunsa yana nan har yanzu, bari mu yi hankali sosai kada wani daga cikinku yă kāsa shiga.

2 Gama mun riga mun ji waˈazin labari mai daɗi kamar yadda su ma suka ji. Amma saƙon labari mai daɗin nan da suka ji bai yi musu wani amfani ba, domin ba su karɓe shi da bangaskiya ba.

3 Amma mu da muka ba da gaskiya, mu ne masu shiga hutun nan. Mu dinga tuna da kalmar Allah nan mai cewa, “Sai na yi fushi na yi rantsuwa cewa, ‘Ba za su shiga hutuna ba sam.’ ” Allah ya faɗa haka ko da yake ya riga ya gama aikinsa tun lokacin da ya halicci duniya.

4 Gama a wani wuri a cikin Rubutacciyar Maganar Allah an yi magana game da rana ta bakwai cewa, “A rana ta bakwai Allah ya huta daga dukan aikinsa.”

5 Amma har yanzu an sāke yin wannan zance cewa, “Ba za su shiga hutuna ba sam.”

6 A dā an yi waˈazin labari mai daɗi game da hutun nan, amma waɗanda aka yi musu waˈazin ba su shiga ba saboda rashin biyayya. To, yanzu haka, akwai zarafi don waɗansu su shiga hutun ke nan.

7 Ga shi kuwa Allah ya sāke shirya wata rana, wadda ya kira, “Yau”. Ya yi magana game da ranar ne, bayan shekaru masu yawa ta bakin Dawuda, kamar yadda Rubutacciyar Maganar Allah ta faɗa a dā, “Yau idan kun ji muryar Allah, kada ku yi taurin zuciya.”

8 Da a ce Yoshuwa ya ba mutanen Allah hutun nan, da Allah bai yi magana daga baya a kan wata rana dabam ba.

9 Wannan ya nuna cewa har yanzu akwai hutu irin ta Ranar Hutu ta Mako domin mutanen Allah.

10 Gama duk waɗanda suka shiga hutun Allah sukan huta daga ayyukansu kamar yadda Allah ya huta daga nasa.

11 Domin haka bari mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu shiga hutun nan. Kada kowa ya kāsa shiga saboda bin misalin waɗanda suka yi rashin biyayya.

12 Hakika, kalmar Allah tana da rai, tana da ƙarfin aiki kuma. Kaifinta ya fi na kowane takobi mai baki biyu. Tana sara har ciki-cikin mutum, ta raba ruhu da rai, da kuma gaɓoɓi da jijiyoyi. Har ma tana gane duk tunani da nufin da suke cikin zuciya.

13 Ba wani abu a dukan halitta wanda yake a ɓoye ga Allah. Kome da kome yana nan a buɗe, a fili kuma, a gaban idonsa. Shi ne kuma wanda za mu ba shi lissafi game da rayuwarmu.

14 To, tun da yake muna da Babban Firist mai girma, wato Yesu Ɗan Allah wanda ya ratsa sammai har gaban Allah, bari mu tsaya a kan amincewarmu wadda muka shaida.

15 Gama Babban Firist nan namu ba wani ne wanda bai damu da kāsawarmu ba. Aˈa, shi ne wanda aka gwada shi ta kowace hanyar da akan gwada mu, amma fa bai yi wani zunubi ba.

16 Saboda haka, bari mu yi ƙarfin zuciya, mu zo kusa da kujerar mulkin Allah, wato wurin alheri, domin mu karɓi jinƙai, mu kuma sami alheri wanda zai taimake mu a lokacin bukata.

Open Bible reader