Hausa Bible
Ibraniyawa 2
1 Saboda haka, ya kamata mu mai da hankali ga abubuwan da muka ji, domin kada rashin lura yă kai mu ga rabuwa da hanya.
2 Saƙon da aka ba mu ta bakin malaˈiku ya sami tabbaci, kuma duk wanda ya ƙi jinsa, ko ya yi rashin biyayya da shi, ya sami hukuncin da ya kamata.
3 In haka ne, ta yaya za mu tsira idan mun ƙyale irin wannan babban ceto wanda Ubangiji ne da kansa ya fara sanar da shi? Waɗanda suka ji kalmarsa kuma sun tabbatar mana cewa wannan gaskiya ne.
4 Saˈan nan Allah ya ƙara tasa shaida a kan tasu ta wurin alamu, da ayyukan ban mamaki, da manyan abubuwa iri-iri, da baye-baye waɗanda aka rarraba ta wurin Ruhu Mai Tsarki bisa ga nufinsa.
5 Wannan zamani mai zuwa, wanda muke magana a kai yanzu, ai, ba malaˈiku ne Allah ya sa su yi mulkinsa ba.
6 A maimakon haka, wani ya shaida a wani wuri cewa, “Ya Allah, mene ne mutum da ka damu da shi, ɗan Adam, har da ka kula da shi?
7 Ka sa shi a ɗan lokaci kaɗan a matsayi ƙasa da na malaˈiku, ka girmama shi da ɗaukaka da daraja,
8 ka sa kome a ƙarƙashin ikonsa.” Da Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikon mutum, ba wani abin da bai ba mutum iko a kai ba. Ko da yake, yanzu haka, ba ma gani yadda mutum yake yin mulki a kan dukan abubuwa.
9 Amma abin da muke gani dai shi ne Yesu wanda a ɗan lokaci kaɗan an sa shi a matsayin da yake ƙasa da na malaˈiku. Yanzu kam, an naɗa shi da ɗaukaka da girma saboda ya sha wahalar mutuwa. Ya yi wannan domin bisa ga alherin Allah ya mutu saboda kowa.
10 Allah ne ya halicci dukan kome, dominsa kuma dukan abubuwa sukan kasance. Allah ya kuma zaɓa yă kawo ˈyaˈya masu yawa ga samun ɗaukaka. Saboda haka, ya dace yă sa mai buɗe hanyar cetonsu yă zama cikakke ta wurin shan wahala.
11 Gama da shi mai tsarkake mutane, da su waɗanda aka tsarkake su kuma, duk suna da Uba ɗaya. Shi ya sa Yesu ba ya jin kunya yă ce da su ˈyanˈuwansa.
12 Ya ce wa Allah, “Zan yi shelar Sunanka ga ˈyanˈuwana, zan yabe ka a cikin taron jamaˈa.”
13 Ya kuma ce, “Ni ma zan dogara ga Allah.” Ya kuma sāke cewa, “Ga ni nan tare da ˈyaˈyan da Allah ya ba ni.”
14 Tun da yake ˈyaˈyan nan mutane ne masu nama da jini, sai ya zama ɗaya da su cikin jiki. Ya yi haka domin ta wurin mutuwarsa, yă halakar da wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato Shaiɗan.
15 Saˈan nan kuma yă kunce duk waɗanda tsoron mutuwa ya ɗaure su, kuma har tsoron ya mai da su bayi dukan rayuwarsu.
16 Lallai ba malaˈiku ne Yesu yake yi musu taimako ba, amma zuriyar Ibrahim ne yake yi musu taimako.
17 Saboda haka ya kamata a mai da shi kamar ˈyanˈuwansa ta kowace hanya, domin yă zama Babban Firist mai aminci, mai jinƙai kuma a cikin hidimarsa ga Allah, domin yă zama hadaya ta ɗaukar alhakin zunuban mutane.
18 Da yake shi da kansa ya sha wahala a lokacin gwadawarsa, ya isa yă taimaki duk waɗanda ake gwada su.