Skip to content

Hausa Bible

Ibraniyawa 13

1 Ku ci gaba da nuna wa junanku ƙauna irin ta ˈyanˈuwa.

2 Kada ku daina yi wa baƙi alheri, gama ta yin haka waɗansu suka yi wa malaˈiku hidima, ba da saninsu ba.

3 Ku tuna da waɗanda suke a ɗaure a kurkuku, kamar kuna a ɗaure tare da su. Ku kuma tuna da waɗanda ake ba su wahala, kamar ku da kanku ne kuke shan wahalar.

4 Zaman aure yă zama abin daraja a gare ku duka. Kada gadon aurenku yă ƙazantu, gama Allah zai hukunta masu yin zina da masu yin lalata.

5 Ku yi nesa da halin son kuɗi, ku kuma kasance da kwanciyar rai da abin da kuke da shi. Ga shi kuwa Allah ya ce, “Har abada ba zan bar ka ba, sam sam ba zan yar da kai ba.”

6 Shi ya sa, ba tare da shakka ba, muna iya cewa, “Ubangiji mai taimakona ne, ba zan ji tsoro ba. Me ɗan Adam zai iya yi mini?”

7 Ku tuna da shugabanninku waɗanda suka faɗa muku kalmar Allah. Ku dubi yadda suka yi rayuwarsu, da yadda ƙarshensu ya kasance, ku kuma bi gurbin bangaskiyarsu.

8 Yesu Almasihu kuwa ba ya canjawa, yadda yake jiya, haka yake yau, haka kuma zai kasance har abada.

9 Kada sababbin koyarwa iri-iri su kwashe hankalinku. Ya dace ku sami ƙarfafawar zuciya ta wurin alherin Allah, ba ta wurin alˈadu iri-iri na cin abinci ba. Waɗannan kam ba su da amfani ga masu kiyaye su.

10 Mu kuwa muna da bagaden hadaya wanda firistocin Tentin Kasancewar Allah a duniyar nan ba su da izni su ci daga hadayarsa.

11 Babban firist yakan kai jinin dabbobi zuwa cikin Wuri Mafi Tsarki domin yă miƙa shi hadaya saboda zunubai, amma naman dabbobin nan akan ƙone shi ne a bayan zango.

12 Haka kuma Yesu ya sha azaba a bayan gari domin yă tsarkake mutane ta wurin nasa jini.

13 Saboda haka sai mu fita zuwa wurinsa a bayan zango, domin mu jimre da irin wulaƙancin da ya jimre da shi.

14 Gama ba mu da birni marar shuɗewa a nan duniya, amma muna dai sa ido ga birnin nan wanda yake zuwa.

15 Bari kuma mu dinga miƙa hadayar yabo ga Allah ta wurin Yesu, wato yabon shaidar darajar Sunansa ke nan.

16 Kada ku daina yin alheri da zumuntar tarayya ta abin da kuke da shi, gama irin waɗannan hadayu suke faranta wa Allah rai.

17 Ku yi wa shugabanninku biyayya, ku kuma miƙa kanku ga ikonsu, gama suna kula da rayukanku, su kuma za su ba da lissafin aikinsu. Ku yi musu biyayya yadda zai sa aikinsu yă zama da farin ciki, ba da nauyin zuciya ba, gama wannan ba zai kawo muku wani amfani ba.

18 Ku yi adduˈa saboda mu. Mun tabbata cewa tunanin zuciyarmu ba ta damunmu game da wani laifi. Nufinmu shi ne mu aikata abin da yake daidai cikin ayyukanmu duka.

19 Ina roƙonku musamman ku yi adduˈa domin Allah yă sa in koma gare ku ba da daɗewa ba.

20 -

21 Allah ya tā da Yesu Ubangijinmu daga matattu ta wurin jinin yarjejeniyar nan ta har abada, Yesu wanda yake Makiyayi Mai Girma na tumaki. Ina roƙon Allah mai ba da salama yă cika ku da kowane abu mai kyau domin ku yi nufinsa, yă kuma dinga aikata a cikinku abin da ya faranta masa rai ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka ta tabbata ga Almasihu har abada abadin. Amin.

22 Ina roƙonku, ˈyanˈuwana, ku yi haƙuri da wannan gargaɗina, gama ba wata doguwar magana ce na rubuta muku ba.

23 Ina so ku sani cewa an sake ɗanˈuwanmu Timoti daga kurkuku. Idan ya zo da wuri, zan zo tare da shi in gan ku.

24 Ku gai da dukan shugabanninku da dukan tsarkaka. ˈYanˈuwanmu daga Italiya suna gaishe ku.

25 Alherin Allah yă tabbata a gare ku duka.

Open Bible reader