Hausa Bible
Ibraniyawa 10
1 Koyarwar Musa kuwa kwatanci ce kawai na abubuwa masu kyau waɗanda suke a gaba, ba ita ce ainihin abubuwan nan ba. Shi ya sa ba ta isa ba ta sa duk masu matsowa kusa da Allah su zama cikakke bisa ga hadayun nan da akan ci gaba da bayarwa shekara biye da shekara.
2 Da a ce Koyarwar Musa tana da iko ne, ai, da an daina miƙa hadayun nan, domin masu miƙa su za su sami tsabtacewa gaba ɗaya, tunanin zuciyarsu kuwa ba zai yi ta damunsu game da zunubansu ba.
3 Amma hadayun nan kuwa hanyar tunawa da zunubi ne, shekara biye da shekara.
4 Gama ba yadda zai yiwu jinin bijimai da na awaki yă kawar da zunubai.
5 Saboda haka, saˈad da Almasihu ya shigo duniya, ya ce, “Hadayu da baye-baye kam ba ka so, amma jiki ne ka shirya mini.
6 Hadayu na ƙonawa da na wanken zunubai kuwa ba ka jin daɗinsu.
7 Sai na ce, ‘Ga ni nan, ya Allah, na zo in aikata nufinka, kamar yadda yake a rubuce game da ni a Rubutacciyar Kalmar Allah.’ ”
8 Da farko ya ce, “Hadayu, da baye-baye, da hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta wanken zunubai kam ba ka so, ba ka kuwa jin daɗinsu.” Ya faɗa haka ko da yake Koyarwar Musa ce ta ce a kiyaye waɗannan umarnai.
9 Ya sāke cewa, “Ga ni nan, na zo in aikata nufinka.” Wato, an ajiye tsari na farko a gefe ke nan domin a kafa na biyun.
10 Bisa ga nufin Allah kuma an mai da mu tsarkaka ta wurin hadayar jikinsa wadda Yesu Almasihu ya miƙa sau ɗaya tak ba ƙari.
11 Kowace rana kowane firist yakan tsaya yana yin hidimarsa, yakan yi ta miƙa irin wannan hadaya wadda ba ta da ikon kawar da zunubai.
12 Amma da Almasihu ya miƙa hadaya ɗaya ta har abada saboda zunubai, sai ya zauna a hannun dama na Allah.
13 Tun lokacin nan kuwa yana jira ne a sa abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa domin yă tattaka su.
14 Bisa ga hadayar nan ɗaya kuwa, ya mai da waɗanda aka tsarkake su su zama cikakku har abada.
15 Ruhu Mai Tsarki ya yi shaida a kanmu game da wannan. Da farko, ya ce,
16 “Ga yarjejeniyar da zan yi da su, bayan lokacin nan, in ji Ubangiji. Zan rubuta Koyarwata a allon zuciyarsu, in kuma sa ta a cikin tunaninsu.”
17 Ya kuma ƙara da cewa, “Zunubansu da laifofinsu ba zan sāke tunawa da su ba.”
18 Saˈad da an gafarta zunubai kuwa, ba wata bukatar hadaya saboda zunubi.
19 Saboda haka, ˈyanˈuwana, muna da cikakken ˈyanci mu shiga Wuri Mafi Tsarki bisa ga jinin Yesu.
20 Shi kuwa ya buɗe mana sabuwar hanya, hanya mai rai kuma, ta labulen nan, wato, jikinsa.
21 Muna kuma da Babban Firist wanda yake mulkin dukan jamaˈar Allah.
22 Saboda haka bari mu matso kusa da Allah da zuciya mai gaskiya, da bangaskiya marar shakka. Mu matso da zuciya wadda aka tsabtace daga alhakin zunubi, da kuma jikin da aka wanke da ruwa mai tsabta.
23 Bari mu tsaya a kan sa zuciyar nan tamu, wadda muke shaida, da ƙarfi sosai domin shi wanda ya yi mana alkawari mai aminci ne.
24 Mu lura da juna ta yadda za mu iza juna ga nuna ƙauna da yin aikin nagarta.
25 Kada mu bar yin taron sujada, kamar yadda waɗansu sun saba yi. A maimakon haka mu dinga ƙarfafa juna, mu kuma ƙara yin haka yayin da kuke ganin cewa Ranar nan tana matsowa kusa.
26 Ba wata sauran hadaya ta wanke zunubi idan mun ci gaba da yin zunubi da gangan bayan da muka sami sanin gaskiya.
27 A maimakon haka, abin da ya rage shi ne jira cikin razana da tsoro saboda hukunci da wuta mai tsananin zafi wadda za ta cinye masu gāba da Allah.
28 Duk wanda ya ƙetare Koyarwar Musa akan kashe shi, babu tausayi, bisa ga shaidar mutum biyu ko uku,
29 balle ma wanda ya rena Ɗan Allah, ya yi banza da jinin yarjejeniyar nan wanda ya tsarkake shi, ya kuma zargi Ruhu Mai Tsarki mai alheri! Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani ya cancanta a yi wa wannan mutum?
30 Gama mun san wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce, ni kuwa zan rama.” Ya sāke cewa, “Ubangiji zai yi shariˈar mutanensa.”
31 Abin ban tsoro ne fa mutum yă fāɗa cikin hannuwan Allah Mai Rai.
32 Ku tuna fa da kwanakin dā. Bayan da kuka sami ganin hasken Allah, kun jimre sosai, kuna kokawa da wahaloli.
33 Wani lokaci ana zaginku a fili, ana tsananta muku a gaban jamaˈa. Wani lokaci kuma kuka yi tarayya da waɗanda suke shan irin waɗannan wahaloli.
34 Gama kun nuna tausayi ga waɗanda suke a kulle a kurkuku, kun kuma nuna farin ciki bayan da aka ƙwace muku kaya, domin kun sani cewa kuna da mallaka mafi kyau da za ta dawwama har abada.
35 Saboda haka kada ku yar da ƙarfin zuciyarku, gama zai kawo muku babban lada.
36 Ya kamata ku jimre, domin ta yin haka ne za ku aikata nufin Allah. Bayan haka kuma ku karɓi abin da aka yi muku alkawari.
37 “Gama ba da daɗewa ba, Mai zuwan nan zai zo, ba zai yi latti ba.
38 Mutumina mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya. Amma idan ya ja da baya, raina ba zai ji daɗinsa ba.”
39 Amma mu kam ba irin masu ja da baya zuwa ga halaka ba ne, mu dai masu ba da gaskiya zuwa ga samun ceto ne.