Hausa Bible
Afisawa 4
1 Saboda haka, ni da nake cikin kurkuku saboda bin Ubangiji, ina roƙonku ku yi zaman da ya dace da darajar kiran da aka yi muku.
2 Kullum ku kasance da tawaliˈu da sauƙin kai da haƙuri, ku kuma yarda da juna cikin ƙauna.
3 Ku yi ƙwazo sosai ku kiyaye ɗayantakar nan da Ruhu ya ba ku, ta wurin salamar da ta ɗaure ku tare.
4 Jiki ɗaya ne, Ruhu Mai Tsarki kuma ɗaya ne. Haka kuma akwai sa zuciyar nan ɗaya wanda aka kira ku dominsa.
5 Ubangiji ɗaya, bangaskiya ɗaya, kuma baftisma ɗaya,
6 Allah ɗaya, wanda shi Uban dukan mutane, wanda yake a bisa duka, ta wurin duka, a cikin duka kuma.
7 Amma an ba kowannenmu baiwarsa gwargwadon yawan alherin Almasihu.
8 Kamar yadda Kalmar Allah ta ce, “Saˈad da ya hau sama ya ɗauki waɗanda ya kama tare da shi, ya kuma yi wa ˈyan Adam baiwa iri-iri.”
9 Me ake nufi da “ya hau”? Ana nuna cewa, da farko ya sauka har zuwa can ƙarƙashin ƙasa!
10 Shi wanda ya sauka ɗin, shi ne kuma ya hau bisa dukan sammai, domin yă cika sama da ƙasa duka.
11 Shi ne kuma ya yi wa ˈyan Adam baiwa. Ga waɗansu ya ba su zaman manzanni, waɗansu zaman annabawa, waɗansu zaman masu shelar labari mai daɗi, waɗansu zaman makiyaya da masu koyarwa.
12 Ya yi wannan domin yă shirya tsarkaka su yi masa aikin hidima domin a gina jikin Almasihu.
13 Za a ci gaba haka har dukanmu za mu kai ga zaman ɗayantaka ta bangaskiya, ga zaman ɗayantaka kuma cikin sanin Ɗan Allah. Za mu zama cikakkun mutane, mu kuma kai matsayi na dukan cikar Almasihu.
14 An yi wannan kuwa domin kada mu koma halin yara, ko mu zama kamar waɗanda ake yawo da hankalinsu, iskar kowace koyarwa tana tura su tana ɗaukar hankalinsu, mutane masu wayo kuma suna ruɗinsu suna cutarsu.
15 Maimakon haka sai mu faɗi gaskiya cikin ƙauna, mu yi girma cikin alˈamuranmu duka har mu kai ga halin Almasihu wanda shi ne kai na jikinsa, jamaˈar masu bi.
16 Domin shi ne yake mulkin dukan gaɓoɓin jiki. Sun haɗu suna riƙe da juna ta wurin aikin kowace jijiya, har ta wurin aikin kowace gaɓa daidai jikin yake ƙara girma, yana ginuwa da halin ƙauna.
17 To, ina dai faɗa muku, ai, gargaɗi ne nake yi muku cikin sunan Ubangiji cewa, kada ku yi rayuwa kamar marasa sanin Allah, masu tunanin banza.
18 Zuciyarsu cike da duhu take. An raba su kuma da rai wanda Allah yake bayarwa, saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurin kansu.
19 Ga kuwa rashin kunya gare su. Sun ba da kansu ga yin lalata, suna shaˈawar yin kowace irin ƙazanta.
20 Wannan ba shi ne abin da kuka koya game da Almasihu ba!
21 Na tabbata an ba ku labarinsa. Da yake ku mutanensa ne, an koya muku gaskiyar da take cikin Yesu.
22 Ai, abin da aka koya muku, shi ne ku yar da halin mutuntaka wanda kuke ciki a dā, halin da yake lalacewa saboda son abubuwa masu ruɗu.
23 Ya kamata a sabunta tunaninku da hankalinku.
24 Ku ɗauki sabon halin nan da Allah ya halitta bisa ga kamannin kansa. Halin nan kuwa, ya bayyana cikin adalci da zaman tsarki.
25 Saboda haka sai ku rabu da ƙarya! Kowa yă dinga faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓin juna ne.
26 In kun yi fushi, kada yă kai ku ga zunubi. Kada ma fushinku yă daɗe ya kai har rana ta fāɗi.
27 Kada kuma ku ba Shaiɗan wata dama.
28 Kada mai sata yă ƙara yin sata. A maimakon haka sai yă yi aikin gaskiya da hannunsa, har da zai sami wani abin da zai iya taimakon waɗanda ba su da shi.
29 Kada wani ƙazamin zance yă fita daga bakinku, sai dai irin maganar da take da amfani domin ƙarfafawar juna bisa ga bukatarku. Ta haka maganarku za ta zama da amfani ga masu jinta.
30 Ku kuma kula fa, kada ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, gama shi alamar shaida ne na Allah a kanku da zai nuna a ranar fansa cewa ku nasa ne.
31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, da haushi, da fushi, da faɗa, da ɓata suna, da kowace irin ƙiyayyar zuciya.
32 Ku yi wa juna kirki, ku ji tausayin juna, ku yafe wa juna kamar yadda Allah ya yafe muku ta wurin Almasihu.