Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 3

1 Wata rana Bitrus da Yohanna suna tafiya Haikali a lokacin adduˈa, da ƙarfe uku na yamma.

2 A ƙofar da ake ce da ita Kyakkyawar Ƙofa, akwai wani mutum wanda tun haifuwarsa shi gurgu ne. Kowace rana akan ɗauke shi zuwa ƙofar Haikali, domin yă roƙi sadaka daga wurin masu shiga.

3 Da ya ga Bitrus da Yohanna za su shiga Haikalin ke nan, sai ya roƙe su sadaka.

4 Bitrus da Yohanna suka zuba masa ido, Bitrus ya ce, “Dube mu.”

5 Sai kuwa duk hankalin gurgun ya koma kansu, yana tsammani za su ba shi wani abu.

6 Amma Bitrus ya ce, “Azurfa da zinariya kam, ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka. A cikin sunan Yesu Almasihu Banazaret, tashi ka yi tafiya.”

7 Sai Bitrus ya kama hannunsa na dama, ya ɗaga shi. Nan take ƙafafunsa da idanun ƙafafunsa suka yi ƙarfi.

8 Ya yi wuf! Ya miƙe tsaye, ya fara tafiya, ya shiga Haikalin tare da su, yana tafiya yana tsalle yana kuma yabon Allah.

9 Dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana yabon Allah.

10 Suka kuwa gane shi ne mai zama a bakin Kyakkyawar Ƙofa ta Haikalin yana roƙon sadaka. Sai suka yi mamaki ƙwarai da gaske game da abin da ya faru da shi.

11 Saˈad da gurgun nan da aka warkar a Kyakkyawar Ƙofa yake riƙe da Bitrus da Yohanna, sai duk jamaˈa suka zo wurinsu a guje a cikin zauren da ake ce da shi Zauren Solomon, suna mamaki.

12 Da Bitrus ya ga haka, sai ya yi wa jamaˈa jawabi ya ce, “Ku Israˈilawa, don me kuke mamakin wannan? Don me kuma kuke ta kallonmu, sai ka ce da ikon kanmu ne, ko kuwa don aniyarmu cikin bin Allah ne muka sa mutumin nan ya yi tafiya?

13 Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakub, Allahn kakanninmu, shi ya ɗaukaka Bawansa Yesu. Shi ne wanda kuka bashe shi, kuka kuma ƙi shi a gaban gwamna Bilatus, ko da yake Bilatus ya yi ƙoƙari yă sake shi.

14 Amma kuka ƙi Mai Tsarkin nan Mai Adalci, kuka roƙa a sakar muku mai kisan kai,

15 kuka kuwa kashe wanda shi ne Tushen Rai. Amma Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa shaidu ne ga wannan.

16 To, ta ikon sunan Yesu ne, wato ta wurin ba da gaskiya gare shi, shi ne ya ba mutumin nan ƙarfi. Ga mutumin. Kun san shi. Ta wurin bangaskiya cikin Yesu, mutumin nan ya sami cikakkiyar lafiya. Dukanku kuwa shaidun wannan ne.

17 “Yanzu, ˈyanˈuwa, na sani cikin rashin sani ne kuka yi haka, kamar yadda shugabanninku ma suka yi.

18 Amma ta haka Allah ya cika abin da ya faɗa ta bakin annabawa duka cewa, Almasihunsa zai sha wuya.

19 Saboda haka sai ku tuba, ku juyo ga Allah domin a wanke zunubanku, domin Ubangiji yă sabunta zuciyarku,

20 yă kuma aiko da Almasihun da ya zaɓa muku tun dā, wato Yesu.

21 Dole ne Yesu yă zauna a sama, har lokacin da za a mai da dukan abubuwa sabo, kamar yadda Allah ya faɗa tun zamanin dā ta bakin annabawansa masu tsarki.

22 Gama Musa ya ce, ‘Ubangiji Allahnku zai aika muku da wani annabi daga cikin ˈyanˈuwanku, kamar yadda ya aike ni. Dole ne ku saurari dukan abin da zai faɗa muku.

23 Zai zama kuma duk wanda ya ƙi sauraron annabin nan, za a kawar da shi daga cikin jamaˈa.’

24 Hakika, dukan annabawan da suka yi annabci, wato tun daga kan Samaˈila, da waɗanda suka zo daga baya, duk sun yi magana a kan waɗannan kwanakin.

25 Annabcin da aka yi ta wurin annabawa, dominku ne, ku ne kuma za ku ci gādon yarjejeniyar da Allah ya yi wa kakanninku, da ya ce wa Ibrahim, ‘Ta wurin zuriyarka ne dukan kabilun duniya za su sami albarka.’

26 Da Allah ya zaɓi Bawansa, ya fara aiko shi wurinku ne domin yă yi muku albarka yă juyo da kowane ɗayanku daga hanyar muguntarsa.”

Open Bible reader