Hausa Bible
Ayyukan Manzanni 22
1 “Ku ˈyanˈuwa da iyaye, ku saurara in bayyana muku abin da ya faru, domin in nuna cewa ba ni da laifi.”
2 Da suka ji ya yi musu magana da yaren Aramaya, sai suka ƙara yin shiru. Saˈan nan ya ce,
3 “Ni Bayahude ne, an haife ni a Tarsus, ƙasar Kilikiya, amma a nan garin na yi girma. Na yi makaranta a ƙarƙashin Gamaliyel, wanda ya koya mini kome game da Koyarwar kakanninmu. Ina da kishin bautar Allah, kamar yadda dukanku kuke yi a yau,
4 har na tsananta wa masu bin wannan Hanya. Ina kakkashe su, ina ɗaure mutane maza da mata, ina sa su cikin kurkuku.
5 Babban firist ma da dukan majalisar shugabannin jamaˈa za su iya shaidata. Daga wurinsu ne na karɓi wasiƙu zuwa ga ˈyanˈuwanmu Yahudawa a cikin Dimashƙu. Na tafi wurin domin in kama masu bin Hanyar nan waɗanda suke a can ma, in kawo su Urushalima domin a hukunta su.
6 “Ina cikin tafiya, na kusa in kai Dimashƙu da tsakar rana, sai babban haske daga sama ya haskaka kewaye da ni.
7 Sai na fāɗi a ƙasa na kuma ji wata murya tana ce mini, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?’
8 Na amsa na ce, ‘Wane ne kai, maigirma?’ Sai ya ce mini, ‘Ni ne Yesu Banazaret wanda kake tsananta wa.’
9 To, waɗanda suke tare da ni sun ga hasken, amma ba su ji muryar wanda yake magana da ni ba.
10 Sai na tambaya na ce, ‘To, me zan yi, Ubangiji?’ Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Tashi, ka shiga Dimashƙu, a can ne za a gaya maka abin da aka shirya maka ka yi.’
11 Tun da ba na iya gani saboda tsananin hasken nan, waɗanda suke tare da ni suka kama hannuna, suka yi mini jagora zuwa cikin Dimashƙu.
12 “Sai kuma wani mai suna Hananiya ya zo wurina. Shi mai bautar Allah ne bisa ga Koyarwarmu ta Musa, wanda dukan Yahudawan da suke da zama a can suke yabonsa.
13 Ya zo ya ce mini, ‘Ɗanˈuwana Shawulu, ka sāke ganin gari.’ Nan take idanuna suka buɗe, na kuwa gan shi.
14 Sai ya ce, ‘Allahn kakanninmu ya zaɓe ka ka san nufinsa, ka ga Mai Adalcin nan, ka kuma ji magana daga bakinsa.
15 Gama za ka zama mai shaidarsa ga dukan mutane game da abin da ka gani, ka kuma ji.
16 To, yanzu me kake jira? Tashi a yi maka baftisma a wanke zunubanka ta wurin kira ga sunan Ubangiji.’ ”
17 “Bayan da na dawo Urushalima, ina adduˈa a Haikali, sai na ga ruˈuya.
18 A cikin ruˈuyar kuwa na ga Yesu yana ce mini, ‘Yi maza, ka tashi ka bar Urushalima da sauri, don ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.’
19 “Ni kuma na ce, ‘Ubangiji, ai, su ma kansu sun sani cewa a kowace majamiˈa na ɗaɗɗaure waɗanda suka gaskata da kai, na kuma dūke su.
20 Saˈad da kuma aka zub da jinin Istifanus mai shaidarka, ni da kaina ina tsaye a wurin, ina goyon bayan abin da aka yi, har ma ina gadin tufafin waɗanda suka kashe shi.’
21 “Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Tashi ka tafi, zan aike ka can nesa wurin waɗanda ba Yahudawa ba.’ ”
22 Taron sun yi ta sauraron Bulus har ya iso wannan kalma, sai suka yi ihu suka ce, “A kashe shi! A raba irin mutumin nan da duniya, bai kamata yă rayu ba!”
23 Sai suka dinga ihu suna jefa mayafansu, suna tā da ƙura.
24 Saboda haka sai shugaban ya ba da umarni a kai Bulus barikin soja a bincike shi da bulala, don a nemi dalilin da ya sa taron suke yi masa ihu haka.
25 Amma bayan da suka ɗaure shi domin su yi masa bulala, sai Bulus ya ce wa babban sojan Roma da yake tsaye kusa, “Ashe, daidai ne bisa ga doka ka yi wa mutumin da yake da ˈyancin Roma bulala, ba tare da an yi masa shariˈa ba?”
26 Da babban sojan Roma ya ji haka, sai ya je wurin shugaban ya ce masa, “Me kake shirin yi ne? Mutumin nan fa yana da ˈyancin Roma.”
27 Sai shugaban ya zo ya ce wa Bulus, “Gaya mini gaskiya, kai kana da ˈyancin Roma?” Sai Bulus ya ce, “I.”
28 Sai shugaban ya ce, “Ni fa da kuɗi mai yawa na sami ˈyancin nan.” Bulus ya ce, “Ni kuwa da shi aka haife ni.”
29 Saboda haka waɗanda suke shirin bincikensa suka ja baya nan da nan. Shi ma shugaban da ya gane Bulus mai ˈyancin Roma ne sai ya ji tsoro, ga shi kuwa ya riga ya ɗaure shi.
30 Washegari kuma shugaban yana so yă san ainihin ƙarar da Yahudawa suke yi game da Bulus, sai ya kunce shi, ya ba da umarni manyan firistoci da dukan majalisa su taru. Saˈan nan ya kawo Bulus ya sa shi yă tsaya a gabansu.