Hausa Bible
Ayyukan Manzanni 14
1 To, a Ikoniya, Bulus da Barnaba suka shiga majamiˈar Yahudawa kamar yadda sun saba. Suka yi waˈazi, har mutane masu yawa, Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba, suka ba da gaskiya.
2 Amma Yahudawan da suka ƙi gaskatawa, suka zuga waɗanda ba Yahudawa ba, suka ɓata tsakaninsu da ˈyanˈuwa masu bi.
3 Sai Bulus da Barnaba suka daɗe a nan sosai, suna waˈazi babu tsoro bisa ga ikon Ubangiji. Ubangiji kuwa ya yi shaidar kalmar alherinsa ta wurin ba da iko a yi alamu da ayyukan ban mamaki ta hannunsu.
4 Amma mutanen garin suka rabu kashi biyu, waɗansu suna goyon bayan Yahudawa, waɗansu kuma suna goyon bayan manzannin.
5 Sai waɗanda ba Yahudawa ba, da Yahudawa, tare da shugabanninsu suka yi shiri domin su wulaƙanta manzannin, su jejjefe su da duwatsu.
6 Da manzannin suka ji haka, sai suka gudu zuwa biranen Likoniya, wato Listira da Darbe, da kuma kewayensu.
7 A wurin suka ci gaba da waˈazin labari mai daɗi.
8 A Listira kuwa akwai wani mutum wanda shi gurgu ne, bai taɓa yin tafiya ba tun da aka haife shi. Yana zaune,
9 yana sauraron waˈazin Bulus. Sai Bulus ya zuba masa ido. Da Bulus ya ga mutumin yana da bangaskiyar da za a warkar da shi,
10 sai ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Tashi ka tsaya kan ƙafafunka.” Mutumin kuwa ya tashi ya fara tafiya.
11 Da taron suka ga abin da Bulus ya yi, suka ɗaga murya gaba ɗaya suna cewa da yaren Likoniya, “Lallai, alloli sun sauko mana da siffar mutane!”
12 Sai suka ba Barnaba suna Zeyus, Bulus kuwa suka ce da shi Hermes, domin shi ne shugaban magana.
13 Sai firist na tsafin Zeyus, wanda ɗakin gunkinsa yake a bayan gari, ya kawo shanu da adon fulawa a ƙofar gari. Sarkin tsafin da jamaˈa suna so su yi wa manzannin hadaya.
14 Amma da manzannin nan Barnaba da Bulus suka ji haka, sai suka yayyage rigunansu don ɓacin rai, suka shiga cikin taron da gudu, suna ɗaga murya suna cewa,
15 “Don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kamarku, mun dai kawo muku labari mai daɗi ne, domin ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku kuma juyo ga Allah Mai Rai, wanda ya halicci sama da ƙasa, da teku, da kuma dukan abin da yake cikinsu.
16 A zamanin dā, ya bar dukan alˈummai su yi tafiya a hanyoyin da suka ga dama.
17 Duk da haka kuwa bai taɓa barin kansa babu shaida ba, saboda yana yin alherin ba ku ruwan sama da damina mai albarka. Yana ƙosar da ku da abinci a daidai lokaci, yana kuma sa ku yi farin ciki.”
18 Duk da waɗannan maganganu ma da kyar suka hana jamaˈar nan su yi musu hadaya.
19 Amma waɗansu Yahudawa suka zo daga Antakiya da Ikoniya suka rinjayi taron, suka jejjefi Bulus, suka ja shi zuwa bayan gari, suna tsammani ya mutu.
20 Amma da masu bi suka kewaye shi, sai ya tashi ya koma cikin birni. Washegari kuma ya tafi Darbe tare da Barnaba.
21 Bayan da Bulus da Barnaba suka yi waˈazin labari mai daɗi a Darbe, sun kuma sami almajirai da yawa, suka koma Listira, da Ikoniya, da kuma Antakiya ta Bisidiya.
22 Suna ƙarfafa masu bi, suna yi musu gargaɗi su tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya. Suna cewa, “Sai tare da azaba mai yawa za mu shiga mulkin Allah.”
23 Bayan da suka kuma zaɓa musu dattawa a kowace jamaˈar masu bi, tare da adduˈa da azumi suka miƙa su ga Ubangiji wanda suka gaskata da shi.
24 Saˈan nan sun bi ta ƙasar Bisidiya zuwa Famfiliya.
25 Da kuma suka faɗa kalmar Allah a Ferga, sai suka tafi Ataliya.
26 Daga nan kuma suka shiga jirgin ruwa suka koma Antakiya, inda tun dā aka yi musu adduˈa cewa alherin Allah yă kiyaye su cikin aikin nan yanzu da suka gama.
27 Da suka iso, suka tara jamaˈar masu bi suka ba da labarin dukan abin da Allah ya yi ta wurinsu, da kuma yadda ya buɗe wa waɗanda ba Yahudawa ba ƙofar bangaskiya.
28 Sun ɗan daɗe a can tare da masu bi.