Skip to content

Hausa Bible

Titus 3

1 Ka tuna wa mutanenka su miƙa kansu ga shugabanni da kuma masu mulki, su yi musu biyayya, su kuma kasance a shirye domin yin kowane irin kyakkyawan aiki.

2 Kada su yi wa wani muguwar magana, kuma su zauna cikin salama, su kuma kasance da sauƙin kai, suna yi wa kowa cikakken tawaliˈu.

3 Gama mu ma a dā wawaye ne, marasa biyayya, aka kuwa ruɗe mu, mun zama bayin shaˈawace-shaˈawace da kwaɗayi iri-iri, muka kuma yi rayuwarmu cikin kishi da ƙiyayyar zuciya. Mutane suka ƙi mu, mu kuma muka ƙi su.

4 Amma a saˈad da aka bayyana alheri da ƙaunar Allah Mai Cetonmu,

5 sai Allah ya cece mu. Wannan kuwa ba domin mun yi ayyuka na adalci ba, amma bisa ga jinƙansa ne ya cece mu ta wurin wankan nan na Ruhu Mai Tsarki wanda ya ba mu sabuwar haifuwa da sabuntawa.

6 Ruhu Mai Tsarkin nan ne aka zubo a yalwace a kanmu ta wurin Yesu Almasihu Mai Cetonmu.

7 Ya yi wannan domin ta wurin alherinsa mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah, kuma mu zama masu gādon rai madawwamin nan da muka sa zuciya a kai.

8 Maganar nan tabbatacciya ce. Ina so ka ƙarfafa waɗannan abubuwa sosai, domin waɗanda suka ba da gaskiya ga Allah su yi hankali su miƙa kansu ga aiki nagari. Waɗannan abubuwa kuwa suna da kyau ainun, suna kuwa da amfani ga kowa.

9 Amma ka guje wa gardamar banza, da lissafin sunayen kakanni, da rarrabuwa, da kuma yawan jayayya game da Koyarwar Musa, saboda ba su da amfani kuma banza ne.

10 Amma ga mutum mai kawo rabuwa, bayan da ka gargaɗe shi da farko da na biyu, sai ka rabu da shi.

11 Ka sani cewa irin mutumin nan ɓatacce ne, kuma ya hukunta kansa ta wurin zunubansa.

12 Saˈad da na aika Artimas ko Tikikus wurinka, sai ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina a Nikafolis, saboda ina da niyyar cin damina a can.

13 Ka kuma yi iyakacin ƙoƙarinka ka taimaki Zenas lauyan nan, da Afollos su kama hanya. Ka kuma tabbatar cewa ba su rasa kome ba.

14 Dole mutanenmu su dinga koyar miƙa kansu ga aikata ayyuka masu kyau, domin su iya ba da taimako wajen biyan muhimman bukatu. Kada su yi rayuwa marar amfani.

15 Duk waɗanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gai da waɗanda suke ƙaunarmu, waɗanda muke tare da su cikin bangaskiya. Alherin Allah yă kasance tare da ku duka. Amin.

Open Bible reader