Hausa Bible
Romawa 16
1 Ina gabatar muku ˈyarˈuwarmu Fibi wadda na shaida cewa ita mai kirki ce. Ita kuwa mai hidimar jamaˈar masu bin Yesu ce a Kankiriya.
2 Ku karɓe ta cikin sunan Ubangiji yadda ya dace a karɓi tsarkaka. Ku kuma ba ta kowane irin taimakon da take bukata daga gare ku, domin ita kanta ta taimaki mutane da yawa, duk da ni ma.
3 Ku gai da Biriskila da Akila, abokan aikina cikin Almasihu Yesu.
4 Su kuwa sun ba da ransu har kusan mutuwa saboda ni. Ba ni kaɗai ne mai godiya a gare su ba, har ma da dukan jamaˈar masu bi ta waɗanda ba Yahudawa ba.
5 Ku gai da jamaˈar masu bi waɗanda suke taruwa a gidansu. Ku gai da Afanitus, abokina na ƙwarai, wanda shi ne na farko wanda ya zama mai bin Almasihu a duk ƙasar Asiya.
6 Ku gai da Maryamu wadda ta sha famar aiki sosai saboda ku.
7 Ku gai da Andaronikus da Yuniya, waɗanda Yahudawa ne kamar ni, waɗanda kuma aka ɗaure su a kurkuku tare da ni. Su kuwa mutane ne da an san su sosai a cikin manzanni, kuma sun riga ni ba da gaskiya cikin Almasihu.
8 Ku gai da Amfiliyatus, abokina na ƙwarai cikin zumuncin Ubangiji.
9 Ku gai da Urbanus abokin aikinmu cikin Almasihu, da kuma abokina Sitakis.
10 Ku gai da Afalis wanda amincinsa cikin Almasihu tabbatacce ne. Ku gai da iyalin Aristobulus.
11 Ku gai da Hirudiyan wanda shi ma Bayahude ne. Ku gai da waɗanda suke cikin Ubangiji a iyalin Narkisus.
12 Ku gai da Tirayifina da Tirayifusa, matan nan masu fama cikin aikin Ubangiji. Ku gai da Farsis, abokiyata da nake ƙauna, wadda kuma ta sha famar aiki sosai saboda Ubangiji.
13 Ku gai da Rufus wanda lallai shi sananne ne a cikin Ubangiji. Ku kuma gai da mamarsa wadda ta ɗauke ni kamar ɗanta.
14 Ku gai da Asinkiritus, da Filigona, da Hermes, da Faturobas, da Harmas da kuma dukan ˈyanˈuwan da suke tare da su.
15 Ku gai da Filologus, da Yuliya, da Niriyus da ˈyarˈuwarsa, da Olimfas, da duk tsarkakan da suke tare da su.
16 Ku gai da juna da sumbar ƙauna mai tsarki. Dukan jamaˈar masu bin Almasihu suna gai da ku.
17 ˈYanˈuwana, ina dai roƙonku ku mai da hankali da masu kawo rabe-rabe tsakaninku, waɗanda suke sa ku dalilin tuntuɓe, suna kuma gāba da koyarwar da kuka karɓa. Ku yi nesa da su!
18 Don kuwa irin waɗannan mutane ba Almasihu Ubangijinmu suke bauta wa ba, sai dai cikinsu. Ta wajen daɗin bakinsu da yabon ƙarya sukan ruɗi masu jinsu. Masu jinsu kuwa masu tunanin yara ne.
19 Kowa ya ji labari yadda kuke yin biyayya, wannan kuwa ya sa ina farin ciki saboda ku. Amma ina so ku zama masu hikima ga abin da yake mai kyau, ku kuma zama marasa laifi ga duk abin da ya shafi mugunta.
20 Allah mai ba da salama kuwa zai tattaka Shaiɗan, yă kuma ba ku iko a kansa, ba da daɗewa ba, Alherin Ubangijinmu Yesu yă kasance tare da ku.
21 Timoti, abokin aikina, yana gaishe ku, haka ma Lushiyus, da Yason, da Sosifata, waɗanda su ma Yahudawa ne.
22 Ni Tartiyus, mai rubuta wannan wasiƙa, ina gaishe ku cikin Ubangiji.
23 Gayus, wanda ya karɓe ni a gidansa, kuma mai karɓar dukan jamaˈar masu bi a gidansa, yana gaishe ku. Erastus, maˈajin gari, da kuma ɗanˈuwanmu Kwartus suna gaishe ku.
24 Bari alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă kasance tare da ku duka. Amin.
25 Bari ɗaukaka ta tabbata ga Allah wanda yake da iko yă kafa ku cikin bangaskiya bisa ga labari mai daɗin nan da nake waˈazinsa a kan Yesu Almasihu. Labari mai daɗin kuwa asiri ne wanda aka ɓoye tun zamanan dā,
26 amma a yanzu an fitar da shi a fili ta wajen rubuce-rubucen annabawa. Bisa ga umarnin Allah madawwami kuma an bayyana shi ga dukan alˈummai, domin su ba da gaskiya su kuma yi biyayya.
27 Bari ɗaukaka ta tabbata ga Allah, wanda shi ne kaɗai mai hikima, ta wurin Yesu Almasihu har abada! Amin.