Skip to content

Hausa Bible

Romawa 10

1 To, ˈyanˈuwana, abin da na fi so fiye da kome shi ne Israˈilawa su sami ceto. Adduˈar da nake yi wa Allah saboda su ke nan.

2 Na dai shaida cewa suna da kishin bautar Allah, amma wannan kuwa ba tare da cikakken sani ba.

3 Tun da yake ba su san hanyar da Allah yake sa mutane su zama masu adalci ba, kuma suna ƙoƙari su kafa tasu hanyar zaman masu adalci a gaban Allah, sai wannan ya sa ba su miƙa kansu ga hanyar da Allah yake sa mutane su zama masu adalci ba.

4 Gama Almasihu shi ne ƙarshen Koyarwar Musa, domin duk mai ba da gaskiya yă sami zaman mai adalci a gaban Allah.

5 Musa ya yi rubutu game da adalcin da ake samuwa ta wurin bin Koyarwarsa cewa, “Duk wanda ya bi Koyarwar nan zai rayu ta wurinta.”

6 Amma ga abin da Rubutacciyar Kalmar Allah ta ce game da adalcin da ake samuwa ta wurin bangaskiya, “Kada ka ce a cikin zuciyarka, ‘Wane ne zai hau sama?’ ” Wato, domin yă sauko da Almasihu.

7 “Ko kuwa ka ce, ‘Wane ne zai sauko har wurin zaman matattu?’ ” Wato, domin yă tā da Almasihu daga matattu.

8 Abin da Rubutacciyar Maganar Allah take faɗin shi ne, “Maganar Allah tana kusa da kai, tana a bakinka, da kuma a cikin zuciyarka.” Maganar nan kuwa ita ce saƙon bangaskiyar da muke waˈazinta.

9 Idan ka shaida da bakinka cewa Yesu shi ne Ubangiji, ka kuma ba da gaskiya cikin zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za a cece ka.

10 Gama da zuciya ne akan ba da gaskiya a sami zaman marar laifi a gaban Allah, kuma da baki ne akan ba da shaida a sami ceto.

11 Kamar yadda Rubutacciyar Maganar Allah ta ce, “Duk mai ba da gaskiya gare shi ba zai sha kunya ba.”

12 Gama ba bambanci tsakanin Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba. Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa, shi ne kuma yakan ba da albarku masu yawa ga duk masu kira gare shi.

13 Kamar yadda Rubutacciyar Maganar Allah ta ce, “Duk wanda ya kira ga sunan Ubangiji zai sami ceto.”

14 Amma ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata da shi ba? Ta yaya za su gaskata da wanda ba su taɓa jin labarinsa ba? Ta yaya kuma za su ji in babu wanda zai yi musu waˈazi?

15 Ta yaya kuma masu waˈazi za su yi waˈazi in ba a aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ina misalin ban shaˈawar masu kawo labari mai daɗi!”

16 Amma ba dukan Israˈilawa ne suka yarda da labari mai daɗin ba. Kamar yadda Ishaya ya ce, “Ya Ubangiji, wa ya gaskata da saƙon da ya ji daga gare mu?”

17 Saboda haka akan ba da gaskiya ta wurin jin saƙon ne, kuma akan ji saƙon ta waˈazi a kan Almasihu ne.

18 Amma ina tambaya, “Wai gaskiya ne ba su ji ba?” Ai, sun ji. Gama Rubutacciyar Maganar Allah ta ce, “Muryar saƙonsu ta bi ta duniya duka, kalmominsu sun kai iyakar duniya.”

19 Ina sāke tambaya. “Wai Israˈilawa ba su gane ba ne?” Da farko, Musa ya amsa cewa Allah ya ce, “Zan sa ku ku yi kishin jamaˈar da ba alˈumma ba ce, ta wurin alˈumma marar wayo zan sa ku ku yi fushi.”

20 Saˈan nan kuma Ishaya ya yi ƙarfin hali har da cewa Allah ya ce, “Waɗanda ba su neme ni ba, su ne na sa suka same ni. Ga waɗanda ba su tambaye ni ba, na bayyana kaina.”

21 Amma game da Israˈila, Allah kuma ya ce, “Duk yini na miƙa hannuwana ga jamaˈa masu rashin biyayya da masu ƙin ji.”

Open Bible reader