Hausa Bible
Filibiyawa 2
1 Kuna samun ƙarfafawa saboda ku na Almasihu ne? Ko kuna samun taˈaziyya ta wurin ƙaunarsa? Ko kuna da zumunci cikin Ruhu? Ko kuma kuna da ƙauna da tausayi a zuciyarku?
2 To, in kuna da waɗannan, ina roƙonku ku sa farin cikina yă cika ta wurin kasancewarku da tunani ɗaya, da ƙauna ɗaya, da nufi ɗaya.
3 Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai da sauƙin kai. Amma cikin sauƙin kai kuma bari kowa yă ɗauka ɗanˈuwansa da muhimmanci fiye da kansa.
4 Kada ku kula da kanku kaɗai, amma ku kula da waɗansu kuma.
5 Bari ku kasance da hali irin na Almasihu Yesu, wato,
6 Ko da yake shi Allah ne, bai mai da kasancewarsa da Allah abin da zai riƙe da ƙarfi ba,
7 sai dai ya mai da kansa kamar ba kome ba, ya ɗauki matsayin bawa, cikin siffar ɗan Adam aka haife shi, ya kuma bayyana cikin kamannin mutum.
8 Ban da haka ma, a cikin kamannin mutum, ya ƙasƙantar da kansa ta wurin yin biyayya, biyayyar da ta kai shi har ga mutuwa, mutuwa a kan gicciye.
9 Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi fiye da kome, ya kuma ba shi sunan nan da ya fi kowane suna,
10 domin ga sunan nan Yesu kowace gwiwa za ta durƙusa, a sama, da nan duniya, da can ƙarƙashin duniya,
11 kowane harshe kuma yă shaida cewa Yesu Almasihu Ubangiji ne, domin a ɗaukaka Allah Uba.
12 Saboda haka, ya ku waɗanda nake ƙauna, ina roƙonku, kamar yadda kullum kuke yi mini biyayya saˈad da ina tare da ku, yanzu ma da ba na nan tare da ku, ku ƙara yin biyayya. Ku yi aiki da ƙwazo yadda sakamakon cetonku zai fita a fili, ku yi shi cikin tsoron Allah da kuma rawar jiki.
13 Gama Allah shi ne yake aiki a zuciyarku, shi ne yake sa ku yi niyya ku kuma yi aiki bisa ga kyakkyawan nufinsa.
14 Duk abin da za ku yi, kada ku yi shi da gunaguni ko gardama,
15 domin ku zama marasa laifi, masu tsarki, ˈyaˈyan Allah marasa tabo. Kuna zama ne a cikin muguwar tsara masu rayuwar kwana-kwana, inda kuke haskakawa a cikinsu kamar haskoki a duniya,
16 kuna kuma miƙa musu zancen rai. Wannan zai sa a Ranar da Almasihu zai dawo in yi taƙama cewa dukan famar da yi da wahalar da na sha, ba a banza suke ba.
17 Bangaskiyarku da aikinku a cikin Ubangiji kamar hadaya ne a gare shi, kuma ko za a zub da jinina a kan hadayar nan, zan yi murna in yi hadayar nan da farin ciki tare da ku duka.
18 Haka kuma sai ku yi farin ciki, ku yi murna tare da ni.
19 Ina sa zuciya cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika Timoti zuwa wurinku ba da daɗewa ba, domin ni ma in ƙara samun ƙarfafawa ta wurin jin labarinku.
20 Ba ni da wani kamarsa wanda ya damu da ku sosai.
21 Sauran dai, abin da ya shafe kansu ne kawai sun damu da shi, ba abin da ya shafi Yesu Almasihu ba.
22 Ai, kun san yadda Timoti yake, yadda muka yi aikin shelar labari mai daɗi tare kamar ɗa da babansa.
23 Saboda haka ina fata zan aika shi da zarar na ji abin da zai faru da ni.
24 Idan kuma Ubangiji ya yarda, ni ma zan zo ba da daɗewa ba.
25 Na ga ya kamata in aika muku da ɗanˈuwana Abaforiditus. Shi abokin aikina ne, abokin famata kuma, wanda kuka aiko yă yi mini hidima.
26 Yana marmari yă gan ku duka, har ma ya damu sosai saboda kun ji ya yi rashin lafiya.
27 Lallai ya yi rashin lafiya har ma ya kusan mutuwa. Amma Allah ya ji tausayinsa, ba shi kaɗai ba, har ma da ni. Da ba haka ba, da baƙin ciki zai yi mini yawa.
28 Shi ya sa na yi niyya sosai in aike shi domin ku ji daɗin sāke ganinsa, ni kuma in rage damuwata.
29 Ku karɓe shi da murna sosai saboda Ubangiji. A girmama irinsu yadda ya kamata,
30 gama ya kusa yă mutu domin aikin Almasihu, yana ba da ransa domin yă yi mini taimakon da ku ba ku iya yi ba.