Skip to content

Hausa Bible

Matiyu 4

1 Saˈan nan Ruhu Mai Tsarki ya kai Yesu cikin daji domin Shaiɗan yă gwada shi.

2 Yesu ya yi azumi kwana arbaˈin dare da rana. Daga baya kuwa yunwa ta kama shi.

3 Sai Shaiɗan ya zo ya ce masa, “Idan kai Ɗan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama burodi.”

4 Yesu ya amsa ya ce, “An rubuta a cikin Rubutacciyar Maganar Allah cewa, “ ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga wurin Allah.’ ”

5 Sai Shaiɗan ya kai shi Urushalima birni mai tsarki ya kai shi can bisa Haikali.

6 Ya ce masa, “Idan kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle ka fāɗi ƙasa, gama a rubuce yake cewa, “ ‘Zai ba da umarni ga malaˈikunsa su tsare ka. Za su tare ka da hannuwansu domin kada ka buga ƙafafunka a dutse.’ ”

7 Sai Yesu ya ce masa, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka!’ ”

8 Sai Shaiɗan ya sāke kai shi kan wani tudu mai tsawo sosai, ya nuna masa dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu.

9 Ya kuma ce masa, “Dukan waɗannan zan ba ka idan ka durƙusa a gabana ka yi mini sujada.”

10 Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan kai Shaiɗan! Gama a rubuce yake cewa, “ ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta masa.’ ”

11 Saˈan nan Shaiɗan ya bar shi. Sai malaˈiku suka zo suka yi masa hidima.

12 Da Yesu ya ji an kama Yohanna, sai ya tashi ya tafi Galili.

13 Ya kuma bar Nazaret ya koma Kafarnahum da zama, wadda take can bakin teku, a kan iyakar yankin Zebulun da Naftali,

14 domin a cika abin da annabi Ishaya ya faɗa cewa,

15 “Yankin zuriyar Zebulun da na Naftali a Galili, yankin nan na mutanen da ba Yahudawa ba, yankin da ya miƙe daga Tekun Meditereniya har zuwa yankin ƙetaren Kogin Yodan,

16 masu zama cikin duhu sun ga babban haske, masu zama a ƙasar inuwar mutuwa kuwa haske ya ɓullo musu.”

17 Tun daga lokacin nan, Yesu ya fara waˈazi, yana cewa, “Ku tuba domin mulkin sama ya yi kusa.”

1i8 Yesu yana tafiya a gefen Tekun Galili ke nan, sai ya ga waɗansu ˈyanˈuwa guda biyu, Siman da ake ce da shi Bitrus, da ɗanˈuwansa Andarawus, suna jefa ragar kamun kifi a teku, domin su masu kamun kifi ne.

19 Sai Yesu ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masu jawo mutane zuwa wurina.”

20 Nan da nan suka bar kayansu na kamun kifi suka bi shi.

21 Da ya ci gaba da tafiya, sai ya ga waɗansu ˈyanˈuwa guda biyu kuma, Yakub ɗan Zabadi, da ɗanˈuwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da babansu Zabadi, suna gyaran ragar kamun kifi. Sai ya kira su.

22 Nan da nan suka bar jirgin duk da babansu, suka bi shi.

23 Yesu ya yi ta zazzaga dukan ƙasar Galili, yana koyarwa a majamiˈunsu, yana waˈazin labari mai daɗi na mulkin Allah. Yana kuma warkar da kowane irin ciwo da rashin lafiya na mutane.

24 Ta haka kuwa aka san da shi a cikin ƙasar Suriya gaba ɗaya. Aka yi ta kawo masa dukan marasa lafiya, da masu fama da ciwo iri-iri, da masu shan wuya, da masu aljanu, da masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su duka.

25 Taron mutane da yawa suka bi shi daga Galili, da kuma daga yankin Garuruwa Goma, da Urushalima, da yankin Yahudiya, har ma daga ƙetaren Kogin Yodan.

Open Bible reader