Hausa Bible
Matiyu 18
1 A lokacin nan almajiran suka zo wurin Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Wa ya fi girma duka a cikin mulkin sama?”
2 Sai ya kira wani ƙaramin yaro, ya sa shi a tsakiyarsu,
3 ya ce, “Hakika ina gaya muku, idan ba kun sāke, kun zama kamar ƙananan yara ba, ba za ku taɓa shiga mulkin sama ba.
4 Duk wanda ya ɗauki kansa ba a bakin kome ba kamar ƙaramin yaron nan, shi ne ya fi girma a mulkin sama.
5 Duk wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan saboda ni, ni ne ya karɓa.”
6 “Amma fa, duk wanda ya sa ɗaya daga cikin yara ƙananan nan da suka gaskata da ni yă yi zunubi, zai fi wa mutumin a rataya babban dutsen niƙa a wuyansa, a kuma nutsar da shi a teku mai zurfi.
7 Kaiton duniya saboda dalilan yin zunubi! Dole ne dalilan yin zunubi su zo, amma kaiton wanda shi ne dalilin.
8 “Idan kuwa hannunka ko ƙafarka yana sa ka ka yi zunubi, ka yanke shi ka yar. Zai fi maka ka shiga rai na har abada da hannu ko ƙafa ɗaya ko gurgu, da a jefa ka cikin wutar da ba ta taɓa mutuwa da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu.
9 Idan kuma idonka yana sa ka ka yi zunubi, sai ka cire shi ka yar. Zai fi maka ka shiga rai na har abada da ido ɗaya, da a jefa ka cikin gidan wutar da ba ta taɓa mutuwa da idanu biyu.”
10 “Ku kula, kada ku rena ko ɗaya daga cikin yara ƙananan nan, gama ina faɗa muku, malaˈikunsu a sama kullum suna ganin fuskar Ubana wanda yake cikin sama.
11 Gama ɗan Mutum ya zo ne yă ceci waɗanda suka ɓata.
12 “Me kuke tsammani, idan makiyayi yana da tumaki guda ɗari, sai ɗaya daga cikinsu ta ɓata, ba zai bar sauran casaˈin da taran a tuddai suna kiwo yă je neman ɗayarsu da ta ɓata ba?
13 Kuma idan ya same ta, gaskiya ina faɗa muku, murnar da yake yi a kanta, ta fi ta casaˈin da taran da ba su ɓata ba.
14 Haka ma, ba nufin Ubanku wanda yake cikin sama ba ne ɗaya daga cikin yara ƙananan nan yă ɓata.”
15 “Idan ɗanˈuwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa ya yi maka laifi, kai da shi kaɗai. Idan ɗanˈuwan ya saurare ka, ka sāke maido da ɗanˈuwanka ke nan.
16 Amma idan bai saurare ka ba, sai ka sāke zuwa wurinsa tare da mutum ɗaya ko biyu domin a tabbatar da kowace magana daga bakin shaidu biyu ko uku.
17 Idan ɗanˈuwan ya ƙi sauraronsu, sai ka faɗa wa jamaˈar masu bi, idan kuma har ya ƙi saurari jamaˈar masu bi, ka mai da shi kamar wanda bai san Allah ba, ko mai zunubi wanda ya ƙi tuba.
18 “Hakika ina gaya muku, duk abin da kuka ɗaure a duniya, a ɗaure yake a sama. Duk abin da kuka kunce a duniya kuma a kunce yake a sama.
19 “Ina sāke gaya muku, idan mutum biyu daga cikinku a duniya suka yarda su roƙi wani abu, Ubana wanda yake cikin sama zai yi musu.
20 Gama duk inda mutum biyu ko uku suka taru cikin sunana, ina tare da su.”
21 Ana nan sai Bitrus ya zo ya ce wa Yesu, “Ubangiji, sau nawa ɗanˈuwana zai yi mini laifi in yafe masa? Sau bakwai?”
22 Yesu ya ce masa, “Ba sau bakwai ba, amma dai bakwai sau sabaˈin.
23 Saboda haka, za a kwatanta mulkin sama da wani sarkin da yake so yă ƙirga dukiyarsa da take hannun bayinsa.
24 Da sarkin ya fara ƙirgawa, sai aka kawo masa wani mutum wanda yake bin bashin azurfa wanda mutumin ba zai iya biya a duk rayuwarsa ba.
25 Da ya kāsa biya, sai sarkin ya sa a sayar da shi da matarsa da ˈyaˈyansa da duk abin da yake da shi domin a biya kuɗin.
26 Sai bawan ya durƙusa a gabansa yana roƙo ya ce, ‘Ka yi haƙuri, zan biya ka kome.’
27 Sai sarkin ya ji tausayin bawan, ya sake shi, ya yafe masa bashin.
28 “Amma wannan bawan daga fitarsa, sai ya tarar da wani abokin aikinsa da yake bin bashin azurfa kaɗan kawai, ya shaƙe masa wuya ya ce, ‘Ka biya ni abin da nake binka.’
29 Sai abokin aikinsa ya durƙusa ya roƙe shi ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka.’
30 Amma bawan ya ƙi, ya kuma je ya sa shi a kurkuku, sai ya biya bashin.
31 Da abokan aikinsa suka ji abin da ya faru, sai ba su ji daɗi ba. Sai suka je suka faɗa wa sarkin duk abin da ya faru.
32 Sai sarkin kuwa ya kira bawan ya ce masa, ‘Kai mugun bawa ne. Na yafe maka duk bashin nan saboda ka roƙe ni.
33 Ashe, bai kamata ka ji tausayin abokin aikinka kamar yadda na ji tausayinka ba?’
34 Sarkin ya ji haushi sosai, ya sa a ba shi wuya har sai ya biya dukan bashin.
35 Haka kuwa Ubana wanda yake cikin sama zai yi wa kowannenku da ya ƙi yafe wa ɗanˈuwansa da zuciya ɗaya.”