Hausa Bible
Luka 3
1 A cikin shekara ta goma sha biyar na mulkin Kaisar Tibariya ne, Buntus Bilatus yana mulkin yankin Yahudiya. Hirudus yana mulkin Galili. Ɗanˈuwansa Filibus yana mulkin Ituriya da Tarakunitas. Lisaniyas yana mulkin Abilene,
2 kuma Hannana da Kayafa su ne manyan firistoci. A wannan lokaci kuwa sai kalmar Allah ta zo wa Yohanna ɗan Zakariya a daji.
3 Sai Yohanna ya je koˈina a dukan yankin Kogin Yodan, yana waˈazi cewa mutane su tuba, a yi musu baftisma domin a yafe musu zunubansu.
4 Kamar yadda yake a rubuce a cikin Littafin Annabi Ishaya cewa, “Murya mai kira a daji tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku gyara hanyoyinsa.
5 Za a ciccika kowane kwari, za a kwantar da kowane dutse da kowane babban tudu. Za a miƙe hanyar da take da kwana-kwana, a gyara mummunar hanya domin ta yi kyau.
6 Dukan ˈyan Adam za su ga ceton Allah!’ ”
7 Saboda haka ne, Yohanna ya ce wa taron jamaˈar da suka zo domin yă yi musu baftisma, “Ku ƙungiyar mugayen macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa hukuncin nan mai zuwa?
8 Ku haifar da halin rayuwa mai kyau wanda zai nuna cewa kun tuba, kamar itacen da ya haifi ˈyaˈya masu kyau. Kada ku yi tunani a zuciyarku cewa, ‘Ibrahim ne babanmu.’ Gama ina faɗa muku, Allah yana da iko yă tā da ˈyaˈya domin Ibrahim daga duwatsun nan.
9 An riga an sa bakin gatari a gindin itace. Duk itacen da bai haifi ˈyaˈya masu kyau ba, sai a sare shi a jefa a wuta.”
10 Sai mutane suka tambaye shi, “Me za mu yi ke nan?”
11 Ya amsa musu ya ce, “Duk wanda yake da riguna biyu, yă raba da wanda ba shi da ko ɗaya, wanda yake da abinci shi ma yă yi haka.”
12 Masu karɓar haraji suka zo domin a yi musu baftisma, suka tambaye shi suka ce, “Malam, me za mu yi?”
13 Ya ce musu, “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa.”
14 Sojoji ma suka tambaye shi, “Mu fa? Me za mu yi?” Sai ya ce musu, “Kada ku sa wa mutane dole su ba ku kuɗi, kuma kada ku yi ƙarya a kansu saboda sun ƙi su ba ku. Ku gode da abin da ake biyanku.”
15 Da yake mutane suna jiran zuwan Almasihu, sai dukansu suka yi tunani a zuciya ko Yohanna shi ne Almasihu ɗin.
16 Sai Yohanna ya ce wa dukansu, “Ni, ina yi muku baftisma da ruwa ne, amma akwai wani wanda yake zuwa wanda ya fi ni girma, har ban isa in kunce igiyar takalmansa ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da wuta kuma.
17 Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, kuma yă tattara alkamarsa yă sa cikin rumbunsa. Amma zai ƙona yayin da wutar da ba a iya kashewa.”
18 Da waɗansu gargaɗi masu yawa, Yohanna ya yi wa mutane waˈazin labari mai daɗi.
19 Amma Yohanna ya tsawata wa gwamna Hirudus, saboda shi Hirudus ya auri Hirudiya, matar ɗanˈuwansa Filibus, ya kuma yi waɗansu mugayen abubuwa.
20 A ƙarshe, Hirudus ya ƙara ɓata alˈamarin da izni a kama Yohanna a kulle shi a kurkuku.
21 Bayan da aka yi wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana adduˈa, sai sama ya buɗe,
22 Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kansa a kamannin kurciya. Sai aka ji wata murya daga sama ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna. Ina jin daɗinka ƙwarai.”
23 Lokacin da Yesu ya fara aikinsa na koyarwa, yana da shekara wajen talatin ne a duniya. Mutane sun ɗauke shi a kan shi ɗan Yusuf ne. Yusuf ɗan Heli,
24 Heli ɗan Mattat, Mattat ɗan Lawi, Lawi ɗan Malki, Malki ɗan Yanna, Yanna ɗan Yusuf,
25 Yusuf ɗan Mattatiya, Mattatiya ɗan Amos, Amos ɗan Nahum, Nahum ɗan Hasli, Hasli ɗan Najaya,
26 Najaya ɗan Maˈata, Maˈata ɗan Mattatiya, Mattatiya ɗan Shimeya, Shimeya ɗan Yosek, Yosek ɗan Yoda.
27 Yoda ɗan Yowanan, Yowanan ɗan Resa, Resa ɗan Zerubbabel, Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ɗan Niri,
28 Niri ɗan Malki, Malki ɗan Addi, Addi ɗan Kosama, Kosama ɗan Elmadama, Elmadama ɗan Er,
29 Er ɗan Yoshuwa, Yoshuwa ɗan Eliyezer, Eliyezer ɗan Yorim, Yorim ɗan Mattat, Mattat ɗan Lawi,
30 Lawi ɗan Simeyon, Simeyon ɗan Yahuda, Yahuda ɗan Yusuf, Yusuf ɗan Yonam, Yonam ɗan Eliyakim,
31 Eliyakim ɗan Meleya, Meleya ɗan Menna, Menna ɗan Mattata, Mattata ɗan Natan, Natan ɗan Dawuda,
32 Dawuda ɗan Yesse, Yesse ɗan Obed, Obed ɗan Bowaz, Bowaz ɗan Salmon, Salmon ɗan Nashon.
33 Nashon ɗan Amminadab, Amminadab ɗan Aram, Aram ɗan Hezron, Hezron ɗan Ferez, Ferez ɗan Yahuda,
34 Yahuda ɗan Yakub, Yakub ɗan Ishaku, Ishaku ɗan Ibrahim, Ibrahim ɗan Tera, Tera ɗan Nahor,
35 Nahor ɗan Serug, Serug ɗan Reyu, Reyu ɗan Feleg, Feleg ɗan Eber, Eber ɗan Shela.
36 Shela ɗan Kenan, Kenan ɗan Arfakshad, Arfakshad ɗan Shem, Shem ɗan Nuhu, Nuhu ɗan Lamek,
37 Lamek ɗan Metusela, Metusela ɗan Enok, Enok ɗan Yared, Yared ɗan Mahalalel, Mahalalel ɗan Kenan,
38 Kenan ɗan Enosh, Enosh ɗan Set, Set ɗan Adam, Adam kuma ɗan Allah.