Skip to content

Hausa Bible

Luka 24

1 Da sassafe Ranar Farko ta mako, matan suka je kabarin da kayan ƙanshin da suka shirya.

2 Sai suka sami an riga an ture dutsen daga bakin kabarin.

3 Suka shiga ciki, amma ba su ga jikin Ubangiji Yesu ba.

4 Tun suna cikin damuwa a kan wannan, sai ga waɗansu mutum biyu tsaye kusa da su, suna sanye da fararen riguna masu haske sosai.

5 Cike da tsoro, matan suka sunkuyar da kansu a ƙasa. Mutanen suka ce musu, “Don me kuke neman mai rai cikin waɗanda suka mutu?

6 Ba ya nan, ya tashi. Ku tuna da abin da ya gaya muku tun yana Galili.

7 Ya ce, ‘Lallai ne a ba da Ɗan Mutum a hannun mutane masu zunubi, a gicciye shi, a rana ta uku kuma yă tashi.’ ”

8 Sai matan suka tuna da maganarsa.

9 Da suka dawo daga kabarin, sai suka faɗa wa sha ɗayan nan da sauran mutane dukan waɗannan abubuwa.

10 Matan da suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa kuwa su ne, Maryamu daga Magadala, da Yowana, da Maryamu mamar Yakub, da waɗansu matan da suke tare da su.

11 Amma manzannin suka ɗauki maganar matan nan wani zancen banza ne kawai, domin haka ba su gaskata ba.

12 Amma Bitrus ya tashi wuf! Ya je wurin kabarin da gudu. Ya sunkuya, ya leƙa ciki, ya ga yadin lilin a ajiye a gefe ɗaya. Sai ya koma gida yana mamakin abin da ya faru.

13 A wannan ranar kuma biyu daga cikin masu bin Yesu suna tafiya za su je wani ƙauyen da ake ce da shi Imawus, wanda nisansa daga Urushalima ya kai misali kilomita goma sha ɗaya.

14 Suna taɗi da juna a kan dukan abubuwan da suka faru.

15 Suna cikin taɗi suna tattauna ke nan, sai Yesu da kansa ya ja kusa yana tafiya da su.

16 Amma an rufe musu idanunsu, har ba su gane shi ba.

17 Sai ya ce musu, “Wane taɗi kuke yi haka da juna, kuna tafiya?” Sai suka tsaya cik, fuskokinsu a ɓace.

18 Ɗaya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai kaɗai ne baƙo a Urushalima da ba ka san abubuwan da suka faru a kwana-kwanan nan ba?”

19 Sai ya ce musu, “Waɗanne abubuwa?” Suka ce masa, “Abubuwan da suka faru da Yesu Banazaret. Shi kuwa annabi ne mai iko cikin ayyuka da magana a gaban Allah da dukan mutane,

20 wanda kuma manyan firistoci da shugabanninmu suka ba da shi a yi masa hukuncin mutuwa, suka kuwa gicciye shi.

21 Dā muna sa zuciya cewa shi ne zai fanshi Israˈila! Ga shi, yau kwana uku ke nan tun da wannan abin ya faru.

22 Ban da haka ma waɗansu mata a cikinmu sun ba mu mamaki. Gama sun je kabarin da sassafe,

23 amma ba su sami jikinsa ba. Sai suka dawo suka ce an yi musu ruˈuya, sun ga malaˈiku waɗanda suka ce yana da rai.

24 Waɗansu a cikinmu ma suka je kabarin suka kuma sami abin nan kamar dai yadda matan suka faɗa, amma shi ɗin ba su gan shi ba.”

25 Sai Yesu ya ce musu, “Haba, ku marasa tunani, ba ku da saurin gaskatawa game da abin da annabawa suka faɗa!

26 Ashe, ba dole ne Almasihu yă sha waɗannan wahaloli ba, yă kuma shiga ɗaukakarsa?”

27 Sai ya bayyana musu duk abin da Rubutacciyar Maganar Allah sun faɗa a kansa, daga Koyarwar Musa har zuwa littattafan annabawa duka.

28 Da suka yi kusa da ƙauyen da za su, sai Yesu ya yi kamar zai wuce,

29 amma suka matsa masa suka ce, “Zauna da mu, ai, yamma ta yi, ga rana duk ta fāɗi.” Sai ya bi su ya sauka a wurinsu.

30 Da suka zauna za su ci abinci, sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su.

31 Nan da nan sai idanunsu suka buɗe, suka kuma gane shi. Amma sai ya ɓace musu.

32 Suka ce wa juna, “Ashe, zuciyarmu ba ta ƙuna ba lokacin da yake magana da mu a hanya, yana bayyana mana Rubutacciyar Maganar Allah?”

33 Suka tashi nan da nan suka koma Urushalima. Suka sami sha ɗayan tare da waɗansu mutane,

34 suna cewa, “Ai, Ubangiji ya tashi da gaske! Har ma ya bayyana ga Bitrus!”

35 Saˈan nan su biyun kuma suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane shi saˈad da yake kakkarya burodi.

36 Tun suna magana game da wannan, sai kawai ga Yesu da kansa a tsaye a tsakiyarsu, ya ce musu, “Salama a gare ku!”

37 Tsoro ya kama su suna rawar jiki, suna tsammani fatalwa ce suke gani.

38 Sai ya ce musu, “Don me kuka ji tsoro haka, kuke kuma shakka a zuciyarku?

39 Ku duba hannuwana da ƙafafuna ku gani, ai, ni ne da kaina. Ku taɓa ni, ku ji, don fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.”

40 Da ya faɗa haka, sai ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa.

41 Tun suna da sauran shakka saboda yawan farin ciki da mamaki, sai ya ce musu, “Kuna da abinci a nan kuwa?”

42 Suka ba shi tsokar gasasshen kifi.

43 Ya karɓa ya ci, su kuma suna kallonsa.

44 Sai ya ce musu, “Waɗannan su ne abubuwan da na yi magana a kai tun ina tare da ku, cewa dole ne a cika duk abin da aka rubuta a kaina a cikin Koyarwar Musa, da littattafan annabawa, da kuma Zabura.”

45 Sai ya buɗe hankalinsu suka gane da Rubutacciyar Maganar Allah,

46 ya kuma ce musu, “Haka aka rubuta cewa dole ne Almasihu yă sha wuya, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu.

47 Kuma a sunansa za a yi wa dukan alˈumman duniya waˈazin tuba da yafewar zunubai. Za a kuwa fara daga Urushalima.

48 Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.

49 Ga shi, ni zan aiko muku da abin da Ubana ya yi alkawari. Amma ku jira a birni tukuna, sai an ba ku iko daga sama.”

50 Sai ya fitar da su zuwa bayan birni, suka kai har Betani. A wurin ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka.

51 Yana cikin sa musu albarka ke nan, sai ya rabu da su, aka kuma ɗauke shi zuwa sama.

52 Su kuwa suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da farin ciki sosai.

53 Ko yaushe kuma suna cikin Haikali suna yabon Allah.

Open Bible reader