Skip to content

Hausa Bible

Luka 20

1 Wata rana Yesu ya shiga Haikali yana koyarwa, yana kuma waˈazin labari mai daɗi ga mutane, sai manyan firistoci da malaman Koyarwar Musa tare da shugabannin jamaˈa suka zo

2 suka ce masa, “Gaya mana iznin da kake da shi da kake yin waɗannan abubuwa. Wa ya ba ka iznin?”

3 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku gaya mini,

4 iznin da Yohanna ya yi baftisma da shi, Allah ne ya ba shi, ko kuwa mutum?”

5 Sai suka tattauna a junansu, suna cewa, “Idan mun ce, ‘Daga wurin Allah ya zo,’ zai ce, ‘Don me ba ku gaskata shi ba?’

6 In kuma muka ce, ‘Daga mutum ne,’ yawan mutanen nan za su jejjefe mu da duwatsu, domin kowa ya yarda cewa Yohanna annabi ne.”

7 Domin haka suka ce masa, “Ba mu san inda ya fito ba.”

8 Sai Yesu ya ce musu, “Ni ma ba zan faɗa muku ko da wane izni nake yin waɗannan abubuwa ba.”

9 Sai Yesu ya gaya wa mutane wannan misali, ya ce, “An taɓa yin wani mutumin da ya yi gonar inabi, sai ya ba da hayarta ga waɗansu manoma, saˈan nan ya tafi wata ƙasa, ya kuma daɗe a can.

10 Da lokacin girbin inabin ya yi, sai ya aiki wani bawansa yă je wurin waɗannan da suka karɓi hayar gonar, yă karɓo masa waɗansu ˈyaˈyan inabi daga gonar. Amma ˈyan hayar suka yi masa dūka, suka sallame shi hannu wofi.

11 Sai mutumin nan ya sāke aiki wani bawa, amma waɗannan ˈyan hayar suka yi masa dūka shi ma, suka kuma wulaƙanta shi suka sallame shi hannu wofi.

12 Har wa yau mutumin ya aiki wani bawa na uku, shi kuma suka yi masa ciwo, suka jefa shi waje.

13 Saˈan nan, mutumin nan mai gonar inabin ya ce, ‘Yanzu me zan yi? Zan aiki ɗana wanda nake ƙauna, na san lallai za su ba shi girma!’

14 Amma da ˈyan hayar suka gan shi, suka ce wa juna, ‘Aha! Ga wanda zai ci gādon gonar, bari mu kashe shi, don gādonsa yă zama namu!’

15 Sai suka wurga shi a bayan katanga, suka kashe shi. “To, me kuke tsammani mai gonar nan zai yi da ˈyan hayar nan?

16 Zai zo ya halaka ˈyan hayar nan, ya ba waɗansu hayar gonar.” Da mutane suka ji haka suka ce, “Allah yă sawwaƙe!”

17 Amma Yesu ya dube su ya ce, “Mene ne nufin wannan aya a cikin Rubutacciyar Maganar Allah? “ ‘Dutsen da masu gini suka ƙi, shi ne ya zama dutse mafi amfani a gini!’ ”

18 “Duk wanda ya fāɗi a kan wannan dutsen, zai halaka, kuma idan dutsen nan ya fāɗi a kan wani, zai niƙa shi yă zama kamar gari.”

19 A nan ne malaman Koyarwar Musa da manyan firistoci suka so su kama Yesu, domin sun gane cewa ya yi wannan misali a kansu ne, amma sun ji tsoron mutane.

20 Sai suka nemi hanya, suka biya waɗansu mutane su yi kamar su masu kirki ne. Suka aike su ne su sa wa Yesu tarko da irin tambayoyin da za su yi masa, da nufi su ba da shi ga iko da kuma hukuncin mai mulki.

21 Waɗanda aka aika kuwa suka tambayi Yesu, suka ce, “Malam, mun sani cewa maganarka da koyarwarka gaskiya ne, mun kuma sani ba ka nuna bambanci, kuma kana koyar da hanyar Allah cikin gaskiya.

22 To, kana gani daidai ne mu biya wa Kaisar haraji, ko aˈa?”

23 Amma Yesu ya gane wayonsu, sai ya ce musu,

24 “Nuna mini dinari. Hoton wa da sunan wane ne a kansa?” Suka amsa, “Na Kaisar ne.”

25 Sai ya ce, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”

26 A nan kuma suka kāsa kama shi da magana a gaban mutane. Sai suka yi shiru suna mamakin wannan amsar da ya ba su.

27 Sai ga waɗansu Sadukiyawa, waɗanda suke cewa wai babu tashin matattu, sun zo wurin Yesu, suka ce,

28 “Malam, Musa ya rubuta mana wannan umarni cewa, ‘Idan mutum ya mutu ya bar matarsa ba ˈyaˈya, ya kamata ɗanˈuwansa yă aure ta domin yă samo masa ˈyaˈya.’

29 To, an taɓa yin waɗansu mutane su bakwai, duk ˈyanˈuwan juna. Babban ya yi aure ya mutu ba yaro.

30 Na biyun ya auri matar, ya mutu ba yaro.

31 Na ukun ma haka. Sai ya zama dukansu bakwai ɗin sun auri macen nan, amma sai suka mutu babu ˈyaˈya.

32 A ƙarshe kuma, ita macen ta mutu.

33 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama? Gama duk bakwai ɗin sun aure ta.”

34 Yesu ya ce musu, “A zamanin nan maza suna aure, ana kuma ba da mata ga aure.

35 Amma waɗanda za su cancanci tashi daga matattu su kuma zauna a zamani mai zuwa ba za su yi aure ba, ba za a kuma aurar da su ba.

36 Gama ba ya yiwuwa su sāke mutuwa saboda za su zama kamar malaˈiku. Za su kuwa zama ˈyaˈyan Allah ke nan saboda sun tashi daga matattu.

37 Ai, Musa ya kuma nuna a fili cewa waɗanda suka mutu za su tashi. A labarin ƙaramin itacen da ya ci wuta, ya yi magana a kan Ubangiji cewa, ‘Shi ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yakub’.

38 Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai. Wannan ya nuna cewa a gare shi kowa mai rai ne.”

39 Sai waɗansu malaman Koyarwar Musa suka yi magana suka ce, “Malam ka faɗa daidai!”

40 Daga nan kuma ba su yi ƙarfin hali su ƙara tambayarsa wani abu ba.

41 Yesu ya tambaye su ya ce, “Yaya za a ce Almasihu ɗan Dawuda ne?

42 Dawuda da kansa ya ce a Littafin Zabura, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana,

43 sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin ƙafafunka.” ’ ”

44 “Dawuda ya ce da Almasihu ‘Ubangiji.’ To, yaya kuma za a ce da shi ɗan Dawuda?”

45 Yesu ya gaya wa almajiransa a gaban mutane cewa,

46 “Ku yi hankali da malaman Koyarwar Musa, su masu son sa manyan riguna suna yawo, masu so a gaishe su a kasuwa, masu so a ba su wuraren zama masu daraja a majamiˈu, da wuraren zama masu kyau a wurin biki.

47 Su ne masu cin kayan matan da mazansu suka mutu, saˈan nan su yi doguwar adduˈa don a gan su. Ai, su za su sha hukunci mafi tsanani.”

Open Bible reader