Skip to content

Hausa Bible

Luka 18

1 Sai Yesu ya ba almajiransa wani misali domin yă koya musu cewa ya kamata su dinga yin adduˈa kullum, kada su gaji.

2 Ya ce, “An taɓa yin wani alƙali a wani gari wanda ba ya tsoron Allah, ba ya kuma kula da mutane.

3 A nan garin kuma akwai wata macen da mijinta ya mutu wadda ta dinga zuwa wurin alƙalin tana roƙonsa cewa, ‘Ka ba ni hakkina cikin ƙarar da aka kawo a kaina.’

4 Da farko, ya ƙi, amma daga baya ya ce a ransa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane,

5 amma saboda macen nan ta dame ni, zan yi ƙoƙari in ga cewa ta sami abin da ta roƙa, domin kada yawan zuwanta yă kawo mini gajiya!’ ”

6 Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan marar gaskiya ya ce!

7 Ashe, Allah ba zai biya wa mutanen da ya zaɓa waɗanda suke masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi sanyin jiki wajen taimakonsu ne?

8 Ina dai gaya muku, zai biya musu hakkinsu, da sauri-sauri kuwa. Amma saˈad da Ɗan Mutum ya dawo, zai sami mai bangaskiya a duniyar nan kuwa?”

9 Yesu ya kuma faɗa wannan misali ga mutanen da suka ɗauka kansu masu adalci ne har suna rena sauran mutane.

10 Ya ce, “An taɓa yin mutum biyu waɗanda suka shiga Haikali domin su yi adduˈa. Ɗaya a cikinsu Bafarisiye ne, ɗayan kuma mai karɓar haraji.

11 “Sai Bafarisiyen ya tashi ya tsaya, ya fara adduˈa yana cewa, ‘Allah, na gode maka saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, masu sata, masu cuta, masu zina. Ni ba kamar mai karɓar harajin nan ba ne.

12 Ina azumi sau biyu a mako, ina kuma ba da zakka ta kowane abin da na samu.’

13 “Amma mai karɓar harajin nan ya tsaya da nisa, bai ko ɗaga idonsa sama ba. Saboda baƙin cikinsa ya sunkuyar da kansa, yana cewa, ‘Allah, ka ji tausayina, ni mai zunubi ne!’ ”

14 Yesu ya ce, “Ina gaya muku, mai karɓar harajin nan ya koma gidansa da samun zaman marar laifi a gaban Allah, ba kamar Bafarisiyen ba. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Amma duk wanda ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”

15 Waɗansu suka kawo ˈyan yaransu domin Yesu ya sa musu hannun albarka. Da almajiransa suka ga haka, sai suka fara tsawata musu.

16 Amma Yesu ya kirawo ˈyan yaran, ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su. Gama, mulkin Allah na irinsu ne.

17 Hakika ina gaya muku duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai taɓa shiga cikinsa ba.”

18 Wani shugaban Yahudawa ya tambayi Yesu ya ce, “Malam, mai kirki, me zan yi in sami rai na har abada?”

19 Yesu ya tambaye shi, ya ce, “Don me kake ce da ni mai kirki? Ai, ba wani mai kirki sai Allah kaɗai.

20 Ka dai san abin da dokoki suka ce, ‘Kada ka yi zina. Kada ka yi kisan kai. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar ƙarya. Ka ba da girma ga babanka da mamarka.’ ”

21 Mutumin ya ce, “Ai, duk na kiyaye waɗannan tun ina yaro.”

22 Da jin haka, sai Yesu ya ce masa, “Akwai abu ɗaya tak wanda ya rage maka ka yi. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka raba wa talakawa, za ka sami dukiya a sama. Saˈan nan ka zo ka bi ni.”

23 Da jin wannan magana, sai mutumin ya ɓata rai, don shi mai arziki ne sosai.

24 Da Yesu ya ga ya ɓata rai, sai ya ce, “Zai zama da wuya sosai masu arziki su shiga mulkin Allah!

25 Gama zai fi wa raƙumi sauƙi yă bi ta ramin allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”

26 Mutanen da suka ji wannan magana suka tambaye shi, suka ce, “To, in haka ne, wa zai iya samun ceto?”

27 Yesu ya ce, “Abin da ya fi ƙarfin mutum, bai fi ƙarfin Allah ba.”

28 Sai Bitrus ya ce, “To, ga shi mun bar gidajenmu mun bi ka.”

29 Yesu ya amsa ya ce, “Na san da haka, kuma hakika ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko mata, ko ˈyanˈuwa, ko iyaye, ko ˈyaˈya saboda mulkin Allah

30 da zai kāsa samun abubuwa da yawa a yanzu, a can zamani mai zuwa kuma yă sami rai marar ƙārewa.”

31 Sai Yesu ya kai sha biyun nan gefe ɗaya, ya ce musu, “Ga shi, za mu haura zuwa Urushalima, inda dukan abin da annabawa suka rubuta a kan Ɗan Mutum zai cika.

32 Za a ba da shi ga waɗanda ba Yahudawa ba, a yi masa baˈa, a wulaƙanta shi, a kuma tofa masa miyau.

33 Za su yi masa bulala, su kuma kashe shi, amma a rana ta uku zai tashi.”

34 Amma almajiran ba su gane da maganar nan da Yesu ya yi ba. An ɓoye musu maˈanar maganar nan, shi ya sa ba su gane abin da yake faɗa ba.

35 Da Yesu ya yi kusa da Yeriko, sai ga wani makaho yana zaune a gefen hanya yana bara.

36 Da ya ji mutane da yawa suna wucewa, sai ya yi tambaya ko mene ne yake faruwa.

37 Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazaret ne yake wucewa.”

38 Sai ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Yesu! Ɗan Dawuda! Ka ji tausayina!”

39 Mutanen da suke gaba suka tsawata masa yă yi shiru. Amma sai ya ƙara ɗaga murya da ƙarfi sosai, yana cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

40 Sai Yesu ya tsaya, ya ce a kawo shi wurinsa. Da ya zo kusa, Yesu ya tambaye shi,

41 “Me kake so in yi maka?” Sai makahon ya amsa ya ce, “Maigirma, ina so in sami ganin gari.”

42 Yesu ya ce masa, “To, ka sami ganin gari! Bangaskiyarka ce ta warkar da kai.”

43 Nan da nan sai ya sami ganin gari, ya bi Yesu, yana ɗaukaka Allah. Da mutane suka ga wannan, sai duka suka yabi Allah.

Open Bible reader