Hausa Bible
Luka 13
1 A daidai wannan lokaci, waɗansu mutanen da suke a wurin suka gaya wa Yesu labarin Galilawan da Bilatus ya sa aka kashe lokacin da suke miƙa wa Allah hadayarsu.
2 Yesu ya amsa musu ya ce, “Don an kashe Galilawan nan haka, kuna tsammani sun fi kowa zunubi ke nan a Galili?
3 Sam! Ina gaya muku, idan ba ku tuba a kan laifofinku ba, dukanku za ku halaka kamarsu.
4 Ko kuwa mutane sha takwas ɗin nan da gini ya fāɗi a kansu a Siluwam, ya kashe su, kuna tsammani sun fi duk sauran mutanen Urushalima zunubi ne?
5 Sam! Ina gaya muku, in ba ku tuba ba, za ku halaka kamarsu.”
6 Sai Yesu ya ba su misali ya ce, “An taɓa yin wani mutum wanda yake da itacen ɓaure a gonar inabinsa. Sai ya zo domin yă tsinka ˈyaˈyan, amma bai sami ko ɗaya ba.
7 Sai ya ce wa mutumin da yake lura da gonar, ‘Duba, yau shekara uku ke nan ina zuwa neman ˈyaˈyan ɓauren nan, amma kullum ba na samun kome a kansa. Sare shi! Don me za a bar shi yă tare wuri a banza?’
8 “Amma mai lura da gonar ya amsa ya ce, ‘Maigirma, a bar shi dai, in bar shi shekara ɗaya, in kuma zuba masa taki a wannan shekara.
9 Idan ya yi ˈyaˈya nan gaba, to, in kuma bai yi ba, sai a sare shi.’ ”
10 Wata rana Yesu yana koyarwa a wata majamiˈa a Ranar Hutu ta Mako,
11 sai ga wata mace wadda aljani ya sa ciwo ya shanye ta na tsawon shekaru goma sha takwas. Duk ta tanƙware, ba ta ma iya miƙewa.
12 Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce, “Uwargida, an warkar da ke daga rashin lafiyarki.”
13 Sai ya sa hannunsa a kanta, nan da nan sai ta miƙe tsab, ta yabi Allah.
14 Amma shugaban majamiˈar ya ji haushi yadda Yesu ya warkar da ita a Ranar Hutu. Sai ya ce wa mutanen da suke nan, “Akwai ranaku har shida da ya kamata a yi aiki, ku zo a ranakun nan a warkar da ku, ba Ranar Hutun ba.”
15 Amma Ubangiji ya ce masa, “Munafukai kawai! Ashe, kowannenku ba ya kunce saniyarsa ko jakinsa, yă kai shi wurin da zai sha ruwa a Ranar Hutu?
16 Macen nan, ˈyar dangin Ibrahim wadda Shaiɗan ya ɗaure, yau shekara goma sha takwas, ashe, bai yi daidai a warkar da ita a Ranar Hutu ta Mako ba?”
17 Wannan maganarsa da ya yi, ta sa duk masu ƙin ganinsa suka ji kunya. Sauran mutane kuwa, duk suka yi ta murna saboda ayyukan ban mamakin da yake yi.
18 Sai Yesu ya ce, “Yaya mulkin Allah yake? Da me kuma zan kwatanta shi?
19 Mulkin sama kamar ƙwayar mastad yake wadda ta fi ƙanƙanta cikin iri duka, wadda wani mutum ya ɗauka ya shuka a gonarsa. Sai ta yi girma har ta zama itace, tsuntsaye kuwa suka yi gida a rassansa.”
20 Yesu ya sāke tambaya, “Da me zan kwatanta mulkin Allah?
21 Kamar yisti yake wanda wata mace ta kwaɓa da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya game da yistin.”
22 Da Yesu ya kama hanya zai tafi Urushalima, sai ya bi garuruwa da ƙauyuka yana koya wa mutane.
23 Sai wani ya tambaye shi ya ce, “Malam, shin, wai mutane kaɗan ne kawai za su sami ceto?” Yesu ya ce musu,
24 “Ku yi ƙoƙari ku shiga ta ƙaramar ƙofa, domin mutane da yawa za su yi ƙoƙarin shiga amma ba za su iya ba.
25 In dai maigidan ya riga ya tashi ya rufe ƙofar gidan, ku kuwa za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasa ƙofar, kuna cewa, ‘Maigida, a buɗe mana ƙofa!’ Shi kuma zai amsa muku yă ce, ‘Ban san inda kuka fito ba!’
26 “Saˈan nan za ku fara kuka kuna cewa, ‘Haba, mu da muka ci, muka sha tare da kai, har ka koyar a garuruwanmu.’
27 Amma zai ce, ‘Ban san inda kuka fito ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’
28 Saˈad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakub, da dukan annabawa a mulkin Allah, ku kuwa ana korarku, a nan ne za ku yi kuka da cizon haƙora.
29 Mutane za su zo daga gabas da yamma, kudu da arewa, su zauna cin biki a mulkin Allah.
30 Ga shi fa waɗanda suke na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na ƙarshe.”
31 A wannan lokaci sai waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce wa Yesu, “Ka tashi daga nan fa, domin Hirudus yana so yă kashe ka.”
32 Sai ya ce musu, “Ku je ku gaya wa mai makircin nan cewa, ‘Yau ina fitar da aljanu, ina kuma warkar da mutane, gobe ma haka, jibi ne zan gama aikina.
33 Duk da haka lallai ne in ci gaba da tafiyata yau da gobe, da kuma jibi, don kuwa bai yi kyau a ce annabi ya mutu ba, in ba a Urushalima ne aka kashe shi ba.’
34 “Ayya, Urushalima! Urushalima! Mai kisan annabawa, mai jifar waɗanda aka aiko gare ta! Sau nawa na so in tattara ku kamar yadda kaza take tattara ˈyan yaranta cikin fikafikanta, amma kun ƙi!
35 Ga shi an bar muku gidanku kufai! Ina kuwa gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ranar da kuka ce, ‘Mai albarka ne, wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!’ ”