Hausa Bible
Yahaya 3
1 Akwai wani mutum mai suna Nikodimus, wanda yake a ƙungiyar Farisiyawa, wani shugaban Yahudawa.
2 Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dare, ya ce masa, “Malam, mun san cewa kai malami ne wanda Allah ya aiko, domin babu wanda zai iya yin waɗannan alamun ban mamaki sai dai wanda Allah yana tare da shi.”
3 Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Hakika, ina gaya maka, babu wanda zai iya ganin mulkin Allah, sai dai an sāke haife shi.”
4 Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Ta yaya za a haifi mutum bayan da ya tsufa? Zai sāke koma cikin mamarsa ne a sāke haifuwarsa sau na biyu?”
5 Yesu ya amsa masa ya ce, “Hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta ruwa da Ruhu ba, ba zai iya shiga mulkin Allah ba.
6 Abin da mutum ya haifa mutum ne, amma abin da Ruhu ya haifa Ruhu ne.
7 Kada fa ka yi mamaki domin na ce maka, ‘Dole a sāke haifarku’.
8 Iska tana busawa inda ta ga dama. Kakan ji motsinta, amma ba ka san wurin da take fitowa ba, ba ka kuma san inda za ta ba. Haka yake daidai da dukan mutumin da Ruhu ya haifa.”
9 Sai Nikodimus ya tambayi Yesu ya ce, “Ta yaya wannan zai yiwu?”
10 Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai babban malami ne a Israˈila, amma duk da haka ba ka gane waɗannan abubuwa ba?
11 Hakika, ina gaya maka, muna maganar abin da muka sani ne, muna kuma shaida muku abin da muka gani, amma duk da haka kun ƙi karɓar abin da muka gaya muku.
12 Ina yi muku magana game da abubuwan da suke a nan duniya, amma ba ku ba da gaskiya ba, yaya za ku ba da gaskiya idan na gaya muku abubuwan da suke na sama?
13 Ba wanda ya taɓa hawa zuwa cikin sama sai dai shi Ɗan Mutum kaɗai da ya sauko daga can.
14 “Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji na tagulla a daji, haka kuma dole ne a ɗaga Ɗan mutum,
15 domin duk wanda ya ba da gaskiya gare shi, zai sami rai na har abada.
16 “Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi kada yă halaka, amma yă sami rai na har abada.
17 Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă hukunta duniya ba, amma domin duniya ta sami ceto ta wurinsa.
18 “Duk wanda ya ba da gaskiya ga Ɗan Allah, ba za a hukunta shi ba. Amma duk wanda bai ba da gaskiya gare shi ba, an riga an hukunta shi ke nan domin bai ba da gaskiya ga sunan makaɗaicin Ɗan Allah ba.
19 Ga yadda hukuncin yake, haske ya shigo duniya, amma mutane suka fi ƙaunar duhu fiye da hasken, gama ayyukansu mugaye ne.
20 Duk wanda yake aikata rashin gaskiya yakan ƙi hasken, ba zai ma zo wurin hasken ba, domin kada ayyukansa su tonu.
21 Amma mai aikata gaskiya kuwa yakan zo wajen hasken, domin a gani a fili cewa abin da yake yi yana yi ne da taimakon Allah.”
22 Bayan haka Yesu da almajiransa suka tafi yankin Yahudiya. A nan ya jima da su, yana yi wa mutane baftisma.
23 Yohanna kuma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salim, domin akwai ruwa mai yawa a can. Mutane suka yi ta zuwa ana yi musu baftisma.
24 Wannan ya faru ne kafin a kulle Yohanna cikin kurkuku.
25 Sai almajiran Yohanna suka shiga gardama da wani Bayahude a kan alˈadar wanke-wanke domin tsabtacewa bisa ga doka.
26 Sai almajiran suka je wurin Yohanna suka ce masa, “Malam, mutumin da kuke tare da shi a dā a ƙetaren Kogin Yodan, wanda kai da kanka ma ka ba da shaida a kansa, ga shi can yana yin baftisma, har kowa da kowa yana zuwa wurinsa.”
27 Sai Yohanna ya amsa ya ce, “Ba mai iya samun kome sai ko an ba shi daga sama.
28 Ku da kanku ma shaiduna ne domin na ce, ‘Ba ni ne Almasihun ba, amma an aike ni ne in riga shi zuwa.’
29 A bikin aure, ango ne mai amarya. Abokin ango wanda ya je auren kuwa yakan jira ne kurum yă ji muryar ango. Yakan kuma cika da farin ciki idan ya ji ango ya yi magana. A ta haka ne farin ciki nawa ya cika.
30 Dole ne mutumin nan yă yi ta ƙaruwa, ni kuma in yi ta raguwa.
31 “Shi wanda ya zo daga sama ya fi kowa. Dukan wanda ya fito daga duniya kuwa na duniya ne, kuma yakan yi maganar abubuwan duniya ne. Wanda kuma ya zo daga sama ya fi kowa duka.
32 Yana shaidar abin da ya ji ya kuma gani ne, duk da haka ba wanda ya yarda da shaidarsa.
33 Amma duk wanda ya yarda da alamar shaidarsa, ya tabbatar ke nan cewa, lallai Allah mai gaskiya ne.
34 Gama shi wanda Allah ya aiko, kalmar Allah ne yake faɗi, domin Allah ya ba shi Ruhunsa babu iyaka.
35 Uban yana ƙaunar Ɗan, ya kuma sa kome a hannunsa.
36 Dukan wanda yake ba da gaskiya ga Ɗan, yana da rai na har abada. Amma duk wanda ya ƙi Ɗan, ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah yă kasance a kansa.”