Hausa Bible
Yahaya 11
1 Akwai wani mutum mai suna Liˈazaru wanda ya yi rashin lafiya a ƙauyen Betani. Betani kuwa ƙauyen su Maryamu ne da ˈyarˈuwarta Marta.
2 Liˈazaru wanda ba shi da lafiya ɗanˈuwan Maryamu ne. Ita ce ta shafa wa Ubangiji man ƙanshi ta kuma share ƙafafunsa da gashinta.
3 To, ˈyanˈuwan nan mata suka aika wa Yesu, suka ce, “Ubangiji, ga shi, wanda kake ƙaunar nan ba shi da lafiya.”
4 Da Yesu ya ji haka sai ya ce, “Wannan rashin lafiya ba zai kai shi mutuwa ba, amma zai kawo ɗaukaka ne ga Allah a kuma girmama Ɗansa.”
5 Yesu kuwa ya ƙaunaci Marta da ˈyarˈuwarta, da kuma Liˈazaru.
6 Amma duk da haka da ya sami labari cewa Liˈazaru ba shi da lafiya, ya ƙara zama kwana biyu a wurin da yake.
7 Bayan haka ya ce wa almajiran, “Mu koma Yahudiya.”
8 Almajiran suka ce masa, “Malam, kwana-kwanan nan fa Yahudawa suka nema su jejjefe ka, kuma za ka sāke komawa can?”
9 Yesu ya amsa ya ce, “Ba awa goma sha biyu ne yini guda ba? To, duk wanda yake tafiya da rana ba ya tuntuɓe, don yana ganin hasken duniyar nan.
10 Amma duk wanda yake tafiya da dare yakan yi tuntuɓe don babu haske a wurinsa!”
11 Bayan da Yesu ya faɗa waɗannan abubuwa, ya ƙara ce musu, “Abokinmu Liˈazaru ya yi barci, amma za ni in tashe shi daga barcin.”
12 Sai almajiran suka ce masa, “Ubangiji, in dai barci ya ɗauke shi, ai, zai warke.”
13 Yesu yana nufin Liˈazaru ya mutu ne, amma su almajiransa suna tsammani yana barcin hutawa ne.
14 Sai Yesu ya gaya musu a fili ya ce, “Liˈazaru ya mutu.
15 Saboda ku ne ina farin ciki yadda ba na wurin, domin ku ba da gaskiya. Amma mu dai tafi wurinsa.”
16 Sai Toma, wanda ake ce da shi ˈYan Biyu, ya ce wa ˈyanˈuwansa almajirai, “Mu ma mu tafi, mu mutu tare da shi.”
17 Da Yesu ya kai wurin, ya ji cewa, Liˈazaru ya mutu har an yi kwana huɗu da binne shi a kabari.
18 Betani kuwa kusa da Urushalima yake, bai kai kilomita uku ba.
19 Yahudawa da yawa suka zo su yi wa Marta da Maryamu taˈaziyyar ɗanˈuwansu.
20 Da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta tafi domin ta marabce shi. Maryamu kuwa ta zauna a gida.
21 Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, ai, da kana nan da ɗanˈuwana bai mutu ba.
22 Ko yanzu ma na sani Allah zai ba ka duk abin da ka roƙe shi.”
23 Yesu ya ce mata, “Ɗanˈuwanki zai tashi.”
24 Marta ta ce masa, “Na sani zai rayu kuma a tashin matattu a ranar ƙarshe.”
25 Sai Yesu ya ce mata, “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda yake ba da gaskiya gare ni, ko ya mutu zai rayu.
26 Wanda yake a raye, yake kuwa gaskata da ni, ba zai mutu ba har abada. Kin gaskata da wannan?”
27 Sai Marta ta amsa ta ce, “I, ya Ubangiji, na ba da gaskiya cewa kai ne Almasihun nan, Ɗan Allah wanda yake zuwa duniya.”
28 Da ta faɗa haka, sai ta je ta kirawo ˈyarˈuwarta Maryamu, ta ce, “Malam ya zo, kuma yana kiranki.”
29 Da jin haka, Maryamu ta yi maza-maza ta tashi ta tafi wurin Yesu.
30 To, Yesu dai bai riga ya shiga cikin ƙauyen ba tukuna. Har yanzu yana wurin da Marta ta marabce shi.
31 Da Yahudawan da suke tare da Maryamu a cikin gida suna mata taˈaziyya suka ga ta tashi da sauri ta fita, sai suka bi ta suna tsammani za ta kabarin ne, ta yi kuka a can.
32 Da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta gan shi, sai ta fāɗi a gabansa, ta ce masa, “Ubangiji, ai, da kana nan da ɗanˈuwana bai mutu ba.”
33 Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita su ma suna kuka, sai abin ya dami Yesu a zuciya sosai.
34 Sai ya ce, “Ina ne kuka binne shi?” Suka ce masa, “Ubangiji, zo ka gani.”
35 Sai Yesu ya yi hawaye.
36 Saboda haka Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”
37 Amma waɗansu daga cikinsu suka ce wa junansu, “Ya buɗe idanun makahon can. To, me ya sa bai yi wani abu wanda zai hana wannan mutum mutuwa ba?”
38 Da Yesu ya sāke damuwa a ransa sosai, ya tafi kabarin. Kabarin kuwa kogon dutse ne, da wani dutse kuma aka rufe bakin.
39 Sai Yesu ya ce, “Ku ture dutsen.” Amma Marta ˈyarˈuwar mutumin da ya mutu ta ce wa Yesu, “Ubangiji, ai, yanzu zai yi wari, don yau kwanansa huɗu ke nan da mutuwa.”
40 Sai Yesu ya ce mata, “Bāna riga na gaya miki cewa idan kin ba da gaskiya za ki ga ɗaukakar Allah ba?”
41 Sai suka ture dutsen. Yesu kuwa ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, na gode maka da ka saurare ni.
42 Ko dā ma na sani kullum kana saurare ni, amma na faɗa haka ne domin mutanen da suke tsaye a nan su ba da gaskiya kai ne ka aiko ni.”
43 Da ya faɗa haka sai ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Liˈazaru, fito!”
44 Sai mutumin da ya mutu ɗin ya fito, ƙafa da hannu a ɗaure da guntayen yadi, fuskarsa kuma a naɗe take da zanen da aka binne shi da shi. Sai Yesu ya ce musu, “Ku kunce shi, yă tafi.”
45 Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo ziyarar Maryamu suka ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi.
46 Amma waɗansunsu suka tafi wurin Farisiyawa, suka gaya musu abin da Yesu ya yi.
47 Domin haka manyan firistoci da Farisiyawa suka tara ˈyan majalisa. Suka tambayi juna suka ce, “Me muke yi ne? Ga wannan mutumin yana yin alamun ban mamaki da yawa!
48 In fa muka ƙyale shi yana yin abubuwan nan, dukan mutane za su ba da gaskiya gare shi. Saˈan nan Romawa kuma za su zo su ƙwace ƙasarmu da kuma Haikalinmu!”
49 Amma ɗayansu mai suna Kayafa wanda ya kasance babban firist a wannan shekara, ya ce musu, “Ku dai ba ku san kome ba sam!
50 Ba ku lura ba, ai, ya fi sauƙi mutum ɗaya yă mutu saboda mutane, da a ce dukan alˈummar ta halaka.”
51 Wannan maganar da Kayafa ya yi ba tunanin kansa ba ne, amma da yake shi ne babban firist a wannan shekara, ya yi annabci cewa Yesu zai mutu saboda alˈummar Yahudawa,
52 ba ma saboda Yahudawa kaɗai ba, amma domin yă tattaro ˈyaˈyan Allah waɗanda suka bazu koˈina su zama ɗaya.
53 Tun daga wannan rana suka yi shawara yadda za su kashe Yesu.
54 Saboda haka Yesu bai ƙara tafiya cikin Yahudawa a fili ba, amma ya bar wurin, ya tafi ƙasar da take kusa da daji, ya shiga wani gari mai suna Ifrayim. A nan ne ya zauna da almajiransa.
55 Da Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, mutane da yawa daga ƙauye suka haura zuwa Urushalima domin su tsabtace kansu bisa ga alˈadarsu kafin bikin.
56 Suka yi ta neman Yesu, suna tsaitsaye a Haikali suna tambayar juna, suna cewa, “Me kuka gani? Zai zo bikin kuwa?”
57 Domin dā ma manyan firistoci da Farisiyawa sun riga sun ba da doka cewa, duk wanda ya san inda Yesu yake, yă zo yă faɗa domin su kama shi.