Skip to content

Hausa Bible

Yahaya 10

1 “Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai shiga wurin da ake ajiye tumaki ta ƙofa ba, amma ya haura ya shiga ciki ta wani gefe, to, shi ɓarawo ne, ɗan fashi ne kuma.

2 Wanda ya shiga ta ƙofar kuwa, shi ne makiyayin tumakin.

3 Maigadin ƙofar yakan buɗe masa. Tumakin kuma sukan saurari muryar makiyayin. Yakan kira tumakinsa da sunayensu yă bi da su yă kai su waje.

4 Bayan da ya fitar da dukan nasa waje, sai yă yi tafiya a gaba, tumakin kuma suna binsa a baya domin sun san muryarsa.

5 Ba za su bi baƙo ba, sai dai su guje shi, don ba su san muryar baƙo ba.”

6 Yesu ya faɗa wa mutanen wannan misali, amma ba su gane abin da yake faɗa musu ba.

7 Domin haka Yesu ya sāke ce musu, “Hakika, ina gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.

8 Duk waɗanda suka zo kafin ni ɓarayi ne da ˈyan fashi, kuma tumakin ma ba su ji su ba.

9 Ni ne ƙofar, wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto, zai shiga yă kuma fita yana kiwo.

10 Ɓarawo yakan zo ne kawai don sata, da kisa, da kuma halakarwa. Amma na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi cikakke.

11 “Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau kuwa shi ne yakan ba da ransa domin tumakin.

12 Ɗan hayar da aka yi hayarsa don kiwo, shi ba makiyayi ba ne, tumakin kuma ba nasa ba ne. Saboda haka da ganin kyarkeci yana zuwa da gudu, sai yă bar tumakin yă gudu. Kyarkeci kuwa yă kama tumakin yă kuma warwatsar da sauran.

13 Mutumin ya gudu ne domin aikin kuɗi ne kawai yake yi, kuma ba abin da ya dame shi da tumakin.

14 “Ni ne makiyayi mai kyau. Na san nawa, nawa kuma sun san ni,

15 kamar yadda dai na san Uba, Uban kuma ya san ni. Ina kuma ba da raina domin tumakin.

16 Ina da waɗansu tumaki kuma waɗanda ba na wannan garke ba ne. Su ma dole ne in kawo su. Za su kuwa saurari muryata, za su zama garke ɗaya, makiyayi ɗaya kuma.

17 Abin da ya sa Uba yana ƙaunata ke nan, saboda ina ba da raina domin in sāke ɗauko shi kuma.

18 Ba mai ƙwace mini rai, domin ni da kaina nake ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Abin da Ubana ya umarce ni in yi ke nan.”

19 Saboda wannan maganar da Yesu ya yi, sai Yahudawa suka shiga muhawara da juna kuma.

20 Da yawa daga cikinsu, suka ce, “Ai, yana da aljani ne, shi ya sa yake hauka. Don me za ku saurare shi?”

21 Amma waɗansu kuwa suka ce, “Aˈa, ai, wannan magana ba ta mai aljani ba ce. Ashe, aljani zai iya buɗe wa makaho ido?”

22 Lokacin sanyi ne ana kuma bikin Miƙawar Haikali a Urushalima.

23 Yesu kuwa yana zagaya a Zauren Solomon a cikin Haikali,

24 sai Yahudawa suka kewaye shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu cikin shakka? In dai kai ne Almasihun ka gaya mana a fili.”

25 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, na riga na gaya muku ba ku ba da gaskiya ba. Ayyukan da nake yi a cikin sunan Ubana su ne suke nuna kowane ne ni.

26 Amma ba ku ba da gaskiya ba, domin ku ba tumakina ba ne.

27 Gama tumakina sukan yi biyayya da abin da nake faɗa, na san su, suna bina kuma.

28 Ina ba su rai na har abada, kuma ba za su taɓa mutuwa ba, kuma ba wanda zai ƙwace su daga hannuna.

29 Ubana wanda ya ba ni tumakin ya fi duka girma, ba kuwa mai iya ƙwace tumakina daga hannunsa.

30 Da ni da Uban, ɗaya ne.”

31 Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu domin su jejjefe shi.

32 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Na yi muku ayyuka masu kyau masu yawa kuma daga wurin Uba, a kan wanne a cikinsu za ku jejjefe ni?”

33 Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ai, ba don wani aiki mai kyau da ka yi ne za mu jejjefe ka ba, amma don maganar saɓo ga Allah ne. Kai da kake mutum kawai kana mai da kanka daidai da Allah.”

34 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, a rubuce yake a Koyarwarku cewa Allah ya ce, ‘Na ce ku alloli ne.’

35 Mun dai san cewa Rubutacciyar Maganar Allah ba ta ƙarya. Idan Ubangiji ya ce da waɗanda suka ji saƙonsa ‘alloli’,

36 to, ni wanda Uba ya keɓe ya kuma aiko ni duniya, maganar reni ga Allah nake yi ke nan da na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne’?

37 In ba ayyukan da Ubana yake yi su nake yi ba, to, kada ku gaskata da ni.

38 Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata da ni ba, ku gaskata da ayyukan, don ku sani, ku kuma gane cewa, Uban yana cikina, ni kuma ina cikin Uban.”

39 Sai suka sāke yin ƙoƙarin kama Yesu, amma ya fita daga hannunsu.

40 Saˈan nan Yesu ya sāke komawa ƙetaren Kogin Yodan wurin da Yohanna ya yi baftisma da farko, ya zauna a can.

41 Sai mutane da yawa suka zo wurinsa. Mutanen suka dinga cewa, “Ai, Yohanna bai taɓa yin alamar ban mamaki ba, amma duk abin da ya faɗa game da wannan mutum gaskiya ne.”

42 A wannan wuri kuwa mutane da yawa suka ba da gaskiya ga Yesu.

Open Bible reader