Skip to content

Hausa Bible

Yakubu 4

1 Mene ne yake kawo faɗa da jayayya tsakaninku? Ba shakka suna zuwa ne ta dalilin kwaɗayi iri-iri waɗanda suke yaƙi a cikinku.

2 Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisan kai. Kukan nemi abu da tsanani, ku kāsa samu, sai ku shiga faɗa da yin jayayya. Ai, ba ku sami abin da kuke nema ba saboda ba ku roƙa ba.

3 Kuma saˈad da kukan roƙa ba ku samu ba, gama kukan roƙa da mugun nufi. Kuna so ku kashe abin da kun samu a kan ayyukan banza na jin daɗin jikinku ne.

4 Ku marasa aminci! Ba ku sani ba cewa zaman abokin duniya yana daidai da zaman gāba da Allah? Gama duk mai ƙaunar duniya, ya mai da kansa mai gāba da Allah ke nan.

5 Ko kuna tsammani a banza ne Rubutacciyar Maganar Allah ta ce, “Allah yana cike da tsananin kishin ƙauna a kan ruhun da ya sa a cikinmu?

6 Amma Allah yana ƙara mana alherinsa mai yawa, shi ya sa Rubutacciyar Maganarsa ta ce, “Allah yana ƙin mai girman kai, amma yana yin alheri ga mai sauƙin kai.”

7 Domin haka sai ku miƙa kanku ɗungum ga Allah. Kada ku ba Shaiɗan dama, shi kuwa zai guje muku.

8 Ku yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da ku. Ya ku masu zunubi, ku tsabtace hannuwanku daga ayyukan zunubi, ku tsabtace zukatanku, ya ku munafukai.

9 Ku yi baƙin ciki, ku yi kuka, ku yi hawaye. Bari dariyarku ta koma kuka, farin cikinku kuma yă koma baƙin ciki.

10 Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Ubangiji, shi kuwa zai ɗaukaka ku.

11 ˈYanˈuwa, kada ku zama masu maganar zargin juna. Saboda duk wanda yake zargin ɗanˈuwansa mai bi, ko ya ɗora masa laifi, yana zargin Koyarwar Musa ke nan, yana kuma ɗora wa Koyarwar laifi. Gama saˈad da ka yi wa Koyarwar Musa shariˈa, ba ka miƙa kanka ga yin biyayya da Koyarwar Musa ba, maimakon haka ka zama mai yi mata shariˈa.

12 Allah ne kaɗai mai ba da Koyarwa, shi ne kuma mai yin shariˈa. Shi kaɗai yake ba da ceto, kuma shi yake da ikon halakarwa. Saboda haka, wane ne kai da har ka isa ka ɗora wa ɗanˈuwanka laifi?

13 Ku saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu tafi gari kaza, mu yi shekara guda muna ta kasuwanci muna cin riba.”

14 Ga shi kuwa ba ku ma san me zai faru gobe ba. Shin, wane irin abu ne ranku? Ai, abu ne kamar hazo wanda yake bayyana a ɗan lokaci saˈan nan yă ɓace.

15 Ya kamata ku ce, “Idan Allah ya yarda, idan kuma muna cikin masu rai, za mu yi kaza da kaza.”

16 Amma ga shi, yanzu kuna taƙama kuna yanga. Ai, wannan irin taƙama muguwar abu ne.

17 Saboda haka duk wanda ya san abin da yă kamata ya yi amma ya ƙi yi, ya yi zunubi ke nan.

Open Bible reader