Hausa Bible
Yakubu 2
1 ˈYanˈuwana, kada ku nuna bambanci a tsakaninku, da yake kun sa bangaskiyarku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangiji Maɗaukaki.
2 Misali, mai yiwuwa wani mai arziki ya shigo cikin taronku yana sanye da zoben zinariya da kuma riguna masu daraja, saˈan nan kuma wani matalauci ya shigo da rigar da ta yayyage.
3 Idan za ku fi ba mai arzikin nan girma ku ce masa, “Ga kujera mai kyau ka zauna,” amma ku ce wa matalaucin nan, “Ka tsaya a can,” ko kuma “Ka zauna a ƙasa,”
4 ai, bambanci ke nan kuke nuna wa junanku, kuna kuma yanke shariˈa da mugun tunani.
5 Ku ji, ˈyanˈuwana waɗanda nake ƙauna! Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su zama masu arziki cikin bangaskiya ba? Ba su ne kuma za su gāji mulkin nan wanda ya yi alkawari wa waɗanda suke ƙaunarsa ba?
6 Amma ku, kukan rena matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke wulaƙanta ku ba? Ba su ne suke jan ku zuwa gaban kotu ba?
7 Ba su ne kuma suke maganar saɓo a kan sunan nan mai daraja da aka san ku da shi ba?
8 Idan kun yi biyayya da Koyarwar nan ta mulkin Allah wadda take cikin Rubutacciyar Maganar Allah cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka, kun yi daidai.”
9 Amma idan kuna nuna bambanci a tsakaninku, wannan zunubi ne. Bisa ga Koyarwar Musa kun zama masu karye doka.
10 Gama duk wanda ya kiyaye dukan Koyarwar Musa, amma ya karye ɗaya, to, ya karye dukan ke nan.
11 Gama shi wanda ya ce, “Kada ka yi zina” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisan kai.” Idan ba ka yi zina ba, amma ka kashe wani, to, ka zama mai karye Koyarwar ke nan.
12 Saboda haka, ku yi maganarku da aikinku yadda da za ta nuna cewa ku mutane ne da za a yi musu shariˈa bisa ga ƙaˈida mai ba da ˈyanci.
13 Gama a lokacin shariˈa, Allah ba zai nuna jinƙai ga mutum marar jinƙai ba. Amma jinƙai zai yi nasara a kan hukunci.
14 ˈYanˈuwa, ina amfani mutum yă ce yana da bangaskiya amma ayyukansa ba su nuna haka ba? Anya! Wannan bangaskiyarsa za ta iya cetonsa kuwa?
15 Misali, mai yiwuwa wani ɗanˈuwa ko wata ˈyarˈuwa suna zama babu rigar sawa, kuma babu abinci na yau da kullum.
16 Idan waninku ya ce musu, “Ku sauka lafiya, Allah ya ba ku abinci da abin sawa,” amma bai yi kome game da bukatarsu nan ta jiki ba, to, ina amfanin wannan?
17 Haka kuma bangaskiya wadda ba ta da ayyukan da suke tabbatar da ita banza ce.
18 Wani zai iya cewa, “Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuma ina da ayyuka ne.” To, nuna mini bangaskiyarka marar ayyuka, ni kuma zan nuna maka bangaskiyata ta wurin ayyukana.
19 Ka gaskata Allah ɗaya ne? To madalla. Ai, ko aljanu ma sun gaskata haka, har ma da rawar jiki.
20 Kai marar hikima! Ko kana bukata har yanzu in tabbata maka yadda bangaskiya marar ayyuka banza ce?
21 Saˈad da kakanmu Ibrahim ya ba da ɗansa Ishaku a kan bagaden hadaya, ba saboda ayyukansa ne aka shaida shi mai adalci ba?
22 To, ka gani yadda bangaskiyarsa tana tafiya tare da ayyukansa, kuma bangaskiyarsa ta zama cikakkiya ta wurin ayyukansa.
23 A nan aka cika Rubutacciyar Maganar Allah cewa, “Saboda Ibrahim ya ba da gaskiya ga Allah, sai Allah ya lissafta wannan adalci ne a gare shi.” Ta dalilin haka kuwa aka ce da Ibrahim abokin Allah.
24 To, kun gani, mutum yana samun zaman marar laifi a gaban Allah saboda ayyukansa ne, ba saboda bangaskiya ita kaɗai ba.
25 Haka yake kuma da karuwar nan Rahab a lokacin da ta ɓoye ˈyan leƙen asirin ƙasar nan, ta kuma taimake su sun tsira ta wata hanya dabam. Ba ta wurin ayyuka ne ta zama marar laifi ba?
26 Saboda haka kamar yadda jikin mutumin da ba shi da ruhu gawa ne, haka kuma bangaskiya marar ayyuka take daidai da gawa.