Skip to content

Hausa Bible

Yakubu 1

1 Daga Yakub bawan Allah da kuma na Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga zuriya goma sha biyun nan da suke a warwatse koˈina cikin duniya. Gaisuwa mai yawa.

2 ˈYanˈuwa, ku mai da kowace irin wahalar da ta same ku abin farin ciki,

3 gama kun san wahalar nan takan gwada bangaskiyarku takan haifar da jimrewa.

4 Sai jimrewarku kuma yă cika aikinsa, ya kai ku ga zaman natsatsu da cikakku har kada ku rasa kome.

5 In waninku yana bukatar hikima, sai yă roƙi Allah wanda yake ba kowa hannu sake ba tare da gori ba, zai kuwa ba shi.

6 Amma sai yă roƙa da bangaskiya, ban da shakka, domin duk mai shakka yana kama da raƙuman ruwan teku waɗanda iska take hurawa tana jujjuye su a ta koˈina.

7 Kada irin mutumin nan yă yi tsammani zai sami wani abu daga wurin Ubangiji,

8 gama shi mai zuciya biyu ne, ba ya ajiye hankalinsa a wuri ɗaya a cikin dukan ayyukansa.

9 Bari ɗanˈuwan da yake matalauci yă yi taƙama da ɗaukakarsa.

10 Haka ma wanda yake mai arziki yă yi taƙama da ƙasƙancinsa. Gama mai arziki zai bushe kamar fulawar ciyawa.

11 Gama in rana ta fito ta yi zafi ƙwarai, takan sa ciyawa ta bushe, sai fulawarta ta fāɗi, kyanta kuma yă ɓace. Haka ma mai arziki zai ɓace cikin kaiwa da kawowarsa.

12 Mai albarka ne mutumin da ya jimre cikin wahalarsa, gama in ya jimre cikin gwaji, zai karɓi hular lada na rai madawwami wanda Allah ya yi alkawari zai ba dukan masu ƙaunarsa.

13 Idan jarraba ta sami mutum, kada yă ce Allah ne ya jarrabce shi. Domin Allah ba ya jarrabtar kowa da mugunta, kuma ba ya yiwuwa a jarrabce shi.

14 Kowane mutum dai yakan sami jarraba saˈad da mugun kwaɗayinsa ya ruɗe shi, ya kuma sha kansa.

15 Mugun kwaɗayi kuwa in ya yi ciki yakan haifi zunubi. Zunubi in ya yi girma yakan haifi mutuwa.

16 ˈYanˈuwana waɗanda nake ƙauna, kada ku yarda a ruɗe ku.

17 Kowace baiwa mai kyau, da kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke. Sun sauko ne daga wurin Allah Uba wanda ya halicci rana, da wata, da taurari duka. Shi kuwa ba ya canjawa, ba ya juye-juye kamar inuwa.

18 Bisa ga nufinsa Allah ya ba mu rai ta wurin kalmarsa mai gaskiya domin mu zama kamar nunan fari na dukan halittarsa.

19 ˈYanˈuwana, waɗanda nake ƙauna, ku sani fa ya kamata kowa yă kasance mai saurin ji, amma ba mai saurin magana ko mai saurin fushi ba,

20 saboda fushin mutum ba ya kai shi ga aikata adalcin Allah.

21 Sai ku kawar da ƙazamin halin nan na zunubi da kuma kowace irin mugunta. Saˈan nan a cikin sauƙin kai ku karɓi kalmar nan da aka shuka a zuciyarku, wadda kuma tana iya kai ku ga ceto.

22 Ku zama masu aikata kalmar Allah, ba masu ji kawai ba, wato kuna ruɗin kanku.

23 Domin duk wanda yake jin kalmar kawai amma ba ya aikatawa yana kama da mutumin da ya dubi fuskarsa a madubi,

24 bayan da ya tashi daga wurin, nan da nan sai yă manta da yadda fuskarsa take.

25 Amma mutumin da ya mai da hankalinsa wajen bincike cikakkiyar koyarwar nan wadda ita ce mai kawo ˈyanci, za a sa masa albarka cikin dukan abin da yake yi, idan har bai zama mai ji kawai yă manta ba, amma ya zama mai naciya cikin aikatawa.

26 Idan wani yana tsammani shi mai addini ne sosai, amma ba ya kame bakinsa, to, yana ruɗin kansa ne, addininsa kuma banza ne.

27 Addinin da Allah Uba ya tabbatar mai tsarki kuma mai gaskiya, shi ne, a kula da matan da mazansu suka mutu, da kuma marayu cikin shan wuyarsu, a kuma keɓe kai daga muguwar rayuwa ta duniya.

Open Bible reader