Skip to content

Hausa Bible

Galatiyawa 6

1 ˈYanˈuwa, in an ga wani yana cikin yin laifi, ku da Ruhu Mai Tsarki yake tare da ku, sai ku komo da shi kan hanya. Amma ku yi haka da halin tawaliˈu, a hankali kuma, domin kada maimakon dawowar da ɗanˈuwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba.

2 Ku taimaki juna ta wajen ɗaukar wahalar juna. Ta haka ne za ku cika koyarwar Almasihu.

3 In wani yana tsammani shi wani abu ne, amma kuwa shi ba kome ba ne, ruɗin kansa yake yi.

4 Amma bari kowa yă gwada aikinsa yă gani. Idan ya yi kyau, saˈan nan zai iya taƙama da abin da ya yi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba.

5 Gama ya kamata kowa yă ɗauki kayan kansa.

6 Duk wanda aka koya masa maganar Almasihu sai yă raba dukan abubuwansa na alheri da wanda ya koya masa.

7 Kada ku ruɗi kanku, ai, ba ya yiwuwa a yi wa Allah wayo. Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.

8 Gama idan mutum ya shuka ta biyan shaˈawar jiki, zai kai shi girbin mutuwa. Idan kuwa ya shuka ta biyan bukatar Ruhu, zai kai shi ga girbin rai na har abada.

9 Saboda haka kada mu gaji da yin abin da yake da kyau. Gama idan ba mu gaji muka bar ƙoƙari ba, lokaci zai zo da za mu yi girbi mai albarka.

10 To, saboda haka, duk saˈad da muke da zarafi, sai mu kyautata wa dukan mutane, musamman waɗanda suke ˈyanˈuwanmu cikin Almasihu.

11 Ku dubi irin manya-manyan rubutun da nake yi muku da hannuna.

12 To, mutanen nan da suke so a gani su wani abu ne, su ne suke so su tilasta muku ku yi kaciya. Suna yi muku haka ne domin suna tsoron tsananin da za su sha saboda gicciyen Almasihu.

13 Ai, ko waɗanda aka yi musu kaciya ma ba sa kiyaye Koyarwar Musa. Su dai suna so a yi muku kaciya domin su yi ta ɗaga kai cewa su ne suka sa a yi muku kaciya.

14 Amma ni ko kusa ba zan ɗaga kai ba, sai dai game da gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu. Gama ta wurin mutuwarsa a kan gicciye ne shaˈanin duniya ya mutu a gare ni, ni kuma na mutu ga shaˈanin duniya.

15 Kaciya da rashin kaciya ba kome suke ba, babban abu shi ne mutum yă zama sabuwar halitta.

16 Salama da jinƙai su kasance tare da dukan waɗanda suke bin wannan ƙaˈida, wato tare da ainihin Israˈila ta Allah.

17 Daga yanzu zuwa nan gaba ˈyanˈuwa, kada kowa yă ƙara damuna da wani abu, gama alamun raunukan da nake da su a jikina sun nuna cewa ni bawan Yesu ne.

18 Bari alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă kasance tare da ruhunku, ˈyanˈuwa. Amin.

Open Bible reader