Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 6

1 To, a kwanakin nan da yawan almajirai yake ƙaruwa, sai Yahudawa masu jin Helenanci suka yi gunaguni a kan Yahudawa masu jin yaren Aramaya. Yahudawa masu jin Helenanci sun yi gunaguni ne don a wajen rabon taimako na kowace rana ba a kula da matansu waɗanda mazansu suka mutu.

2 Sai sha biyun nan suka kirawo duk jamaˈar masu bi, suka ce, “Ai, bai yi kyau mu bar waˈazin kalmar Allah, mu shiga shaˈanin abinci ba.

3 Saboda haka, ˈyanˈuwa, sai ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku, waɗanda aka san su da halin kirki, cike da Ruhu da kuma hikima, waɗanda za mu ba su wannan aiki.

4 Mu kuma sai mu sami damar nacewa da yin adduˈa da kuma koyar da kalmar Allah.”

5 Jamaˈa duka kuwa suka ji daɗin abin da suka faɗa. Sai suka zaɓi Istifanus, wani mutumin da yake cike da bangaskiya da Ruhu Mai Tsarki, da Filibus, da Burokoras, da Nikanor, da Timon, da Barminas, da Nikolas mutumin Antakiya, wanda ba Bayahude ba ne amma ya shiga addinin Yahudawa.

6 Waɗannan ne aka gabatar a gaban manzanni, waɗanda suka yi musu adduˈa kuma suka sa musu hannun albarka.

7 Kalmar Allah kuwa sai ƙara yaɗuwa take yi. Yawan masu bi kuma a cikin birnin Urushalima sai ƙaruwa yake ta yi sosai, firistoci masu yawa sosai kuma suka karɓi bangaskiyar nan.

8 To, Istifanus, cike da alheri da iko, ya aikata manyan ayyukan ban mamaki da alamu a cikin jamaˈa.

9 Sai waɗansu na majamiˈar da ake ce da ita Majamiˈar ˈYantattu, suka tayar wa Istifanus da gardama. Waɗannan kuwa Yahudawa ne daga Sayirin da Alekzandiriya, da kuma daga ƙasar Kilikiya, da ta Asiya.

10 Amma a ina! Sun kāsa gardama da shi, domin yana magana da hikimar da Ruhun Allah ya ba shi.

11 Sai suka zuga waɗansu mutane a ɓoye domin su ce, “Mun ji shi yana zagin annabi Musa, yana yi wa Allah maganar reni.”

12 Ta haka, suka tā da hankalin jamaˈa, da dattawa, da malaman Koyarwar Musa, su kuma suka hau masa, suka kama shi, suka kai shi gaban majalisa.

13 Sai shugabannin jamaˈa suka kawo masu shaidar ƙarya, waɗanda suka ce, “Mutumin nan koyaushe yana maganar banza a kan wurin nan mai tsarki da kuma Koyarwar Musa.

14 Ga shi, mun ji shi yana cewa wai Yesu Banazaret nan zai rushe wurin nan, yă kuma canja duk alˈadun da annabi Musa ya bar mana.”

15 Duk waɗanda suke zaune a majalisar kuwa suka zuba masa ido, suka ga fuskarsa ta zama kamar ta malaˈika.

Open Bible reader