Hausa Bible
Ayyukan Manzanni 2
1 Da ranar Bikin Fentikos ta yi, duk masu bi suna tare a wuri ɗaya.
2 Ba labari sai aka ji wata ƙara daga sama kamar ta babbar iska, ta cika dukan gidan da suke zaune a ciki.
3 Sai ga waɗansu abubuwa kamar harsunan wuta, suka bayyana a gare su, suna rarrabuwa, suna sassauka a kan kowane ɗayansu.
4 Sai duk aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka kuma fara magana da waɗansu yare dabam-dabam, yadda Ruhun ya yi musu baiwar yin magana.
5 To, akwai waɗansu ˈyan addinin Yahudawa waɗanda suke zama a Urushalima sun kuwa zo ne daga kowace alˈumma a ƙarƙashin sama.
6 Da suka ji ƙarar iskar ɗin nan, sai taron mutane ya haɗu. Dukansu suka yi mamaki, don kowannensu ya ji taron suna magana da yaren garinsu.
7 Suka yi mamaki sosai, suna cewa, “Ashe, duk masu maganar nan ba Galilawa ba ne?
8 Yaya kuma kowannenmu yana ji suna magana da yarensa?”
9 Ga mu kuwa, Fartiyawa, da Mediyawa, da Elamawa, da mutanen Mesofotamiya, da na yankin Yahudiya, da na Kafadokiya, da na Fantus, da na Asiya,
10 da na Firijiya, da na Famfiliya, da na Masar, da kuma na kewayen Sayirin ta ƙasar Libiya, har ma da baƙi daga Roma. Ga mu waɗanda aka haife mu a cikin addinin Yahudawa da waɗanda suka tuba suka shiga addininmu.
11 Ga mu kuma Kiritawa, da Larabawa, duk muna ji suna magana da yarenmu a kan manyan abubuwan da Allah ya yi.
12 Duka kuwa suka yi mamaki, suka ruɗe, suna ce wa juna, “Mene ne wannan yake nufi?”
13 Amma waɗansu suka yi musu baˈa suka ce, “Ruwan inabi suka sha suka bugu.”
14 Sai Bitrus ya tashi tsaye tare da sha ɗayan nan, ya ɗaga murya ya yi musu jawabi, ya ce, “Ku ˈyanˈuwana Yahudawa da dukan masu zama a Urushalima, ku ji, ku kuma kula da abin da zan faɗa muku.
15 Mutanen nan ba su bugu ba kamar yadda kuke tsammani, tun da yake yanzu ƙarfe tara ne kawai na safe.
16 Wannan, ai, shi ne abin da annabi Yowel ya faɗa cewa,
17 “ ‘Allah ya ce, a kwanakin ƙarshe zan zubo wa dukan ˈyan Adam Ruhuna. ˈYaˈyanku maza da mata za su yi annabci. Samarinku za su ga ruˈuyoyi, tsofaffinku kuma za su yi mafarkai.
18 Hakika, har ma a kwanakin nan zan zubo Ruhuna a kan bayina maza da mata, za su kuma yi annabci.
19 Zan nuna abubuwan ban mamaki a sararin sama, da alamun ban mamaki a nan ƙasa, wato jini, da wuta, da kuma baƙin hayaƙi.
20 Za a mai da rana duhu, wata kuma zai zama ja kamar jini, kafin Ranar Ubangiji ta zo, babbar Ranar nan mai ɗaukaka.
21 A lokacin nan ne duk wanda ya kira ga sunan Ubangiji zai sami ceto.’ ”
22 “Ya ku ˈyanˈuwana Israˈilawa, ku ji wannan magana. Yesu Banazaret mutum ne da Allah ya tabbatar muku cewa ya yarda da shi. Allah ya nuna wannan ta wurin ayyukan ban mamaki, da abubuwan ban mamaki, da alamu waɗanda ya yi ta wurin Yesu a cikinku, kamar yadda ku ma kuka sani da kanku don duk sun faru a idonku.
23 Shi mutumin nan, an ba da shi gare ku bisa ga yadda Allah ya ƙaddara kuma da yadda ya riga ya sani, kuka kuwa gicciye shi, kuka kashe shi ta hannun masu zunubi.
24 Amma Allah ya fanshe shi daga ikon mutuwa, ya tashe shi daga matattu da yake ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.
25 Gama Dawuda ya yi magana game da shi ya ce, “ ‘Kullum ina ganin Ubangiji, yana a hannun damana, domin kada in jijjigu.
26 Saboda haka zuciyata tana murna, harshena yana rera waƙar farin ciki, jikina zai zauna da sa rai.
27 Gama ba zai bar raina a kabari ba, ko yă bar Mai Tsarkinsa yă ruɓa ba.
28 Ka koya mini hanyar da za ta kai ga rai. Za ka cika ni da farin ciki ta wurin kasancewarka tare da ni.’ ”
29 “ˈYanˈuwana Israˈilawa, zan iya yi muku magana babu shakka game da kakanmu Dawuda. Dawuda ya mutu, an binne shi, kabarinsa kuma yana nan tare da mu har wa yau.
30 Shi annabi ne, kuma ya san Allah ya yi masa alkawari tare da rantsuwa, cewa zai naɗa wani daga cikin zuriyarsa sarki, kamar yadda ya naɗa shi Dawuda.
31 Tun da yake Dawuda ya hango haka, ya kuma yi magana a kan tashin Almasihu daga matattu cewa ba za a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma ba zai ruɓa ba.
32 Allah ya tā da Yesun nan daga matattu, mu kuwa duk shaidu ne ga wannan.
33 Da yake an ɗaukaka shi ga hannun dama na Allah, ya kuma karɓi Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, yadda aka yi alkawari, sai ya zubo Ruhun a kanmu. Shi ne ya kawo abin da kuke gani, kuke kuma ji.
34 Ai, ba Dawuda ne ya hau sama ba, amma shi da kansa ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, Zauna a hannun damana,
35 sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin ƙafafunka.’ ”
36 “Saboda haka, sai duk jamaˈar Israˈila fa su sani cewa Yesun nan da kuka gicciye, Allah ya mai da shi Ubangiji, da kuma Almasihu.”
37 To, da suka ji haka, kalmar ta soki zuciyarsu, suka ce wa Bitrus da sauran manzannin, “ˈYanˈuwa, mene ne za mu yi?”
38 Sai Bitrus ya ce musu, “Sai ku tuba, a yi wa kowannenku baftisma cikin sunan Yesu Almasihu don a gafarta muku zunubanku. Za ku kuwa sami kyautar Ruhu Mai Tsarki.
39 Gama wannan alkawarin Allah dominku ne tare da ˈyaˈyanku, da kuma dukan waɗanda suke nesa, wato dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu ya kira zuwa wurinsa.”
40 Sai ya yi ta tabbatar musu da maganganu masu yawa, yana ta yi musu gargaɗi yana cewa, “Ku cece kanku daga muguwar tsarar nan masu rayuwar kwana-kwana.”
41 Waɗanda suka yarda da maganar Bitrus kuwa aka yi musu baftisma. A ranar nan kuma suka ƙaru da wajen mutum dubu uku.
42 Sai suka miƙa kansu duka ga koyarwar da manzanni suke yi, suna zumunci, suna cin abinci tare, suke kuma yin adduˈa.
43 Sai tsoro ya kama kowa, don Allah yana yin ayyukan ban mamaki da alamu da yawa ta wurin manzannin.
44 Dukan waɗanda suka ba da gaskiya sun kasance tare cikin zumunci, suna amfani da kome nasu tare gaba ɗaya.
45 Suka sayar da abin da suke da shi, suka rarraba wa kowa kuɗin bisa ga bukatarsa.
46 Kowace rana kuma suna zuwa Haikali da nufi ɗaya. Suna cin abinci tare a gidajensu, suna ci suna sha da farin ciki, da yardar rai,
47 tare da yabon Allah. Suna kuma da farin jini a wurin mutane duka. Kowace rana kuma Ubangiji yana ƙara musu waɗanda ake cetonsu.