Hausa Bible
Titus 1
1 Daga Bulus bawan Allah kuma manzon Yesu Almasihu domin in ƙarfafa bangaskiyar waɗanda Allah ya zaɓa, in taimake su su san gaskiyar da ta haifar da hali irin na Allah
2 ta wurin sa zuciya ga rai madawwami. Allah wanda da ba ya ƙarya ya yi alkawarin wannan rai madawwami tun kafin farawar zamanai.
3 Saˈan nan a daidai lokaci ya bayyana shi ta wurin saƙonsa wanda nake waˈazi, wanda kuma aka ba ni amanarsa ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu.
4 Zuwa ga Titus, ɗana na gaske cikin bangaskiya da muke da ita dukanmu. Alheri da salama daga Allah Uba da Almasihu Yesu Mai Cetonmu su kasance tare da kai.
5 Na bar ka a Kirit domin ka ƙarasa daidaita alˈamuran da suka rage a yi, ka kuma naɗa dattawa a kowane gari, kamar yadda na umarce ka.
6 Ya kamata dattijo yă kasance marar laifi a gaban mutane, mai mace ɗaya, wanda kuma ˈyaˈyansa masu ba da gaskiya ne, kuma ba a zarginsu da halin iskanci ko rashin biyayya ba.
7 Tun da yake mai kula da jamaˈar masu bi mai riƙon amanar Allah ne, dole ne yă kasance marar laifi ga kowa. Kada yă zama mai nuna iko, ko mai saurin fushi, ko mai buguwa, ko mai saurin dūka, ko kuwa mai kwaɗayin ƙazamar riba.
8 A maimakon haka, yă kasance mai karɓar baƙi, mai son nagarta, kuma mai kamun kansa, mai gaskiya a zuci, mai tsarki, mai horar da kansa.
9 Mai lura da jamaˈar ya kamata yă zama wanda yana riƙe da tabbatacciyar maganar nan ta Allah daidai kamar yadda aka koyar, domin yă ƙarfafa waɗansu ta wurin koyarwa ta gaskiya, yă kuma iya ƙaryata kuskuren waɗanda suke gāba da koyarwar.
10 Akwai ˈyan tawaye da yawa, masu maganganun banza, masu ruɗu, musamman cikin Yahudawan da suka nace a kan maganar kaciya.
11 Dole ne a sa su su yi shiru, gama suna tā da hankalin iyalai da yawa ta wurin koyar da abin da bai kamata ba domin neman ƙazamar riba.
12 Ai, wani annabi na Kiritawa shi ma ya faɗa cewa, “Kiritawa kullum masu ƙarya ne, mugayen dabbobi, ˈyan ƙyuya masu yawan cin abinci.”
13 Wannan shaida gaskiya ce. Saboda haka ka tsawata musu da zafi, domin su kafu a kan gaskiya cikin bangaskiya,
14 domin su daina kasa kunne ga tatsuniyoyin Yahudawa, da bin dokokin mutane waɗanda suka ƙi gaskiya.
15 Ga mai tsabtar zuciya kome mai tsabta ne. Amma ga masu ƙazanta da marasa ba da gaskiya ba abin da yake da tsabta. Gaskiya dukan tunanin zuciyarsu da hankalinsu ƙazantattu ne.
16 Da baki suna cewa sun san Allah, amma ta wurin ayyukansu suna musūn saninsa. Sun zama abin ƙyama, marasa biyayya, kuma ba su ma isa su yi aiki nagari ba.