Hausa Bible
Filibiyawa 4
1 Saboda haka, ˈyanˈuwana, ku da kuke a zuciyata kullum, har ina marmarin ganinku, ku da kuke farin cikina, da hular ladan nasarar da zan samu saboda aikina, ina roƙonku ku tsaya da ƙarfi cikin Ubangiji, ku waɗanda nake ƙauna.
2 Ina jan kunnen Yudiya da Sintiki, su shirya da juna saboda su na Ubangiji ne.
3 Kai kuma abokin aikina mai aminci, ina roƙonka ka taimaki waɗannan mata, saboda sun sha fama tare da ni a cikin aikin shelar labari mai daɗi. Haka ma Kilemen da sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suke a rubuce a Littafin Rai.
4 Ku yi farin ciki cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku, yi farin ciki.
5 Bari ku kasance da halin haƙuri cikin dangantakarmu da kowa. Ku tuna fa, Ubangiji ya yi kusan zuwa.
6 Kada ku damu da kome, sai dai a cikin kome ku faɗa wa Allah bukatunku ta wurin adduˈa da roƙo, tare da godiya.
7 Ta haka kuwa Allah zai ba ku salama iri wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam, za ta kuma tsare zukatanku da tunaninku cikin Almasihu Yesu.
8 A ƙarshe kuma, ˈyanˈuwana, ku dinga yin tunani a kan iyakar abin da yake na gaskiya, da iyakar abin da ya isa bangirma, da iyakar abin da yake daidai, da iyakar abin da yake da tsabta, da iyakar abin da yake jawo ƙauna, da iyakar abin da yake na kirki, wato a kan dukan abin da yake mafi kyau, ko abin da ya isa yabo, a kan waɗannan sai ku yi tunani.
9 Ku aikata abubuwan da kuka koya kuka kuma karɓa, da kuma abubuwan da kuka ji, kuka gani a wurina. Allah mai salama kuwa zai kasance tare da ku.
10 Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji saboda yanzu kun sāke nuna kuna kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni, amma ba ku sami dama ku nuna mini ba.
11 Ba wai ina kukan rashin wani abu ba ne. Ai, na koyi yadda zan zauna da kwanciyar rai a kowane halin da nake ciki.
12 Na san yadda zan zauna ko cikin talauci ko cikin yalwata. Zan iya zama a kowane irin hali, ko cikin yunwa ko cikin ƙoshi, ko cikin rashi ko cikin samu.
13 Zan iya yin kome ta wurin Almasihu wanda yake ƙarfafa ni.
14 Duk da haka, kun kyauta da kuka taimake ni a lokacin da nake cikin wahala.
15 Ku Filibiyawa kun sani, a lokacin da na fara aikin waˈazin labari mai daɗi, da na bar ƙasar Makidoniya ba wata jamaˈar masu bin Yesu wadda ta haɗa kai da ni ta wurin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai.
16 Domin ko a lokacin da nake Tasalonika, kun aiko mini da taimakon abubuwan da nake bukata ba ma sau ɗaya ba.
17 Kada ku yi tsammani ina neman kyauta a wurinku ne, aˈa, sai dai ina neman abin da a ƙara lissafta a kan ribarku.
18 An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Abaforiditus. Wannan bayarwa ce mai ƙanshi, hadaya ce kuma wadda Allah zai karɓa yă kuma ji daɗinsa.
19 Allahna kuma zai biya muku kowace bukatarku bisa ga ɗaukakar albarkunsa a yalwace ta wurin Almasihu Yesu.
20 Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu da Ubanmu, har abada. Amin.
21 Ku gai da dukan tsarkaka cikin Almasihu Yesu. ˈYanˈuwan da suke tare da ni suna gaishe ku.
22 Tsarkaka duka suna gaishe ku, musamman waɗanda suke a fādar Kaisar.
23 Alherin Ubangiji Yesu Almasihu yă kasance tare da ruhunku. Amin.