Hausa Bible
Matiyu 9
1 Sai Yesu ya shiga jirgin ruwa, ya haye tekun ya je Kafarnahum, garin da ya yi girma.
2 Sai aka kawo masa wani shanyayye yana kwance a kan tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Kada ka damu, ɗana, an gafarta maka zunubanka.”
3 Da jin wannan, waɗansu malaman Koyarwar Musa suka ce wa junansu, “Wannan mutumin yana yi wa Allah saɓo.”
4 Amma Yesu ya san abin da suke tunani a kai, sai ya ce musu, “Don me kuke yin mugun tunani a zuciyarku haka?
5 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya’?
6 Amma ina so ku sani cewa Ɗan Mutum yana da iko yă gafarta zunubai a duniya.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ka ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.”
7 Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gidansa.
8 Da taron mutanen suka ga haka sai suka ji tsoro, suka ɗaukaka Allah wanda ya ba mutane irin wannan iko.
9 Da Yesu ya ci gaba da tafiya, sai ya ga wani mutum wanda ake ce da shi Matiyu, yana zaune a wurin karɓar haraji. Sai Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.
10 Daga baya, da Yesu yana cin abinci a gidan Matiyu, sai masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa suka zo suka zauna tare da shi da almajiransa.
11 Da Farisiyawa suka ga haka, sai suka ce wa almajiransa, “Don me malaminku yake cin abinci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”
12 Da Yesu ya ji wannan sai ya ce, “Masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.
13 Ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake so a wurinku, ba hadaya ba.’ Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai domin masu zunubi.”
14 Ana nan sai almajiran Yohanna Mai Baftisma suka zo wurin Yesu suka ce masa, “Me ya sa mu da Farisiyawa mukan yi azumi, amma almajiranka ba sa yi?”
15 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Abokan ango za su yi baƙin ciki tun ango yana tare da su ne? Ai, kwanaki suna zuwa da za a ɗauki angon a bar su. A lokacin ne za su yi azumi.
16 “Ba wanda zai yi facin tsohuwar riga da sabon yadi, gama facin zai naɗe rigar, yagewar ma za ta fi ta dā.
17Ba wanda zai zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. Idan ma an zuba, salkunan za su fashe, ruwan inabin kuma yă zube, salkunan kuma su lalace. Sabon ruwan inabi dai, sai a zuba shi a cikin sababbin salkuna. Da haka ba za a rasa ko ruwan, ko kuma salkunan ba.”
18 Yesu yana kan gaya musu haka ke nan, sai ga wani shugaban majamiˈa ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “ˈYata ta mutu ba da jimawa ba, ka zo ka taɓa ta, za ta tashi.”
19 Yesu kuwa ya tashi tare da almajiransa, suka bi mutumin.
20 Sai ga wata mata da ta yi shekara goma sha biyu tana fama da ciwon zubar da jini, ta zo ta bayansa ta taɓa bakin rigarsa,
21 gama ta ce a ranta, “Idan na taɓa ko da rigarsa kawai, zan warke.”
22 Da Yesu ya juya ya gan ta, sai ya ce, “Kada ki damu ˈyata. Bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take matar ta warke.
23 Da Yesu ya zo gidan shugaban, ya ga masu busa sarewa da taron mutane ana ta hayaniya.
24 Sai ya ce, “Ku tashi daga nan! Yarinyar ba ta mutu ba, tana barci ne kawai.” Sai suka yi masa dariyar reni.
25 Amma da aka kore su waje, sai ya shiga ya kama hannun yarinyar, sai ta tashi.
26 Labarin kuwa ya bazu duk cikin wannan yanki.
27 Yesu yana barin wurin ke nan, sai makafi biyu suka bi shi suna kira da ƙarfi suna cewa, “Ka yi mana jinƙai, ya kai Ɗan Dawuda!”
28 Da Yesu ya shiga wani gida sai makafin suka zo wurinsa, ya ce musu, “Kun ba da gaskiya zan iya warkar da ku?” Suka ce masa, “I, Ubangiji.”
29 Saˈan nan ya taɓa idanunsu ya ce, “Bisa ga bangaskiyarku za a warkar da ku.”
30 Sai idanunsu suka buɗe. Saˈan nan Yesu ya ja musu kunne sosai ya ce, “Kada ku faɗa wa kowa wannan.”
31 Amma suka fita suka yi ta baza labarinsa koˈina a ƙasar.
32 Da za su tafi, sai aka kawo wani da aljani ya hana shi magana.
33 Da aka fitar da aljanin, wannan da ba ya iya magana kuwa ya fara magana. Taron mutane kuwa suka yi mamaki suka ce, “Ba a taɓa ganin wani abu kamar haka a Israˈila ba.”
34 Amma Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon shugaban aljanu ne yake fitar da aljanun.”
35 Daga nan Yesu ya bi dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majamiˈu, yana shelar labari mai daɗi na mulkin Allah, yana kuma warkar da mutane daga kowane irin ciwo da rashin lafiya.
36 Da ya ga jamaˈa sun taru da yawa, sai ya ji tausayinsu, gama suna shan wahala kuma ba mai taimako, kamar tumakin da ba su da makiyayi.
37 Sai ya ce wa almajiransa, “Girbin yana da yawa, amma masu aikin kaɗan ne.
38 Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbin yă aiko da masu aiki su yi masa girbi.”