Hausa Bible
Matiyu 9:16
“Ba wanda zai yi facin tsohuwar riga da sabon yadi, gama facin zai naɗe rigar, yagewar ma za ta fi ta dā. 17Ba wanda zai zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. Idan ma an zuba, salkunan za su fashe, ruwan inabin kuma yă zube, salkunan kuma su lalace. Sabon ruwan inabi dai, sai a zuba shi a cikin sababbin salkuna. Da haka ba za a rasa ko ruwan, ko kuma salkunan ba.”
Open Bible reader