Hausa Bible
Matiyu 17
1 Bayan kwana shida sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakub, da ɗanˈuwan Yakub, wato Yohanna, ya kai su kan wani tudu mai tsawo, inda suka kasance su kaɗai.
2 Sai kamanninsa ya canja a gabansu, fuskarsa ta yi haske kamar rana, sai rigunan da ya sa suka yi fari fat.
3 Nan da nan sai annabi Musa da annabi Iliya suka bayyana a gare su, suna magana da Yesu.
4 Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke a nan wurin. Idan kana so zan kafa bukkoki guda uku a nan, ɗaya dominka, ɗaya domin annabi Musa, ɗaya kuma domin annabi Iliya.”
5 Yana magana ke nan sai ga wani girgije mai haske ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan shi ne Ɗana, wanda nake ƙauna, ina jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”
6 Da almajiran suka ji haka sai tsoro ya kama su sosai, har suka fāɗi ƙasa.
7 Sai Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”
8 Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu shi kaɗai.
9 Da suke saukowa daga tudun, Yesu ya ja musu kunne ya ce, “Kada ku gaya wa kowa abin da kuka gani, sai an tā da Ɗan Mutum daga matattu.”
10 Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, don me malaman Koyarwar Musa suke cewa dole sai annabi Iliya ya fara zuwa?”
11 Ya amsa ya ce, “Lallai Iliya zai zo, zai kuma gyara kome.
12 Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa gane shi ba, har ma suka yi masa abin da suka ga dama. Haka kuma Ɗan Mutum zai sha wuya a hannunsu.”
13 Sai almajiran suka gane cewa yana yi musu magana a kan Yohanna Mai Baftisma ne.
14 Da suka kai wajen taron jamaˈa, sai wani mutum ya zo wurin Yesu ya durƙusa a gabansa ya ce,
15 “Ubangiji, ka ji tausayin ɗana, yana farfaɗiya, kuma yana shan wuya sosai. Sau da yawa yakan fāɗi cikin wuta da kuma cikin ruwa.
16 Na kuwa kai shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.”
17 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ku mutanen tsarar nan, marasa bangaskiya kuma masu mugunta, har zuwa yaushe zan zauna tare da ku? Har yaushe zan jimre da ku? Ku kawo mini shi nan.”
18 Sai Yesu ya tsawata wa aljanin, aljanin kuwa ya bar yaron. Nan take yaron ya warke.
19 Sai almajiran suka zo wurin Yesu a lokacin da ba kowa tare da shi, suka ce masa, “Don me mu muka kāsa fitar da aljanin?”
20 Yesu ya ce musu, “Saboda bangaskiyarku ƙarama ce. Hakika ina gaya muku, idan kuna da bangaskiyar da ta yi ƙanƙanta kamar ƙwayar mastad, za ku iya ce wa tudun nan yă tashi daga nan zuwa can, kuma zai tashi. Ba kuwa abin da zai gagare ku.
21 Ai, irin wannan ba ya fita sai da adduˈa da azumi.”
22 Da almajiran suka taru a yankin Galili, sai Yesu ya ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga hannun mutane,
23 za su kuma kashe shi. A rana ta uku kuma za a tashe shi.” Sai almajiran suka damu sosai.
24 Da Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, masu karɓar haraji domin Haikali suka sami Bitrus suka ce masa, “Malaminku ba ya biyan harajin Haikali ne?”
25 Ya ce, “Yana biya mana.” Da Bitrus ya dawo gida, sai Yesu ya fara yi masa magana ya ce, “Me ka gani game da wannan tambaya? Daga wurin wa sarakuna suke karɓar kuɗin haraji, daga wurin ˈyaˈyansu, ko daga wurin waɗansu?”
26 Da Bitrus ya amsa, “Daga wurin waɗansu,” sai Yesu ya ce, “Wato, ˈyaˈyansu ba sa biya ke nan.
27 Duk da haka, domin kada mutanen nan su ji haushinmu, ka je teku ka jefa ƙugiya, ka buɗe bakin kifin da ka fara kamawa, za ka sami azurfar da zai isa, sai ka ɗauki azurfa ɗin ka biya harajinka da nawa.”