Hausa Bible
Matiyu 11
1 Da Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan waɗannan umarnai, sai ya tashi daga wurin ya tafi yana koyarwa yana waˈazi a garuruwansu.
2 A lokacin kuwa Yohanna Mai Baftisma yana cikin kurkuku. Saˈad da ya ji abubuwan da Almasihu yake yi, sai ya aiki almajiransa wurinsa
3 su ce masa, “Kai ne wanda zai zo, ko mu sa ido ga wani?”
4 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku koma ku faɗa wa Yohanna abin da kuka gani kuka kuma ji, wato,
5 makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, masu cutar fatar jiki suna samun tsabtacewa, kurame suna jin magana, ana tā da waɗanda suka mutu, ana kuma ba talakawa labari mai daɗi.
6 Mai albarka ne wanda bai yi shakkar bangaskiyar da yake da ita a kaina ba.”
7 Da suka tafi, sai Yesu ya fara yi wa taron mutanen magana a kan Yohanna ya ce, “Me kuka fita ku gani a daji? Kun fita ganin dogayen ciyawar da iska take kaɗawa ne?
8 To, me kuka fita ku gani? Kuna tsammani za ku ga wani wanda ya sa riguna masu kyau ne? Ai, mutanen gidan sarki ne suke sa riguna masu kyau.
9 To, me kuka fita ku gani? Annabi? I, ina gaya muku, har ma ya fi annabi.
10 Wannan shi ne wanda aka rubuta a kansa cewa, “ ‘Ga shi, na aikar da manzona yă riga ka gaba, wanda zai shirya maka hanya kafin ka zo.’
11 “Hakika ina gaya muku, ba a taɓa haifuwar wani a duniyar nan wanda ya kai Yohanna Mai Baftisma girma ba. Amma duk da haka, wanda ya fi ƙanƙanta a mulkin sama ya fi shi.
12 Tun daga zamanin Yohanna Mai Baftisma har zuwa yau mulkin Allah yana shan wuyar tashin hankali, masu tashin hankali kuma suke so su ƙwace mulkin Allah da ƙarfi.
13 Gama Koyarwar Musa da littattafan annabawa duka sun yi magana a kan mulkin kafin Yohanna yă zo,
14 kuma idan za ku yarda da saƙonsu, Yohanna shi ne wanda aka yi magana a kai saˈad da aka ce Iliya zai zo.
15 Bari mai kunnen ji, yă ji.
16 “Amma da me zan kwatanta wannan zamani? Kamar yara ne da suke zaune a kasuwa suna kiran abokan wasansu suna cewa,
17 “ ‘Mun hura muku sarewa, kun ƙi ku yi rawa! Mun rera waƙar mutuwa, kun ƙi ku yi kuka!’
18 “Gama da Yohanna ya zo bai cika ci da sha ba, sai suka ce, ‘Yana da aljanu.’
19 Da Ɗan Mutum ya zo yana ci yana sha, suka ce, ‘Ga mai yawan ci da sha, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’ Duk da haka, ana gane hikimar Allah a ayyukanta.”
20 Sai ya fara tsawata wa garuruwan, inda ya yi yawancin ayyukansa na ban mamaki, gama mutanen nan ba su tuba ba.
21 “Kaitonki, Korasin! Kaitonki, Betsaida! Gama da a ce ayyukan ban mamakin da aka yi a cikinku ne, aka yi a Taya da Sidon, da sun tuba tun tuni, sun sa tsumma da toka a jikinsu.
22 Amma ina gaya muku, a Ranar Shariˈa za a fi jin tausayin mutanen Taya da Sidon fiye da ku.
23 Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani ɗaukaka ki za a yi zuwa sama ne? A ina! Ƙasƙantar da ke za a yi har wurin zaman matattu. Ayyukan ban mamakin da aka yi a cikinki, da su ne aka yi a Sodom, da tana nan har wa yau.
24 Amma ina gaya muku, a Ranar Shariˈa za a fi jin tausayin mutanen Sodom fiye da ke.”
25 A wannan lokaci ne Yesu ya ce, “Na gode maka, ya Uba, Ubangijin sama da duniya, saboda ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana wa ˈyan yara.
26 Haka ne ya Uba, gama wannan shi ne abin da ya yi maka kyau.
27 “Ubana ya ba ni dukan abu, kuma ba wanda ya san Ɗan sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban sai Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so yă bayyana masa.
28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji, kuma kuna fama da kaya masu nauyi a kanku, zan ba ku hutawa.
29 Ku miƙa kanku ga umarnaina kamar yadda saniya takan miƙa wuyanta ga gungumen noma, ku kuma koya daga wurina, domin ni mai tawaliˈu ne, mai sauƙin kai, kuma za ku sami hutu a zuciyarku.
30 Gama gungumena yana da sauƙi, umarnaina kuma ba nauyi.”