Hausa Bible
Markus 5
1 Yesu da almajiransa suka kai hayin tekun da yake a yankin Garasinawa.
2 Da saukar Yesu daga jirgin ruwan, nan da nan sai ga wani mai ƙazamin ruhu, ya fito daga inda ake binne mutane, ya tarye shi.
3 Mutumin kuwa, a wurin binne mutane ne yake kwana. Ba mai iya ɗaure shi kuma, ko da sarƙa ma.
4 Don dā an sha ɗaure hannuwansa da ƙafafunsa da sarƙa, amma yakan tsintsinke su. Har ba wanda yake da ƙarfi yă bi da shi.
5 Kullum kuwa dare da rana yana yawo cikin inda ake binne mutane, da kan duwatsu, yana ihu, yana tsattsage jikinsa da duwatsu.
6 Da ya ga Yesu daga nesa, sai ya tashi da gudu ya durƙusa a gabansa.
7 Ya yi ihu da ƙarfi ya ce, “Ina ruwanka da ni, Yesu Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Na roƙe ka da sunan Allah, kada ka ba ni wahala.”
8 Ya faɗa haka ne don Yesu ya ce masa, “Rabu da mutumin nan, kai ƙazamin ruhu!”
9 Yesu ya tambaye shi ya ce, “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa ya ce, “Sunana Tuli ne, gama muna da yawa.”
10 Sai ya roƙi Yesu sosai kada yă kore su daga yankin.
11 Kusa da wurin nan kuwa akwai wani babban garken aladu da yake kiwo a gangaren tudun.
12 Ƙazaman ruhohin nan suka roƙi Yesu suka ce, “Ka sa mu je wurin aladun nan, mu shiga cikinsu.”
13 Yesu kuwa ya yarda. Sai ƙazaman ruhohin suka fita suka shiga cikin aladun. Garken kuwa alade wajen dubu biyu ne, suka kuwa tashi a guje, suka gangara suka fāɗi cikin tekun, suka halaka a ruwa.
14 Da ganin haka, makiyayan aladun suka gudu suka ba da labarin a garinsu da karkararsu. Mutane suka fito domin su ga abin da ya faru.
15 Da suka zo wurin Yesu suka ga mutumin da dā yake cike da aljanu, yana zaune da riguna a jikinsa, yana cikin hankalinsa kuma, sai suka ji tsoro.
16 Waɗanda aka yi abin a idonsu kuwa, suka yi ta ba da labarin abin da ya faru da mai aljanun da kuma aladun.
17 Sai mutanen suka fara roƙi Yesu yă bar yankinsu.
18 Yesu yana shiga cikin jirgin ruwa ke nan, sai wanda dā yake da aljanun nan ya roƙe shi yă yarda masa yă tafi tare da shi.
19 Amma Yesu bai yarda masa ba. Ya ce masa, “Tafi gida wurin ˈyanˈuwanka, ka faɗa musu irin manyan abubuwan da Ubangiji ya yi maka, da kuma yadda ya ji tausayinka.”
20 Sai mutumin ya tafi, ya fara baza labari a yankin Garuruwa Goma a kan irin manyan abubuwan da Yesu ya yi masa. Dukan mutane kuwa suka yi ta mamaki.
21 Da Yesu ya sāke hayewa zuwa wancan gefen tekun cikin jirgin ruwa, sai mutane da yawa suka taru wurinsa. Tun yana nan a bakin tekun,
22 sai ɗaya daga cikin shugabannin majamiˈa mai suna Yayirus, ya zo wurin. Da ganin Yesu kuwa, ya fāɗi a gabansa,
23 ya yi ta roƙonsa, yana cewa, “ˈYata ƙarama tana bakin mutuwa. Ina roƙonka ka zo ka taɓa ta domin ta warke ta rayu.”
24 Sai Yesu ya tafi tare da shi. Mutane da yawa suka bi shi har suna matsa shi.
25 Akwai wata mace a wurin wadda ta yi shekara goma sha biyu tana zub da jini.
26 Ta kuma sha wahala sosai a hannun masu magani da yawa har ta kashe dukan abin da take da shi. Amma maimako ta sami sauƙi, sai ciwon ya yi ta ƙaruwa.
27 Dā ma, ta ji labarin Yesu, domin haka, ta shiga cikin mutane ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa,
28 tana tunani a ranta cewa, “Ko da rigarsa ma na taɓa kawai, zan warke.”
29 Nan da nan zubar jininta ta tsaya, ta kuma ji a jikinta an warkar da ita.
30 Nan da nan Yesu ya ji wani iko ya fita daga gare shi, sai ya juya a cikin taron, ya ce, “Wa ya taɓa rigata?”
31 Sai almajiransa suka ce masa, “Haba! Kana ganin mutane suna matsarka haka, ka ce, ‘Wa ya taɓa ni?’ ”
32 Amma Yesu ya dudduba domin ya ga wanda ya yi wannan abin.
33 Matar kuwa da ta san abin da aka yi mata, ta zo cikin tsoro da rawar jiki, ta fāɗi a gabansa, ta faɗa masa dukan gaskiya.
34 Sai ya ce mata, “ˈYata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kin warke daga ciwonki.”
35 Yana cikin magana ke nan, sai ga waɗansu mutane daga gidan Yayirus suka ce, “Ai, ˈyarka ta mutu! Me ya sa kana ta damun malamin?”
36 Amma Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, ya ce wa shugaban majamiˈa, “Kada ka ji tsoro, kai dai ka ba da gaskiya.”
37 Bai bar kowa yă bi shi ba sai Bitrus, da Yakub, da kuma Yohanna ɗanˈuwan Yakub.
38 Da suka kai gidan Yayirus, Yesu ya ga mutane sun rikice suna ta kuka suna ihu.
39 Ya shiga ciki, ya ce musu, “Don me kuke kuka kuna ihu haka? Ai, yarinyar ba ta mutu ba, barci take yi.”
40 Sai suka yi masa dariyar reni. Amma ya fitar da dukan mutane waje, ya ɗauki baban yarinyar da mamarta, da kuma almajiransa waɗanda suke tare da shi, ya shiga inda yarinyar take.
41 Ya kama hannunta, ya ce mata, “ Talita kumi,” wato “Yarinya, ki tashi.”
42 Nan da nan yarinyar ta tashi ta yi tafiya. Shekarunta kuwa goma sha biyu ne. Wannan kuwa ya sa suka yi mamaki sosai.
43 Amma Yesu ya ja musu kunne sosai cewa kada kowa yă ji wannan labari. Ya kuma ce musu su ba ta abinci.