Skip to content

Hausa Bible

Markus 4

1 Yesu ya kuma fara koyarwa a bakin Tekun Galili. Taron mutane da yawa sosai suka taru kewaye da shi, har sai da ya shiga jirgin ruwa ya zauna a cikinsa a kan tekun. Taron mutanen kuwa suna a bakin tekun a kan tudu.

2 Sai ya koya musu abubuwa da yawa ta wurin misalai. Ya ce musu,

3 “Ku kasa kunne! Wani manomi ya tafi gonarsa domin yă yi shuka.

4 Yana cikin yafa irin ke nan, sai waɗansu iri suka fāɗi a kan hanya, sai tsuntsaye suka zo suka cinye su.

5 Waɗansu iri kuma suka fāɗi a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa sosai. Sai suka tsiro da sauri saboda ƙasar wurin ba ta da zurfi.

6 Da rana ta yi zafi, sai ta ƙone su har suka bushe, don ba su da saiwa sosai.

7 Waɗansu kuma suka fāɗi a cikin ƙaya, sai ƙayar ta tashi ta sha ƙarfinsu har ba su yi tsaba ba.

8 Waɗansu kuwa suka fāɗi a ƙasa mai kyau. Suka tsira suka yi girma, suka yi kai, waɗansu tsaba talatin-talatin, waɗansu sittin-sittin, waɗansu har ma ɗari-ɗari.”

9 Saˈan nan ya ce, “Duk mai kunnen ji, bari yă ji.”

10 Lokacin da Yesu yake zaune shi kaɗai, sai almajiransa sha biyu da waɗansu masu binsa suka roƙe shi ya gaya musu abin da misalin nan yake nufi.

11 Sai ya ce musu, “Ku kam, an yarda muku ku san asirin mulkin Allah. Amma waɗanda ba sa cikinku, kome sai cikin misalai.

12 Shi ya sa, “ ‘Za su yi ta dubawa, amma ba za su taɓa gani ba, Su yi ta ji kuma, amma ba za su gane ba. Domin kada su gane, su tuba a kuma yafe musu.’ ”

13 Sai Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku gane misalin nan ba? To, yaya za ku gane sauran?

14 Mai yafa irin nan fa kalmar Allah yake yafawa.

15 Irin da ya fāɗi a hanya, shi ne kwatancin mutanen da suka ji kalmar Allah. Amma da zarar suka ji, nan da nan sai Shaiɗan ya zo ya ɗauki kalmar da aka shuka a zuciyarsu.

16 Haka kuma irin da ya fāɗi a wurin da yake da duwatsu, shi ne kwatancin waɗanda da zarar suka ji kalmar sai suka karɓa da farin ciki.

17 Amma tun da ba su da tushe, ba su daɗe sosai ba. Saˈad da azaba ko tsanani ya tashi saboda wannan kalmar Allah, nan da nan sai su ja da baya.

18 Irin da ya fāɗi a wurin da yake da ƙaya, shi ne kwatancin mutanen da suka ji kalmar,

19 amma damuwar duniya, da son arziki, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, suka shiga suka hana kalmar girma, har ta zama ba ta da amfani.

20 Irin da ya fāɗi a wurin da yake da kyau kuwa, shi ne kwatancin waɗanda suka ji kalmar Allah, suka karɓa, suka kuma yi amfani da ita, har suka yi riba waɗansu talatin-talatin, waɗansu sittin-sittin, waɗansu ma har ɗari-ɗari.”

21 Yesu ya ci gaba da cewa, “Ko kukan kawo fitila ku rufe ta da kwano ne? Ko kuma kukan ajiye ta a ƙarƙashin gado ne? Ba kukan ajiye fitila a sanda mai riƙe fitilu ba?

22 Ba abin da yake a ɓoye yanzu, wanda ba za a bayyana ba. Ba abin da yake asiri kuma, wanda ba za a tone shi ba.

23 Duk mai kunnen ji, bari yă ji.”

24 Ya kuma ce musu, “Ku ji da kyau fa! Da mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a ƙara.

25 Duk wanda yake da abu, za a ƙara masa, wanda ba shi da abu kuma, ko ɗan abin da yake da shi ma za a karɓa daga gare shi.”

26 Yesu ya kuma ce, “Ga yadda mulkin Allah yake. Yana nan kamar yadda wanda ya yafa iri a gonarsa.

27 A kwana a tashi har irin ya tsira ya yi girma, mutumin bai ma san yadda aka yi ba.

28 Ƙasa tana ba da amfani da kanta, da farko takan fitar da kara, saˈan nan kai, sai kuma kan ya fitar da ƙwaya.

29 Saˈad da amfani ya nuna, sai yă sa lauje yă yanka, domin lokacin girbi ya zo.”

30 Yesu ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta mulkin Allah? Ko kuwa da wane misali ne za mu nuna yadda yake?

31 Yana kama da ƙwaya iri na mastad wadda irinta ta fi ƙanƙanta a dukan irin da ake shukawa a ƙasa.

32 Duk da haka, in an shuka ta, takan yi girma ta fi duk sauran kayan lambu, takan yi manyan rassa, har tsuntsaye su iya sauka a inuwarta.”

33 Da irin waɗannan misalai da yawa Yesu ya faɗa musu kalmar Allah, daidai iyakar ganewarsu.

34 Bai faɗa musu kome ba, sai tare da misali. Amma lokacin da yake tare da almajiransa su kaɗai, yakan faɗa musu kome da kome a fili.

35 A ranar nan, da rana ta kusan fāɗuwa, Yesu ya ce wa almajiransa, “Mu haye zuwa wancan gefen tekun.”

36 Suka bar taron mutane, suka tafi da shi yadda yake a cikin jirgin da yake zaune a ciki. Akwai waɗansu jirage kuma tare da su.

37 Sai babban hadari mai iska ya taso, har yana tā da ruwan tekun sama yana bubbuga jirgin. Ruwa kuwa yana shiga cikin jirgin har jirgin ya kusan cika da ruwa.

38 Yesu kuwa yana can bayan jirgin yana barci kansa a matashi. Almajiransa suka tashe shi, suka ce, “Malam, za mu halaka, ba ka damu ba ko?”

39 Sai Yesu ya farka, ya tsawata wa iskar, ya kuma ce wa ruwan tekun, “Natsu! Ka yi shiru!” Sai iskar ta daina, wuri duk ya yi tsit.

40 Ya ce wa almajiransa, “Me ya sa kuka ji tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?”

41 Sai suka ji tsoro sosai, suka ce wa juna, “Wane ne wannan? Har iska da ruwan teku ma suna yi masa biyayya!”

Open Bible reader