Skip to content

Hausa Bible

Yahaya 2

1 A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mamar Yesu kuwa tana wurin auren.

2 An gayyaci Yesu da almajiransa ma a auren.

3 Da ruwan inabi ya ƙāre, sai mamar Yesu ta ce masa, “Ruwan inabinsu ya ƙāre.”

4 Yesu ya amsa mata ya ce, “Mama, me ya sa kika zo wurina? Ai, lokacina bai yi ba tukuna.”

5 Sai mamar Yesu ta ce wa masu hidimar, “Duk abin da Yesu ya ce ku yi, sai ku yi.”

6 Yahudawa kuwa suna da alˈadar tsabtacewa, saboda haka akwai randuna shida waɗanda da dutse ne aka gina su aka ajiye a wurin, kowacce tana cin wajen lita ɗari na ruwa.

7 Sai Yesu ya ce wa masu hidimar, “Ku cika randunan nan da ruwa.” Sai suka ciccika su fal.

8 Saˈan nan ya ce musu, “To, yanzu ku ɗiba, ku kai wa uban bikin.” Sai suka ɗiba ruwan suka kai masa.

9 Ruwan kuwa ya canja ya zama ruwan inabi, sai uban bikin ya sha kaɗan. Shi kuwa bai san inda aka samo ruwan inabin ba, amma masu hidimar da suka ɗebo ruwan sun sani. Sai ya kira angon suka tsaya a gefe,

10 saˈan nan ya ce masa, “Ai, kowa yakan fara ba da kyakkyawan ruwan inabi tukuna, bayan da mutane suka sha da yawa, saˈan nan kuma ya kawo wanda bai kai na farin kyau ba. Amma kai ka ɓoye kyakkyawan ruwan inabin sai yanzu!”

11 Wannan ita ce alamar ban mamaki ta farko wadda Yesu ya yi, ya kuwa yi wannan ne a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuma suka ba da gaskiya gare shi.

12 Bayan haka sai Yesu ya gangara zuwa Kafarnahum, da shi da mamarsa da ˈyanˈuwansa da kuma almajiransa. Suka yi zama na ˈyan kwanaki a can.

13 Da lokacin Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, sai Yesu ya tafi Urushalima.

14 A cikin filin Haikalin, ya sami mutane suna sayar da shanu, da tumaki, da tattabaru, da kuma masu canjin kuɗi suna zaune a teburansu.

15 Sai Yesu ya tuƙa bulala da igiya, ya kore su duka daga Haikalin, har da tumakin da shanun. Ya kuma tutture teburan masu canjin, ya warwatsar da dukan kuɗaɗensu.

16 Sai Yesu ya ce wa mutanen da suke sayar da tattabarun, “Ku fitar da waɗannan daga nan! Kada ku mai da Gidan Ubana kasuwa.”

17 Da wannan ya faru, sai almajiransa suka tuna da abin da aka rubuta a Maganar Allah cewa, “Kishi na ƙaunar da nake yi wa Gidanka tana ƙunani kamar wuta.”

18 Sai shugabannin Yahudawa suka tambayi Yesu suka ce, “To, wace alamar ban mamaki ce za ka yi mana wadda za ta nuna cewa kana da ikon yin dukan waɗannan abubuwa?”

19 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe wannan Haikali, ni kuwa zan tā da shi a cikin kwana uku.”

20 Sai suka tambaye shi suka ce, “Ya ɗauki shekara arbaˈin da shida ana kan ginin wannan Haikali! Kai kuma ka ce za ka tā da shi a cikin kwana uku?”

21 Amma haikalin da Yesu ya yi magana a kai, jikinsa ne.

22 Bayan da aka tā da Yesu daga matattu, sai almajiransa suka tuna da wannan abin da Yesu ya faɗa, suka kuma ba da gaskiya ga Rubutacciyar Maganar Allah, da kuma maganar da Yesu ya faɗa.

23 A lokacin da Yesu yana Urushalima domin Bikin Ƙetarewa, mutane da yawa sun ba da gaskiya gare shi domin alamun ban mamaki waɗanda suka gani ya yi.

24 Amma Yesu bai yarda da su ba, domin ya san su duka sosai.

25 Gama ba ya bukatar wani yă shaida wani abu game da mutum, saboda ya san abin da yake a zuciyar ɗan Adam.

Open Bible reader