Skip to content

Hausa Bible

Yahaya 17

1 Bayan da Yesu ya faɗa waɗannan abubuwa sai ya ɗaga kansa ya dubi sama ya yi adduˈa ya ce, “Ya Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka don shi ma yă ɗaukaka ka.

2 Gama ka ba Ɗan iko a kan dukan mutane, domin yă ba da rai na har abada ga waɗanda ka ba shi.

3 Rai na har abada kuwa shi ne, mutane su san ka, kai da kake Allah Makaɗaici na gaskiya, su kuma san Yesu Almasihu wanda ka aiko.

4 Na ɗaukaka ka a duniya ta wurin cika dukan aikin da ka ba ni in yi.

5 Yanzu kuma, ya Uba, ka ɗaukaka ni da ɗaukakar nan da nake da ita a gabanka tun kafin halittar duniya.”

6 “Na riga na bayyana yadda kake ga mutanen da ka ba ni a nan duniya. Tun dā ma su naka ne, amma ka ba ni su, sun kuma yi biyayya da kalmarka.

7 Yanzu kuwa sun sani cewa duk abin da ka ba ni daga gare ka yake.

8 Gama kalmar da ka faɗa mini na faɗa musu, sun kuwa karɓa. Sun san hakika daga wurinka ne na fito, sun kuma ba da gaskiya kai ne ka aiko ni.

9 Ina roƙo ne dominsu. Ba domin mutanen duniya nake yin roƙon ba, amma domin mutanen da ka ba ni, domin su naka ne.

10 Duk abin da nake da shi naka ne, kuma duk abin da kake da shi nawa ne. An kuma bayyana ɗaukakata ta wurinsu.

11 Ina zuwa wurinka. Ba zan zauna a duniya kuma ba, amma su suna cikin duniya tukuna. Ya Uba Mai Tsarki, ka lura da su da ikon sunanka, wato sunan da ka ba ni, domin su zama ɗaya, kamar dai yadda nake da kai.

12 Lokacin da nake tare da su, na lura da su da ikon sunanka, sunan da kai ka ba ni. Na kiyaye su, kuma ba wanda ya ɓace sai dai ɗayansu nan kaɗai wanda yake ɗan halaka, domin a cika annabcin Rubutacciyar Maganar Allah.

13 Yanzu ina zuwa wurinka. Amma ina roƙon waɗannan abubuwa ne tun ina duniya domin waɗannan masu bina su sami farin cikina cikakke a zukatansu.

14 Na faɗa musu kalmarka. Duniya kuma ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.

15 Ba ina roƙonka cewa ka ɗauke su daga duniya ba, amma ina roƙo ne ka tsare su daga Mugun nan.

16 Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.

17 Ka tsarkake su ta wurin gaskiya, gama kalmarka kuwa ita ce gaskiya.

18 Na aike su cikin duniya, kamar yadda kai ma ka aiko ni.

19 Saboda su ne nake tsarkake kaina domin su ma a tsarkake su da gaske.”

20 “Ba kuwa waɗannan kaɗai nake roƙa wa ba, amma ina roƙo kuma domin dukan waɗanda za su ba da gaskiya bisa ga maganarsu.

21 Ya Uba, ina roƙo domin dukansu su zama ɗaya. Kamar yadda kake cikina, ni kuma ina cikinka, ina roƙo bari su ma su kasance a cikinmu, domin mutanen duniya su ba da gaskiya cewa kai ne ka aiko ni.

22 Ni na ba mutanen nan ɗaukakar da kai ka ba ni, domin su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya.

23 Zan zauna a cikinsu, kai kuma a cikina, domin su zama ɗaya sosai, domin mutanen su sani kai ne ka aiko ni, su kuma sani ka ƙaunace su kamar yadda ka ƙaunace ni.

24 “Ya Uba, ina so waɗannan mutanen da ka ba ni su zauna tare da ni inda nake. Ina so su ga ɗaukakarka, wadda ka ba ni saboda kana ƙaunata kafin a halicci duniya.

25 Ya Uba, Mai Adalci, mutanen duniya ba su san ka ba, amma ni kam na san ka, waɗannan mutane kuma sun sani cewa kai ne ka aiko ni.

26 Na sanar musu yadda kake, zan kuma ci gaba da sanar musu, domin ƙaunar da kake yi mini ta kasance a cikinsu, ni kuma in kasance a cikinsu.”

Open Bible reader