Skip to content

Hausa Bible

Yahaya 15

1 “Ni ne itacen inabi na ainihi, Ubana kuwa shi ne manomin.

2 Kowane reshe a cikina da ba ya ba da ˈyaˈya, sai yă yanke shi. Kowane reshe mai yin ˈyaˈya kuwa yakan ƙara gyara shi domin yă ƙara haifuwa.

3 Ko yanzu ma kuna da tsabta saboda maganar da na faɗa muku.

4 Ku zauna a cikina, ni kuma a cikinku. Kamar yadda reshen itacen inabi ba ya iya ba da ˈyaˈya da kansa, sai ko yă kasance haɗe da itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun kasance haɗe da ni.

5 “Ni ne itacen inabi, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, shi ne mai yin ˈyaˈya da yawa. Gama in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba.

6 Duk wanda bai zauna a cikina ba, yana kama da reshen da aka jefar da shi yă bushe. Mutane sukan tattara irinsu ne su jefa a wuta, a ƙone su.

7 In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku.

8 Ku haifar da halin rayuwa mai kyau wadda za ta nuna cewa ku almajiraina ne, kamar itacen da ya haifi ˈyaˈya masu kyau, gama wannan ne yake ɗaukaka Ubana.

9 Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma ina ƙaunarku. To, ku zauna a cikin ƙaunar da nake nuna muku.

10 Ni na bi umarnan Ubana, na kuma zauna a cikin ƙaunarsa. Haka ku kuma, in kun bi umarnaina za ku zauna a cikin ƙaunata.

11 “Na gaya muku haka domin farin cikina yă kasance a cikinku, farin cikinku kuma yă zama cikakke.

12 Umarnina, shi ne, ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.

13 Ba ƙaunar da ta fi wannan, wato mutum yă ba da ransa saboda abokansa.

14 Ku abokaina ne in kun yi abin da na ce ku yi.

15 Ba zan ƙara ce da ku bayi kuma ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. Amma ina ce da ku abokai gama na gaya muku dukan abin da na ji daga wurin Ubana.

16 Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na kuma sa ku ku je ku haifar da halayen rayuwa mai kyau kamar itace mai haifar da ˈyaˈya, halayen da za su dawwama. Saˈan nan Uba zai ba ku dukan abin da kuka roƙa a cikin sunana.

17 Umarnin da na ba ku shi ne ku ƙaunaci juna.”

18 “Idan dai duniya ta ƙi ku, ku sani cewa ta ƙi ni kafin ta ƙi ku.

19 Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.

20 Ku tuna da abin da na faɗa muku cewa, ‘Bawa ba ya fin maigidansa.’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da maganata, da za su yi biyayya da taku ku ma.

21 Za su yi muku dukan waɗannan ne saboda sunana, don ba su san wanda ya aiko ni ba.

22 Da ba domin na zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu kam, ba su da wata hujja a kan zunubinsu.

23 Wanda ya ƙi ni ya ƙi Ubana ma.

24 Na yi ayyuka da yawa a cikinsu waɗanda ba wanda ya taɓa yi. Da a ce ban yi ayyukan nan ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun ga abin da na yi, amma duk da haka sun ƙi ni, sun kuma ƙi Ubana.

25 Wannan ya faru ne kuwa domin a cika maganar da take a rubuce a Koyarwarsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’

26 “Zan sa Mai Taimako yă zo wurinku daga wurin Uba. Shi ne Ruhu na gaskiya, mai fitowa daga wurin Uba, shi ne zai yi shaida a kaina.

27 Ku ma shaidu ne, domin tun farko kuna tare da ni.

Open Bible reader