Hausa Bible
Yakubu 3
1 ˈYanˈuwana, kada da yawa a cikinku ku zama masu koyarwa, domin kun san cewa mu da muke koyarwa za a yi mana shariˈa mafi tsanani fiye da ta sauran mutane.
2 Gama dukanmu mukan yi kuskure da yawa. Idan kuwa wani ba ya kuskure a maganarsa, to, lallai shi cikakke ne, mai iya lura da jikinsa gaba ɗaya.
3 Mukan sa wa doki linzami a baki domin yă yi biyayya da mu. Ta haka mukan iya bi da shi zuwa inda muke so.
4 Ku kuma duba jiragen ruwa ku gane. Ko da yake su manya ne, kuma iska mai ƙarfi ce take tura su, duk da haka da ɗan ƙaramin sandan tuƙi ne mai tuƙin jirgin yakan iya juya jirgin zuwa koˈina da yake so.
5 Haka ma harshen mutum yake. Ko da yake shi ɗan ƙarami ne cikin gaɓoɓin jiki duk da haka yana cike manyan taƙama! Ku dubi yadda ƙanƙanuwar wuta takan iya ƙone daji ƙurmus!
6 Ai, harshen mutum fa wuta ne, duniya ne ta mugunta cikin gaɓoɓin jikinmu! Harshe yana kuma ɓata mutum gaba ɗaya. Yakan zuga dukan rai yă tafasa, harshen kansa ma ake kunna shi da wuta daga Gidan Wuta.
7 Ɗan Adam yana iya shan kan kowace dabba, har ma ya riga ya sha kan dabbobi iri-iri, wato, namomin daji, da tsuntsaye, da dangin macizai da ƙadangaru, da kuma halitta cikin teku.
8 Amma ba wanda ya taɓa iya shan kan harshensa. Harshe mugun abu ne marar hutu, kuma yana cike da dafi mai halakarwa.
9 Da shi ake yabon Ubangijinmu wanda yake Ubanmu, da shi kuma ake zagin mutane waɗanda Allah ya yi cikin kamanninsa.
10 Da baki ake yabo, da shi kuma ake zagi. Haba, ˈyanˈuwana! Ai, bai kamata yă kasance haka ba.
11 Ko rijiya ɗaya za ta iya ba da ruwa mai daɗi, ta kuma ba da ruwa mai gishiri?
12 ˈYanˈuwana, itacen ɓaure zai iya haifar ˈyaˈyan zaitun, ko itacen inabi zai iya haifar ˈyaˈyan ɓaure? Ta haka kuma rijiya mai ba da ruwan gishiri ba za ta ba da ruwa mai daɗi ba.
13 Wane ne mai hikima da ganewa a cikinku? Sai yă nuna ta ta wurin yin rayuwa mai kyau, da kuma aiki mai kyan da yake yi cikin sauƙin kai wanda yake fitowa daga cikin hikima.
14 Amma idan a zuciyarku kuna da tsananin kishi da kuma sonkai, to, ku bar yin taƙama da musūn sanin gaskiya.
15 Wannan hikima ba irin da take saukowa daga sama ba ce, amma ta duniya ce. Kuma ba ta ruhaniya ba ce, amma ta Shaiɗan ce.
16 Gama duk inda akwai kishi da sonkai, to, akwai kowace irin rikicewa da mugunta a wurin.
17 Amma hikimar da take daga wurin Allah, da farko dai mai tsarki ce, kuma mai kawo salama ce, mai hankali ce, mai sauƙin kai ce, mai yawan tausayi ce, mai yawan alheri ce. Ba ta nuna bambanci ko munafunci.
18 Daga ƙwayar salama wadda masu kawo salama suke shukawa, akan girbe adalci.