Skip to content

Hausa Bible

Ibraniyawa 5

1 Akan zaɓi kowane babban firist daga cikin mutane ne domin yă yi hidima a madadin sauran mutane a kan alˈamuran Allah. Shi ne mai miƙa baye-baye da hadayu saboda zunubai.

2 Tun da yake shi da kansa yana da nasa kāsawa, yana iya yă bi da masu rashin sani da masu kauce hanya a hankali.

3 Saboda kāsawar nan tasa, ya zama tilas yă miƙa hadayu, ba saboda zunuban jamaˈa kaɗai ba, amma saboda nasa zunuban ma.

4 Ba wanda zai zaɓa wa kansa aikin nan mai daraja. Mutum yakan zama babban firist ne bisa ga kiran Allah, kamar yadda aka kira Haruna.

5 Haka kuma Almasihu bai ɗaukaka kansa yă zama Babban Firist ba. A maimakon haka, Allah ya ce masa, “Kai Ɗana ne, yau na zama Ubanka.”

6 Ya sāke yin magana a wani wuri ya ce, “Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”

7 A lokacin da Yesu yake cikin duniya, ya miƙa adduˈoˈi da roƙe-roƙe tare da kuka mai tsanani da hawaye. Ya kuwa miƙa adduˈoˈinsa ga Allah wanda yana iya cece shi daga mutuwa. Domin shi mai biyayya ne cikin tsoron Allah, Allah ya karɓi roƙonsa.

8 Ko da yake Yesu Ɗan Allah ne, ya koyi yin biyayya ta hanyar azabar da ya sha.

9 Bayan da ya kai ga zaman cikakke, sai ya zama tushen ceto na har abada ga duk masu yi masa biyayya.

10 Ta haka kuma Allah ya naɗa shi Babban Firist bisa ga tsarin Melkizedek.

11 Muna da abubuwa da yawa da muke so mu faɗa game da wannan zance, amma yana da wuya mu bayyana muku, gama ba ku da saurin ganewa.

12 Ko da yake a yanzu kam ya kamata da kun zama masu koyarwa, amma har yanzu kuna bukatar wani yă sāke maimaita muku koyarwa mai sauƙi ta kalmar Allah. Ba ku isa cin abinci mai kauri ba, sai shan nono kawai!

13 Duk wanda nono ne abincinsa, shi jariri ne, bai kuwa san kome game da koyarwa ta adalci ba.

14 Amma abinci mai kauri shi ne na waɗanda suka yi girma. Waɗannan su ne masu ƙoƙarin yin amfani da hankalinsu kullum, har ma suna iya bambanta nagarta da mugunta.

Open Bible reader