Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 11

1 Manzanni da sauran ˈyanˈuwan da suke a koˈina a yankin Yahudiya suka ji cewa waɗanda ba Yahudawa ba ma sun karɓi kalmar Allah.

2 Da Bitrus ya je Urushalima, waɗansu manyan Yahudawa masu bi, waɗanda suka tsaya a kan alˈadarsu ta kaciya, suka yi masa faɗa.

3 Suka ce, “Don me ka je wurin arna marasa kaciya, har ka ci abinci tare da su?”

4 Sai Bitrus ya fara yi musu bayani dalla-dalla cewa,

5 “Ina birnin Yoffa ina adduˈa, sai na ga ruˈuya, na ga wani abu yana saukowa kamar babban mayafi, an sauko da shi daga sama ta kwanarsa huɗu, har ya iso kusa da ni.

6 Da na dube shi sosai, na ga dabbobi masu ƙafa huɗu, da namomin daji, da dangin macizai da ƙadangaru, da kuma tsuntsaye a ciki.

7 Na kuma ji wata murya ta ce mini, ‘Bitrus, ka tashi, ka yanka ka ci.’

8 Amma na ce, ‘Sam! Ubangiji, ba wani abin ƙazanta ko marar tsabta wanda ya taɓa shiga bakina.’

9 Sai murya ta amsa daga sama ta yi magana sau na biyu, ta ce, ‘Abin da Allah ya tsabtace, kada ka ce da shi mai ƙazanta.’

10 An yi wannan sau uku, saˈan nan aka ɗauki abin zuwa sama.

11 A daidai wannan lokaci, sai ga mutum uku sun tsaya a bakin ƙofar gidan da nake, an aiko su wurina ne daga Kaisariya.

12 Sai Ruhu ya ce mini in bi su, kada in nuna bambanci tsakanin su da mu. ˈYanˈuwan nan shida kuma suka rako ni, har muka shiga gidan mutumin nan.

13 Sai ya faɗa mana yadda ya ga malaˈika ya tsaya a gidansa, yana cewa, ‘Ka aika zuwa Yoffa a kirawo Siman, wanda ake ce da shi Bitrus.

14 Shi zai kawo maka saƙon da za ka sami ceto ta wurinsa, kai da mutanen gidanka duka.’

15 Na fara yi musu magana ke nan, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu, daidai yadda ya sauko mana da farko.

16 Sai na tuna da kalmar Ubangiji, yadda ya ce, ‘Yohanna dai ya yi baftisma da ruwa, amma ku da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.’

17 To, da yake Allah ya yi musu baiwa daidai da wadda ya yi mana, saˈad da muka ba da gaskiya ga Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni in hana Allah!”

18 Da Yahudawa masu bi suka ji haka, suka rasa abin da za su ce, sai suka yabi Allah suna cewa, “Ashe, har waɗanda ba Yahudawa ba ma Allah ya yi musu hanyar tuba da samun rai.”

19 To, masu bi suka warwatse saboda tsananin nan da ya tashi saboda kashewar Istifanus. Waɗansu suka tafi har zuwa ƙasar Finikiya da Sayifurus, da birnin Antakiya. Suna waˈazin kalmar Allah, amma ga Yahudawa kaɗai.

20 Amma akwai waɗansu masu bi daga Sayifurus da Sayirin, waɗanda suka tafi Antakiya suka yi wa Helenawa magana, suna ba su labari mai daɗi na Ubangiji Yesu.

21 Hannun ikon Ubangiji kuwa yana tare da su, har mutane da yawa suka tuba, suka juyo wurin Ubangiji.

22 Labarin abin da ya faru a Antakiya kuwa ya kai kunnen jamaˈar masu bin da take a Urushalima. Jamaˈar masu bi kuma ta aika Barnaba zuwa can Antakiya.

23 Da ya zo, ya kuma ga alherin da Allah ya yi musu, ya yi farin ciki, ya gargaɗe su duka su tsaya da bangaskiya cikin Ubangiji da dukan zuciyarsu.

24 Barnaba kuwa mutumin kirki ne, cike da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya. Sai mutane masu yawan gaske suka juyo zuwa wurin Ubangiji.

25 Daga nan sai Barnaba ya tafi Tarsus domin yă nemi Shawulu.

26 Da ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antakiya. Shekara ɗaya cif, suna taruwa da jamaˈar masu bi, suna koya wa mutane masu yawan gaske. A Antakiya ne aka fara kiran masu bin Almasihu da suna Kirista.

27 To, a wannan lokaci, waɗansu annabawa suka zo Antakiya daga Urushalima.

28 Ɗaya daga cikinsu, mai suna Agabus, ya tashi tsaye, ya yi magana da ikon Ruhu cewa za a yi wata babbar yunwa a duniya duka. Wannan kuwa ya faru a zamanin Kalaudiyus.

29 Sai almajiran suka yanke shawara cewa su aika wa ˈyanˈuwan da suke cikin yankin Yahudiya taimako, kowa daidai ƙarfinsa.

30 Haka kuwa suka yi, suka aika wa dattawan jamaˈar masu bi a yankin Yahuda taimakon ta hannun Barnaba da Shawulu.

Open Bible reader