Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 1

1 Ya Tiyofilus, a rubutuna na farko na rubuta maka game da dukan abubuwan da Yesu ya fara yi, da kuma waɗanda ya fara koyarwa,

2 har zuwa ranar da aka ɗauke shi zuwa sama. Kafin a ɗauke shi zuwa sama, ya yi wa manzannin da ya zaɓa umarni ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

3 Bayan mutuwarsa, ya bayyana gare su da rai, har ya tabbatar musu maganar tashinsa ta wajen ayyuka iri-iri. Ya yi kwana arbaˈin, yana magana a kan alˈamuran mulkin Allah.

4 A saˈad da yake tare da su tukuna, ya umarce su cewa, “Kada ku bar Urushalima. Ku jira sai alkawarin da Ubana ya yi ya cika tukuna, wanda na faɗa muku da bakina, cewa,

5 Yohanna ya yi wa mutane baftisma da ruwa, amma nan da ˈyan kwanaki, za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”

6 Da manzannin suka taru, sai suka tambayi Yesu suka ce, “Ubangiji, yanzu ne za ka mayar wa Israˈila mulki?”

7 Yesu ya ce musu, “Uba kaɗai yake da ikon shirya lokatai da zamanai, amma ku ba a ba ku damar sanin waɗannan ba.

8 Amma za ku sami iko saˈad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku zama shaiduna a Urushalima, da cikin dukan yankin Yahudiya, da Samariya, har zuwa iyakar duniya.”

9 Da ya faɗa haka, suna cikin dubawa, sai aka ɗauke shi zuwa sama. Wani girgije ya rufe shi, ba su ƙara ganinsa ba.

10 Saˈad da suke zuba ido sama, shi kuma yana tafiya, sai ga mutum biyu a tsaye kusa da su, sanye da fararen riguna.

11 Sai suka ce, “Ku mutanen Galili, don me kuke tsaye kuna kallon sama? Yesun nan da aka ɗauke daga wurinku zuwa sama, zai sāke dawowa kamar yadda kuka ga ya tafi zuwa sama.”

12 Sai manzannin suka koma Urushalima daga Tudun Itatuwan Zaitun, wanda yake kusa da Urushalima, misalin tafiyar Ranar Hutu ta Mako guda, wato wajen kilomita ɗaya.

13 Da suka shiga birnin, suka hau gidan sama inda suke zama, wato su Bitrus, da Yohanna, da Yakub, da Andarawus, da Filibus, da Toma, da Bartalomi, da Matiyu, da Yakub ɗan Halfa, da Siman wanda ake ce da shi mai kishin ƙasarsu, da kuma Yahuda ɗan Yakub.

14 Duk waɗannan sun miƙa kai ga yin adduˈa da nufi ɗaya tare da waɗansu mata, da Maryamu mamar Yesu, da kuma ˈyanˈuwansa.

15 A kwanakin nan, akwai taron ˈyanˈuwa wato, masu ba da gaskiya wajen mutum ɗari da ashirin. Bitrus ya tashi a tsaye ya ce,

16 “ˈYanˈuwa, lallai ne a cika Rubutacciyar Maganar Allah da Ruhu Mai Tsarki ya faɗa a dā ta bakin Dawuda game da Yahuda, wanda ya yi wa masu kama Yesu jagora.

17 Gama dā shi ɗaya daga cikinmu ne, an kuma ba shi rabonsa cikin aikin nan.”

18 Da ladan mugun aikinsa kuwa Yahuda ya sayi wani fili, sai ya fāɗi da kai, cikinsa ya fashe, kayan cikinsa duk suka zuba a waje.

19 Duk mazaunan Urushalima kuwa sun san abin nan da ya faru, har da ake ce da filin “Akaldama” da yarensu, wato Filin Jini.

20 “Gama a rubuce yake a Zabura cewa, “ ‘Bari wurin zamansa yă zama kufai, kada a rage wani a ciki.’ An kuma ce, ‘Matsayinsa wani yă ɗauka.’ ”

21 “Domin haka ya kamata a zaɓi wani daga cikin mutanen nan, wanda yake tare da mu duk kwanakin da Ubangiji Yesu yake shiga da fita a wurinmu.

22 Ya kamata wannan mutum yă zama wanda ya kasance tare da mu tun daga lokacin da Yohanna yake yin baftisma har zuwa ranar da aka ɗauki Yesu daga wurinmu zuwa sama. Dole ne ɗaya daga cikin mutanen nan yă shaida tashinsa daga matattu tare da mu.”

23 Sai suka gabatar da mutum biyu, Yusuf mai suna Barsaba, wanda kuma ake ce da shi Yustus, da kuma Matiyas.

24 Almajiran suka yi adduˈa suka ce, “Ubangiji, ka san zuciyar kowa. Bari ka nuna mana wanda ka zaɓa a cikin waɗannan mutum biyu,

25 yă zama manzonka, yă ɗauki matsayin aikin manzon da Yahuda ya bari domin yă tafi wurin da ya dace da shi.”

26 Sai suka yi ƙuriˈa a kansu, Matiyas ya ci, aka kuma sa shi yă zama manzon Yesu tare da goma sha ɗayan nan.

Open Bible reader