Hausa Bible
Filibiyawa 1
1 Daga Bulus da Timoti, bayin Almasihu Yesu zuwa ga dukan tsarkakan da suke bin Almasihu Yesu a Filibi, tare da masu kula da jamaˈar masu bi da masu yi mata hidima.
2 Alheri da salamar Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu su kasance tare da ku.
3 Ina gode wa Allah a duk lokacin da na tuna da ku.
4 A kullum, da farin ciki kuwa nake yin roƙe-roƙena ga Allah saboda ku duka.
5 Ina godiya saboda kun haɗa kai da ni cikin aikin shelar labari mai daɗi tun daga ranar farko har zuwa yau.
6 Na tabbata shi wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai ci gaba har yă gama shi a Ranar da Yesu Almasihu zai dawo.
7 Daidai ne in yi ta tunawa da ku haka, ku duka, domin kuna a zuciyata, saboda dukanku kuna zumunci da ni cikin alherin Allah a lokacin da aka kulle ni a kurkuku, da kuma ta wurin kāre labarin nan mai daɗi wanda na tabbatar da shi.
8 Allah shi ne shaidata, ya san yadda nake marmarinku duka da ƙaunar Almasihu Yesu.
9 Adduˈata ita ce ƙaunarku ta yi ta yalwata, tare da sanin Allah da kuma kowace irin ganewa.
10 Wannan zai taimake ku ku iya zaɓar abin da ya fi kyau, domin a Ranar da Almasihu zai dawo ku zama masu tsarki, marasa tabo,
11 cike kuma da sakamakon cetonku, wato, halin adalcin da ake samuwa ta wurin Yesu Almasihu, domin a ɗaukaka a kuma yabi Allah.
12 ˈYanˈuwa, ina so ku sani cewa, abin da ya faru da ni ya ƙara sa labari mai daɗi ya yaɗu,
13 har sojojin gidan sarki, da sauran mutane suka sani cewa an kulle ni a kurkuku saboda Almasihu ne.
14 Kulle ni da aka yi a kurkuku, ya sa ˈyanˈuwa da yawa a cikin Ubangiji suka ƙara samun ƙarfin hali su yi shaidar kalmar Allah ba tare da jin tsoro ba.
15 Waɗansu dai suna waˈazin Almasihu saboda kishi da sonkai ne, amma waɗansu suna yi da nufi alheri.
16 Waɗannan da suke yin waˈazi da nufin alheri suna yin waˈazi saboda ƙauna ne, gama sun sani an kulle ni domin ina kāre labarin nan mai daɗi ne.
17 Waɗancan kuwa suna waˈazi a kan Almasihu saboda halin sonkai ne ba cikin gaskiya ba. Sonsu ne in ƙara shan wahala a kurkuku.
18 To, ba kome. Muhummin abu shi ne, a kowane hali, ko da nufin ƙarya, ko da nufin gaskiya, ana waˈazi a kan Almasihu ne. Wannan yana sa in yi farin ciki. I, zan ci gaba da yin farin ciki,
19 gama na sani cewa ta wurin adduˈoˈinku, da taimako daga wurin Ruhun Almasihu Yesu, a ƙarshe dai wannan zai sa a sake ni.
20 Ina marmari, kuma ina sa zuciya cewa kada in kawo wa kaina kunya cikin aikin Ubangiji, amma in yi magana da cikakken ƙarfin zuciya. Cikin dukan abin da zan yi, bari Almasihu yă sami ɗaukaka yanzu da kowane lokaci a wurina, ko ina da rai ko na mutu.
21 A gare ni kam, idan na rayu, domin Almasihu ne, idan ma na mutu, duk riba ce.
22 Idan ya zama zan rayu cikin jiki, zan yi aiki mai amfani ke nan. Amma na rasa wane ne zan zaɓa.
23 Hakika, hankalina ya rabu biyu. Abin da nake so dai, in koma wurin Almasihu in zauna tare da shi. Haka ya fi kyau ƙwarai.
24 Amma ya kamata in kasance cikin jiki tukuna domin amfaninku.
25 Tun da yake ina da tabbaci haka, na sani zan zauna tare da ku duka domin ku ƙara girma da farin ciki cikin bangaskiyarku.
26 Ta haka, idan na sāke kawo muku ziyara, za ku sami babban dalilin yin taƙama da Almasihu Yesu saboda abin da yake yi ta wurina.
27 Sai dai ku yi zaman da ya cancanci labari mai daɗi na Almasihu. Ta haka, ko na zo na gan ku, ko ma ban zo ba, zan ji labarinku in sani cewa kuna tsayawa sosai tare, kuna fama tare, raˈayinku ɗaya saboda bangaskiya ta labari mai daɗi,
28 ba tare da jin tsoron abokan gābanku ba ko kaɗan. Ai, wannan tabbaci ne a gare su cewa za su halaka, amma a wurinku tabbacin cetonku ke nan. Wannan tabbaci kuwa daga wurin Allah yake.
29 Gama alherin da ya yi muku saboda Almasihu, ba domin ku ba da gaskiya gare shi kawai ba, amma har ma domin ku sha wahala saboda shi,
30 kuna shan fama iri yadda kuka gani na sha, kuna kuma ji nake sha har yanzu.