Skip to content

Hausa Bible

Matiyu 3

1 A kwanakin nan Yohanna Mai Baftisma ya fito yana waˈazi a cikin dajin yankin Yahudiya,

2 yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya kusa!”

3 Wannan shi ne wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar mai kira a daji tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, Ku gyara hanyoyinsa!’ ”

4 Rigar da Yohanna ya sa kuwa an yi ta da gashin raƙumi ne. Yana kuwa ɗaure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da ruwan zuma.

5 Sai mutanen Urushalima da na yankin Yahudiya duka, da na dukan ƙasashen yankin Kogin Yodan, suka yi ta zuwa wurinsa,

6 suna faɗin zunubansu, yana yi musu baftisma a Kogin Yodan.

7 Amma da Yohanna ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa domin a yi musu baftisma, sai ya ce musu, “Ku ƙungiyar mugayen macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa hukuncin nan na Allah mai zuwa?

8 Ku haifar da rayuwa mai kyau wadda za ta nuna cewa kun tuba, kamar itacen da ya haifi ˈyaˈya masu kyau.

9 Kada kuwa ku yi taƙama a ranku cewa, ‘Ibrahim ne babanmu’, gama ina faɗa muku Allah yana da ikon yi wa Ibrahim ˈyaˈya da duwatsun nan.

10 An riga an sa bakin gatari a gindin itace. Duk itacen da bai ba da ˈyaˈya masu kyau ba, sai a sare shi a jefa a wuta.”

11 Ni dai da ruwa nake yi muku baftisma, domin a nuna kun tuba, amma wanda ya fi ni girma zai zo a bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da wuta kuma.

12 Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, kuma yă tattara alkamarsa yă sa cikin rumbunsa, amma zai ƙona dusar a wutar da ba a iya kashewa.

13 A lokacin nan ne Yesu ya zo daga Galili, ya je Kogin Yodan wurin Yohanna domin a yi masa baftisma.

14 Yohanna ya so ya hana shi, ya ce, “Ni, da nake bukata ka yi mini baftisma, yaya za ka zo wurina?”

15 Amma Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari yă zama haka yanzu, domin haka ne ya yi kyau mu cika dukan adalcin da Allah yake so.” Saˈan nan Yohanna ya yarda masa.

16 Da aka yi wa Yesu baftisma, ya fito daga ruwan ke nan, sai nan da nan sama ya buɗe, ya ga Ruhun Allah yana saukowa a kamannin kurciya, har ya sauka a kansa.

17 Sai aka ji wata murya daga sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana da nake ƙauna, wanda nake jin daɗinsa ƙwarai.”

Open Bible reader