Hausa Bible
Matiyu 19
1 Da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, ya bar yankin Galili ya shiga yankin Yahudiya, wanda yake a ƙetaren Kogin Yodan.
2 Mutane da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da masu ciwo a can.
3 A nan, waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa domin su gwada shi, sai suka tambaye shi suka ce, “Bisa ga Koyarwar Musa, daidai ne mutum ya saki matarsa a kan kowane irin dalili?”
4 Ya amsa musu ya ce, “Ashe, ba ku karanta ba cewa, shi Mahaliccin da ya yi su tun farko ‘ya yi su ne namiji da ta mace?’ Ya kuma ce,
5 ‘Domin haka fa, mutum zai bar babansa da mamarsa yă manne wa matarsa, su biyun kuma su zama ɗaya.’
6 Har nan gaba ba za su zama mutum biyu ba, sai dai su zama kamar mutum ɗaya. Saboda haka, abin da Allah ya haɗa, kada wani yă raba.”
7 Sai suka ce masa, “To, don me annabi Musa ya yi doka a ba da takardar kashe aure, a kuma saki matar?”
8 Sai Yesu ya ce musu, “Saboda kuna da taurin zuciya shi ya sa Musa ya yarda muku ku saki matanku, amma daga farko ba haka ba ne.
9 Ina kuma gaya muku, duk wanda ya saki matarsa, idan dai ba saboda an same ta da yin zina ba, ya kuma aure wata, ya yi zina.”
10 Sai almajiran suka ce masa, “Idan haka yake tsakanin mutum da matarsa, ashe ma rashin aure ya fi.”
11 Amma ya ce musu, “Ba kowa ne zai iya ɗauka maganar nan ba, sai dai waɗanda Allah ya yarda musu.
12 Akwai waɗanda aka haifa da ba za su iya yin aure ba. Akwai waɗanda mutane ne suka mai da su haka. Akwai kuma waɗanda suka yarda ba za su yi aure ba domin ƙaunar mulkin sama. Duk mai iya ɗaukar maganar nan yă ɗauka.”
13 Saˈan nan aka kawo wa Yesu yara ƙanana domin yă sa musu albarka, yă kuma yi musu adduˈa, amma almajiransa suka tsawata wa waɗanda suka kawo yaran.
14 Amma Yesu ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin sama na irinsu ne.”
15 Sai ya sa musu hannu albarka, saˈan nan ya tafi.
16 Ana nan sai wani ya zo wurin Yesu ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne zan yi domin in sami rai na har abada?”
17 Yesu ya ce masa, “Don me kake tambaye ni a kan abin da yake da kyau? Ai, Allah kaɗai ne mai kyau. Idan kuwa kana so ka sami rai na har abada, sai ka kiyaye dokokin nan.”
18 Sai ya ce wa Yesu, “Waɗanne dokoki?” Sai Yesu ya ce, “Kada ka yi kisan kai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya,
19 ka ba da girma ga babanka da mamarka. Ka kuma ƙaunaci maƙwabcinka kamar yadda kake ƙaunar kanka.”
20 Sai saurayin ya ce masa, “Ai, na kiyaye waɗannan duka, me ya rage mini?”
21 Yesu ya ce masa, “Idan kana so ka zama cikakke, ka je ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba talakawa kuɗin, za ka sami lada a sama. Saˈan nan ka zo ka bi ni.”
22 Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi yana baƙin ciki, gama yana da arziki sosai.
23 Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Hakika ina gaya muku, zai zama da wuya mai arziki yă shiga mulkin sama.
24 Ina sāke gaya muku. Zai fi wa raƙumi sauƙi ya bi ta ramin allura da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”
25 Da almajiran suka ji haka sai suka yi mamaki sosai, suka ce, “Idan haka ne, to, wa zai sami ceto?”
26 Amma Yesu ya dube su ya ce, “Ga mutane kam, ba zai yiwu ba, amma ga Allah kowane abu mai yiwuwa ne.”
27 Sai Bitrus ya ce, “Ga shi mun bar kome domin mu bi ka, to, me za mu samu?”
28 Yesu ya ce musu, “Hakika ina gaya muku, a zamani mai zuwa, lokacin da Ɗan Mutum zai zauna a kujerar mulkinsa mai ɗaukaka, ku da kuka bi ni, ku ne kuma za ku zauna a kujerun mulki goma sha biyu, ku yi mulkin zuriya goma sha biyun nan na Israˈila.
29 Kuma duk wanda ya bar gidaje, ko ˈyanˈuwa maza, ko ˈyanˈuwa mata, ko baba, ko mama, ko yara, ko gonaki, domin yă girmama sunana, zai sami fiye da haka sau ɗari, yă kuma gāji rai na har abada.
30 Amma mutane da yawa waɗanda suke na farko, za su zama na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.”