Hausa Bible
Matiyu 16
1 Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo wurin Yesu domin su gwada shi, suka roƙe shi yă nuna musu wata babbar alamar da za ta bayyana ikonsa.
2 Ya amsa musu ya ce, “Idan yamma ta yi, kuka ga sama ta yi ja, sai ku ce, ‘Yawwa, gari zai yi kyau gobe.’
3 Da safe kuma idan kuka ga sama ta yi ja, ta ɓata fuska, sai ku ce, ‘Yau kam za a yi ruwan sama.’ Kuna iya gane yanayin sararin sama, amma ba ku iya gane alamun wannan zamani ba.
4 Mutanen zamanin nan marasa aminci ga Allah ne, mugaye ne kuma. Suna so su ga alama, amma ba za a nuna musu wata alama ba, sai dai alamar Yona.” Sai ya bar su ya tafi.
5 Da almajiran suka kai wancan gefen, ashe, sun manta ba su kawo burodi ba.
6 Sai Yesu ya ce musu, “Ku kula fa, kuma ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”
7 Sai suka fara magana da junansu suna cewa, “Ko saboda ba mu kawo burodi ba ne?”
8 Da Yesu ya ga haka sai ya ce, “Ku masu ƙaramar bangaskiya, don me kuke cewa ba ku da burodi?
9 Har yanzu ba ku gane ba? Kun manta yadda na ciyar da mutum dubu biyar da burodi biyar? Kuma kwanduna nawa kuka tara?
10 Ko kuma lokacin da na ciyar da mutum dubu huɗu da burodi bakwai, kwanduna nawa kuka tara?
11 Yaya kuka kāsa ganewa cewa ba burodi nake magana a kai ba? Na ce ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”
12 Saˈan nan ne almajiran suka gane cewa ba yana ce musu su yi hankali da yistin da ake sa a cikin burodi ba ne, amma yana nufin su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa ne.
13 To, da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke cewa Ɗan Mutum yake?”
14 Sai suka ce, “Waɗansu suna cewa Yohanna Mai Baftisma, waɗansu kuma Iliya, waɗansu kuma Irmiya, ko kuma ɗaya daga cikin annabawa.”
15 Ya ce musu, “Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?”
16 Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Almasihu, Ɗan Allah Mai Rai.”
17 Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai mai albarka ne Siman ɗan Yona! Gama ba mutum nama da jini ba ne ya bayyana maka wannan, sai dai Ubana wanda yake cikin sama.
18 Ina kuma gaya maka, kai Bitrus ne, a kan wannan dutse kuma zan gina jamaˈata ta masu bi, wadda ikon mutuwa ma ba shi da iko a kanta.
19 Zan ba ka mabuɗan mulkin sama. Kuma abin da aka ɗaure a duniya, zai zama a ɗaure a sama, dukan abin da aka kunce a duniya, zai zama a kunce a sama.”
20 Sai ya ja wa almajiransa kunne sosai kada su gaya wa kowa cewa shi ne Almasihu.
21 Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara nuna wa almajiransa cewa dole ne yă je Urushalima, yă sha wuya iri-iri a hannun dattawa, da manyan firistoci, da malaman Koyarwar Musa, a kuma kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.
22 Sai Bitrus ya ja shi gefe ɗaya ya fara tsawata masa yana cewa, “Allah yă sawwaƙe, Ubangiji! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba.”
23 Amma Yesu ya juya ya ce masa, “Ka rabu da ni, kai Shaiɗan! Kai mai sa tuntuɓe ne a gare ni, gama kana tunani kamar mutum ne, ba kamar Allah ba.”
24 Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai so yă bi ni, sai yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa yă bi ni.
25 Gama duk wanda yake so yă ceci ransa, zai rasa shi. Amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.
26 Wane amfani ne mutum zai samu, idan ya sami duniya duka a bakin ransa? Ko kuwa me mutum zai iya bayar a maimakon ransa?
27 Ɗan Mutum dai zai zo da malaˈikunsa cikin ɗaukakar Ubansa, saˈan nan ne zai biya kowane mutum bisa ga aikinsa.
28 Hakika ina gaya muku, akwai waɗansu a tsaye a nan da ba za su mutu ba, har sai sun ga zuwan Ɗan Mutum cikin mulkinsa.”