Hausa Bible
Matiyu 14
1 A lokacin nan, Sarki Hirudus Antifas ya ji labarin Yesu.
2 Sai ya ce wa masu yi masa aiki, “Ai wannan Yohanna Mai Baftisma ne. An tashe shi daga matattu, shi ya sa yake da ikon yin waɗannan ayyukan ban mamaki.”
3 Gama dā ma Hirudus ya kama Yohanna ya ɗaure shi, ya sa shi a kurkuku saboda Hirudiya, matar ɗanˈuwansa Filibus.
4 Gama dā ma Yohanna ya yi ta gaya wa Hirudus cewa bisa ga doka, bai kamata yă auri Hirudiya ba.
5 Ko da yake Hirudus yana so yă kashe Yohanna, amma yana jin tsoron mutane, gama sun ɗauka Yohanna annabi ne.
6 Amma da ranar da aka haifi Hirudus ta sāke zuwa, sai ˈyar Hirudiya ta yi rawa a gaban baƙin da suka zo bikin. Ta sa Hirudus ya ji daɗi sosai
7 har ma ya yi mata alkawari tare da rantsuwa cewa, zai ba ta duk abin da ta roƙa.
8 Mamarta kuwa ta ba ta shawara game da abin da za ta ce, sai ta ce, “A ba ni kan Yohanna Mai Baftisma yanzu a cikin kwano.”
9 Sarki kuwa ya damu, amma saboda rantsuwar da ya yi a gaban baƙin, sai ya yi umarni a ba ta.
10 Ya aika zuwa kurkuku aka cire kan Yohanna.
11 Aka kuwa kawo kan a cikin kwano, aka ba yarinyar, sai ta kai wa mamarta.
12 Sai almajiran Yohanna suka zo, suka ɗauki gawarsa suka binne. Sai suka je suka gaya wa Yesu.
13 Da Yesu ya ji haka, sai ya tashi ya shiga jirgin ruwa ya haye zuwa wani wuri inda ba kowa domin yă kasance shi kaɗai. Amma da taron mutanen suka ji haka, sai suka fito daga garuruwa suka bi shi da ƙafa.
14 Da ya fita daga jirgin kuwa, ya ga mutane sun taru da yawa. Sai ya ji tausayinsu, ya kuma warkar da marasa lafiya a cikinsu.
15 Da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuma yamma ta yi. Ka sallami mutanen nan domin su je ƙauyuka su saya wa kansu abinci.”
16 Yesu ya ce musu, “Ba lallai su tafi ba, ku ba su wani abu su ci.”
17 Suka amsa suka ce, “Ba mu da kome a nan sai burodi guda biyar da kifi guda biyu.”
18 Sai ya ce, “Ku kawo mini.”
19 Sai ya umarci mutanen su zauna a kan ciyawa. Ya ɗauki burodin nan guda biyar da kifin biyu, sai ya ɗaga kansa sama, ya yi godiya ga Allah. Sai ya rarraba burodin ya ba almajiransa, almajiran kuma suka ba jamaˈa.
20 Dukansu suka ci suka ƙoshi. Suka tattara duk abin da ya rage, har ya cika kwanduna goma sha biyu.
21 Mutanen da suka ci kuwa sun kai maza dubu biyar, ban da mata da yara.
22 Suna gamawa ke nan, sai Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa domin su koma can gefen. Shi kuwa ya tsaya a wurin domin yă sallami taron.
23 Bayan da ya sallami taron, sai ya hau kan tudu shi kaɗai domin yă yi adduˈa. Har yamma ta yi sosai yana can shi kaɗai.
24 A wannan lokaci kuwa jirgin yana tsakiyar teku, raƙuman ruwa suna buga shi, kuma iska tana gāba da su.
25 Wajen ƙarfe uku na dare sai ga Yesu yana takawa a kan teku zuwa wurin almajiransa.
26 Amma da almajiran suka gan shi yana tafiya a kan teku, sai suka ji tsoro, suka ce, “Fatalwa ce!” Suka yi ihu saboda tsoro.
27 Nan da nan sai Yesu ya yi musu magana ya ce, “Kada ku damu! Ni ne, kada ku ji tsoro!”
28 Sai Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ubangiji, idan kai ne, ka sa in zo wurinka a kan ruwan.”
29 Yesu ya ce, “Zo mana.” Saˈan nan Bitrus ya fita daga jirgin, ya fara tafiya a kan ruwa zai je wurin Yesu.
30 Amma da ya ga iskar ta yi ƙarfi, sai ya ji tsoro ya fara nutsewa. Sai ya yi ihu, ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”
31 Nan da nan sai Yesu ya miƙa hannunsa ya kamo shi, ya ce masa, “Kai mai ƙaramar bangaskiya, don me ka yi shakka?”
32 Da suka shiga jirgin sai iskar ta daina hurawa.
33 Waɗanda suke cikin jirgin suka yi wa Yesu sujada, suna cewa, “Gaskiya, kai Ɗan Allah ne.”
34 Da suka ƙetare tekun, suka sauka a yankin Janisarat.
35 Mutanen garin kuwa suka gane, ashe, Yesu ne, sai suka aika a faɗa wa kowa da yake a wannan sashen ƙasar, suka kawo masa dukan marasa lafiya.
36 Suka roƙe shi su taɓa ko da bakin rigarsa. Dukan waɗanda suka taɓa kuwa suka warke.