Hausa Bible
Markus 7
1 Farisiyawa da waɗansu malaman Koyarwar Musa daga Urushalima suka zo suka taru wurin Yesu.
2 Sai suka lura waɗansu almajiransa suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta, wato ba su wanke hannu bisa ga alˈada ba.
3 Ga shi Farisiyawa har da sauran Yahudawa ba sa cin abinci sai sun wanke hannu sarai tukuna, bisa ga alˈadun dattawa.
4 In suka komo daga kasuwa kuwa, ba sa cin abinci sai sun yi wanka tukuna. Akwai kuma waɗansu alˈadu da yawa da suka gāda, suke kiyayewa, kamar wanke-wanken kwafuna, da tukwane, da tulunan tagulla.
5 Sai Farisiyawa da malaman Koyarwar Musa suka tambayi Yesu, “Don me almajiranka ba sa bin alˈadun dattawa amma suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta?”
6 Sai ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku munafukai! Kamar yadda yake a rubuce cewa, “ ‘Mutanen nan fa, da bakinsu ne kawai suke girmama ni, amma zukatansu sun yi nesa da ni.
7 A banza suke yi mini sujada. Suna koyar da dokokin mutane, a matsayin kalmar Allah.’ ”
8 “Kun bar abin da Allah ya ce a yi, kuna bin alˈadun mutane.”
9 Sai ya ce musu, “Lallai kam kun iya barin umarnin Allah domin ku bi alˈadunku!
10 Gama Musa ya ce, ‘Ka girmama babanka da mamarka,’ kuma, ‘Wanda ya zagi babansa ko mamarsa dole ne a kashe shi.’
11 Amma kukan bar mutum yă ƙyale iyayensa a lokacin da suke da bukata, yă ce, ‘Duk abin da dā za ku samu a wurina na riga na keɓe wa Allah ko.’
12 Ta haka kuka hana shi yă taimaki babansa ko mamarsa.
13 Ta haka kuna mai da kalmar Allah wofi saboda alˈadun da kuke koya wa yaranku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa.”
14 Sai Yesu ya sāke kiran jamaˈa, ya ce musu, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma gane da kyau.
15 Abin da yake shiga cikin mutum daga waje ba shi ne yake ƙazantar da mutum a gaban Allah ba, abin da yake fitowa daga cikin mutum, shi ne yake ƙazantar da mutum a gaban Allah.
16 Duk mai kunnen ji, bari yă ji.”
17 Saˈad da ya rabu da taron ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi maˈanar wannan koyarwa.
18 Ya amsa ya ce, “Ashe, ku ma ba ku gane ba? Ba ku gane cewa duk abin da ya shiga cikin mutum daga waje ba ya iya ƙazantar da mutum a gaban Allah,
19 gama ba cikin zuciyarsa yake shiga ba, amma cikin cikinsa ne, saˈan nan yă kuma fita daga jikinsa?” A wannan maganar Yesu ya nuna cewa kowane irin abinci marar ƙazanta ne.
20 Ya ci gaba da cewa, “Abin da yake fitowa daga cikin mutum, shi ne yake ƙazantar da mutum.
21 Don daga cikin zuciyar mutum ne mugayen tunani suke fitowa, kamar su lalata, da sata, da kisan kai, da zina,
22 da kwaɗayi, da mugunta, da ruɗu, da halin neman jin daɗi na rashin kunya, da kishi, da ɓata suna, da girman kai, da kuma wawanci.
23 Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin zuciya suke fitowa, suna kuwa ƙazantar da mutum.”
24 Daga nan sai Yesu ya tashi ya tafi yankin Taya da Sidon. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa yă sani ba. Amma duk da haka ɓoyewarsa bai yiwu ba.
25 Nan da nan sai wata mace wadda ˈyarta ƙarama take da ƙazamin ruhu ta ji labarinsa. Ta zo ta fāɗi a gabansa.
26 Matar kuwa Baheleniya ce. A yankin Finikiya aka haife ta, a cikin ƙasar Suriya. Sai ta roƙi Yesu yă fitar wa ˈyarta aljanin.
27 Yesu ya ce mata, “Bari ˈyaˈya su ci su ƙoshi tukuna, ba daidai ba ne a kwashi abincinsu a ba karnuka.”
28 Amma matar ta amsa ta ce, “I, haka ne, malam, amma ai, karnuka sukan ci abin da yake fāɗuwa daga teburin yara.”
29 Sai ya ce mata, “Saboda wannan amsa da kika bayar, ki tafi gida, aljanin ya rabu da ˈyarki.”
30 Sai ta koma gida ta ga ˈyarta a kwance a gado, aljanin kuwa ya rabu da ita.
31 Sai Yesu ya fita daga yankin Taya, ya bi ta Sidon ya je Tekun Galili. A hanya, ya zo yankin Garuruwa Goma.
32 A can aka kawo masa wani kurma, wanda da kyar yakan yi magana. Suka roƙe shi yă taɓa mutumin domin yă warkar da shi.
33 Yesu ya ja kurman gefe inda ba kowa, sai ya sa yatsunsa a kunnuwansa, ya tofa miyau, ya kuma taɓa harshensa da miyaun.
34 Saˈan nan ya ɗaga kai sama ya yi numfashi mai zurfi, ya ce masa, “ Iffata!” Wato “Buɗe!”
35 Da faɗin haka sai kunnuwan mutumin suka buɗu, abin da ya ɗaure harshensa kuma ya kunce, sai ya fara magana da kyau.
36 Yesu ya ja musu kunne kada su faɗa wa kowa, amma da yana hana su, su kuma suna ƙara baza labarin.
37 Mutane suka cika da mamaki, suka ce, “Kai, ya yi kome da kyau! Har ma ya sa waɗanda dā suke kurma suna jin magana, waɗanda dā suke bebe kuma suna yin magana.”