Skip to content

Hausa Bible

Markus 16

1 Da Ranar Hutu ta Mako ta wuce, Maryamu daga Magadala, da Maryamu mamar Yakub, da kuma Salomi, suka sayo kayan ƙanshi domin su je su shafa wa jikin Yesu.

2 A ranar farko ta mako, da sassafe wajen fitowar rana suka tafi kabarin.

3 Da suke kan hanya, suka ce wa juna, “Wa zai ture mana dutsen daga bakin kabarin?”

4 Amma da suka kai wurin, suka ɗaga kai suka ga, ashe, an riga an ture dutsen. Babban dutse ne kuwa.

5 Da suka shiga kabarin, sai suka ga wani saurayi a zaune a gefen dama, da farar riga a jikinsa, sai suka ji tsoro.

6 Sai saurayin ya ce musu, “Kada ku yi mamaki. Kuna neman Yesu Banazaret wanda aka gicciye? Ai, ya tashi. Ba ya nan. Ga inda aka kwantar da shi!

7 Yanzu sai ku tafi ku gaya wa almajiransa, har da Bitrus, cewa zai riga su zuwa Galili, a can ne za su gan shi kamar yadda ya faɗa musu.”

8 Matan kuwa suka fita da gudu, sun ruɗe suna rawar jiki. Ba su kuma ce wa kowa kome ba, domin suna jin tsoro. [

9 Da Yesu ya tashi daga matattu da sassafe a rana ta farko ta mako, ya fara nuna kansa ga Maryamu daga Magadala, wato macen nan da Yesu ya fitar mata da aljanu bakwai.

10 Ita kuwa ta tafi ta faɗa wa mutanen da suke tare da shi tun dā, waɗanda suke baƙin ciki suna ta kuka.

11 Amma da suka ji cewa Yesu yana da rai, har ma ta gan shi, ba su ba da gaskiya ba.

12 Bayan haka Yesu ya canja kamanni ya nuna kansa ga waɗansu biyu daga cikin almajiran a lokacin da suke tafiya ƙauye.

13 Sai biyun nan suka koma suka faɗa wa sauran, amma har yanzu suka ƙi su yarda da labarin.

14 Daga baya Yesu ya nuna kansa ga sha ɗayan a daidai lokacin da suke cin abinci. Sai ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu da taurin kansu, don ba su gaskata waɗanda suka gan shi bayan tashinsa ba.

15 Ya kuma ce musu, “Ku tafi koˈina a dukan duniya, ku yi wa dukan ˈyan Adam shelar labarin nan mai daɗi.

16 Duk wanda ya ba da gaskiya, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda ya ƙi ba da gaskiya za a hukunta shi.

17 Ga abubuwan da masu bina za su yi don shaidar gaskiyarsu. A cikin sunana za su fitar da aljanu, za su kuma yi magana da sababbin harsuna.

18 Za su ɗauki macizai da hannuwansu. Idan kuma suka sha dafi, ba zai yi musu kome ba. Za su kuma sa hannuwansu a kan marasa lafiya, su warke.”

19 Bayan da Ubangiji Yesu ya yi musu wannan jawabi, sai aka ɗauke shi aka kai shi cikin sama, ya zauna a hannun dama na Allah.

20 Almajiran kuwa suka fita, suka yi ta waˈazi koˈina. Ubangiji kuwa ya yi aiki tare da su, yana tabbatar da gaskiyar maganarsu ta wurin alamu masu ban mamakin da ya sa su suka yi tare da maganar.]

Open Bible reader